🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 26

2.9K 121 8
                                    

🥀🌺🥀 *FAHIMTA..* 🥀🌺🥀

_It's about a girl who is been molested by her step grandmother eventually she met someone that changed her life..._

           *XINNEE SMART*

*LAST PAGE*.......

*Page.. 26* Ganin kansa na neman yin ciwo ne yasa yafita, direct bedroom d'insa yanufa kwanciya yayi akan bed d'insa, take bacci yayi awon gaba dashi,

         Baifarka ba Sai gurin bayan la'asar, da wani irin ciwon Kai yatashi, time yaduba, tashi yayi yayi al'wala yagabatar da sallolin da ake binsa,

       Tsananin tunanin mafarkan zainab da yayi ne kedamunsa, sossai yake son ganinta, a gefe d'aya na zuciyarsa kuwa tsantsar tasanar Rukayya, ce aciki,

DA kyar yaga gari yawaye, wanka yayi yanufi office d'insu yanema izinin, tafiya gida, yana samun permission, yanufa airport yayi bucking flight,

           Rukayya, kam tunda tasamu yafita batare da yace mata komai ba hankalinta ya d'an kwanta, rufe qofar room d'inta tayi dan karma yadawo, dan batason sake haduwa dashi sai sunyi magana da boka, dan haka tai zamanta a d'aki, saida taji fitarshi, tayi saurin zuwa kitchen tasamu abunda tasakawa cikinta dan sossai take jin yunwa,

      *********yana dawowa yasoma shiri neman wayarsa yayi baigani ba dan yaso kiran, zainab, dabaigani ba, sai ya ha'kura, tunda gobe zashi gida,

         Ko tunanin neman Rukayya, baiyiba,
**********

Rayuwa na tafiyar wa zainab, kadaran kadahan, babu yabo babu fallasa, haka take rainon d'anta wanda akasawa sunan mahaifin mijinta, wato Muhammad, saidai suna kiransa da Abul'bait,

       Taci gaba dayin wainar fulawar ta, tun lokacin datayi arba'in, zuciyar ta, kuwa har gobe da jibi, son ma'aruf ne acikinta sossai take wahala da begensa, saidai bata fasa addu'a ba, roqonta a kullum Allah yadawo mata da Ma"aruf,

*****************

MUM ce zaune yayinda Nina, ke kwance kan qafarta tana sheshekar kuka, rarrashinta mum, taci gaba dayi, kiyi ha'kuri Nina, insha'Allah za'a ganta ne....

Sallamar wanda mum, taji ne yasa tad'ago Kai takalli qofar shigowa parlour, tabbas kuwa shine, kasa haquri mum tayi tace, Ma"aruf? Kaine?

      Murmushi yayi, ya isa gareta, hugging nata yayi, hawaye nasauko masa, rarrashinsa mum, tashiga yi harta samu yayi shiru,

    MUM, dan Allah kiyafeni, wlh bansan mai yahau kainaba da har namanta dake nadaina kiranki a waya, mum, nasan kina fushi dani amma dan Allah ki gafarce ni,wl..... Rufe masa baki mum, tayi tana girgiza masa Kai alamar yayi shiru,

Ya'isa haka Baba, wlh nayafe maka duniya da lahira, kuma nidama ban qullace ka ba, nasan ko wani Bawa da tashi jarabawa, mukuma Rukayya, ce jarabawar mu, dan ko rantsuwa nayi bazanyi kaffara ba da Sanya hannunta acikin wannan al'amarin dake faruwa,

       Hawaye yagoge, sossai idonsa yai ja, yace abun takaicin ma,wai har zainab namanta, Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un, wlh tausayinta nakeji ni bnma san da wani idon zan kalleta ba, ya qarasa fad'a kamar zai fashe da kuka,

       Nina ce tace, yanzun ma gashi bama musan a inda takeba, saurin kallon Nina yayi bangane ba? Amina ina zainab d'in? Ba'asan inda takeba?

Inna"lillahi wa'inna ilaihim"raji'un, dafe kansa yayi, wani irin qunci na ziyartar zuciyarsa, mum, ce taharari Nina,

       Kaga Ma"aruf garka daga hankalinka nasan insha'Allah Za aganta, abunda yasa bamuyi saurin saka cigiya kafafen sadarwa ba, saboda, munaso mufara bincikawa gidansu ko tanacan, to matsalar ma shine rashin sanin gidansu da bamuyi ba..... ni yanzun zanje neman ta mum, ni nasan gidansu,

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now