🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part9

1.4K 89 0
                                    

🥀🌺🥀 *FAHIMTA...* 🥀🌺🥀

_It's about a girl who is been molested by her step_ _grandmother eventually she met someone that changed her_ _life...._

*XINNEE SMART*

9...... Kai tsaye d'akin dayake tunanin nata ne yashiga tura 'kofar yayi a hankali,

Zainab da tai shirin bacci tana zaune akan gadonta tana duba wani English book saboda sun kusa yin exam,

Jin motsin bud'e' kofa ne yasa ta juyawa dan a zaton ta mum ce... Sa'banin haka bad guy tagani, dan sunan datasa masa kenan tun ranar da taganshi da kwalbar champagne, wanda a tunanin ta giya ce, dakuma taba,
tasaka masa sunan wanda acewarta bata ga mutumin da ya had'a munanan halayya ba kamarsa,

         Jikinta ne yahau kyarma dan itakam ta tsani ganinsa shiyasa ma tamatsu ayi aurensa yatafi ko tasamu ta sake, dan tun ranar da tafara ganinsa taga yana 'ko'karin ta'bata ta tsorata dashi.... Ganinsa a gabanta ne yafargar da ita duniyar tunanin data lula,

Cike da tsoro ta'kura masa ido...

Zainab! Yakira sunanta cikin  kasalalliyar murya, wanda yasa gaban zainab d'in tsananta bugu, sake Kiran sunan nata yayi,  yayin da takasa amsawa tsabar tsorota da tayi dashi,

       Tun ranar da nafara ganinki a rayuwa ta naji inasonki dan kinyimun haka komai naki yamun,naso injira ki kisamu koda matakin secondary ne kafun inbayyana miki soyayya ta saidai kuma nakasa zuciya ta ta'ki amincemun da haka musamman dakika nemi ku'buce mun, a kullum sonki na azabtar da zuciyata ko wani step na rayuwata sonki hauhawa yake a tare dani,

Dan haka nayi tunanin gwara insanar dake......

Duk da har yanzun yarinyace dan shekarun ta iya 15 ne kawai amma hakan bai hanata gane kalmar son daya ke ambata ba saidai sauran kalaman nasane sunyi wa 'kwa'kwalwarta girma... dan haka bazata ce ga inda maganganun nasa suka dosa ba saidai kuma kalmar son da ya fad'a ce abun ke bata mamaki da takaici....... Maganarsa ce takatseta, daga gajeren tunanin datake,

      Idan har kin amincemun zan sanar da mum, sufasa shirin aurena da Rukayya da sukeyi,sai ayi shirinsa dak......

Dawa?

tayi saurin katse shi da tambaya, kallon ta yayi yayin da taci gaba da magana.... Lallai yama sunanka? ko da yake basai nasan sunanka ba, ta ta'be baki Idan dai kana FAHIMTAR mai nake cewa yau baka yi shaye shayen ba.... saurin d'aga kansa yayi yadubeta cike da mamakinta... Itakam ko a Jikinta taci gaba da magana duk da tsoron dake ratsa ta hakan baisa tayi shiru ba tsabar karfun hali irin na zainab,

        Inada wanda nakeso kuma shi naiwa al'kawarin kaina, shi nakeso, kuma bazan ta'ba canzawa ba, tana gama fad'in haka tashige toilet abunta,

Shikam tsabar mamaki da takaici ne suka sa ya kasa tashi,

Candai yalalla'ba yami'ke d'akinsa yanufa jiki ba 'kwari ransa duk a jagule,

Tunani yake.... Mai yasa baiyi tunanin zainab mace ce ba? Maiyasa baiyi tunanin tana da zuciya kamar kowa ba? Maiyasa baiyi tunani zata iya son wani ba? Tabbas nayi kuskure da na amincewa zuciyata cewa, zainab bazata'kini ba, to ko in fad'a mata cewa nine nataimaketa? Nine naceceta daga hannun azzalumai? A a bazan yi hakaba dan wata 'kila ta amincemun dan Ramawa kura aniyarta, nikuma nafison tasoni badan taimakon da naimata ba, to meye mafita ?

     Tambayoyin da yake wa kansa kenan, wayarsa dake gefensa ce tayi ringing, a gogo yaduba yanzun 11:45pm, sanan yad'au wayar, shiru yaji anyi dan haka Shima shirun yayi can yaji muryar macce, hello,

     Amsawa yayi Shima,

shiru ne yasake biyo wa baya bayan yan da'ki'ku,can dai tasake cewa Ru'kayya ce.....

to Sai me? dan Rukayya ce Sai akace takira mutum sha d'ayan dare?

       Shiru tayi batace masa komai ba, shikuwa yaci gaba da fad'a inda yake shiga ba nan yake fita ba kaf 'bacin ransa saida yasauke shi akanta, daga 'karshe yayi tsaki yakashe wayarsa,

.......................................................
A'bangaren Amarya Rukayya' bacin rai a gunta ba a magana, take shawarar yar uwarta Maryam tafad'o mata, da ta'ki amincewa,  amma yanzun kam yazama mata dole takai Ma"aruf gurin boka dan sam bata ga alamun zai sota ba bare yadaraja ta,

Take tashiga Alla Alla gari yawaye taje gidan Maryam dan suje akama mata Ma"aruf a hannunta, mumushin Jin dad'i tasaki da ta tuna yadda zata ri'ka juyashi,


Gari na wayewa, tun sassafe tanufi gidan Maryam, nan suka nufi wani 'kauye Sai gurin boka inda a take boka ya had'a mata komai saidai yatabbatar mata da akwai matsala a gaba amma yanzun kam sai yadda tayi da Ma"aruf, Jin statement d'in boka na'karshe yasa bata damu da zancensa na farko ba, a take ta amince ya had'a musu komai nan yabata wata yar kwalba yace ta adanata, domin duk ranar da tabari tafashe to asirin ya karye kenan, jiki na rawa takarba tayi godiya sanan tabiyashi suka tafi,

Aikuwa tundaga ranar Ma"aruf yashiga rawar 'kafa da Rukayya,

inda itakam ranta kamar farar audiga, yayin da A'bangaren zainab kamar ancire mata' kaya dan tun ranar baisake yimata magana ba hakan yayi mata daidai ko bakomai zatasamu tayi karatun ta a nutse had'i da tunanin gwarzon zuciyarta batare da wata damuwa ba,

           Ana gobe d'aurin aure Nina, tazo daga makaranta, inda jininsu yahadu da zainab dan itama sam batada 'kyamatar mutane,

Anyi shagulgula, inda duk inda zainab tayi to idanun Ma"aruf na kanta har tsalguwa takeyi, wanda shikuma ana shi' bangaren ya yanke cewa zaibata time tayi karatun ta, lokacin ta'kara sanin meye rayuwa dan Shikam tun ranar da mum tabashi tarihin zainab yaji tamkar ansake damfara masa sonta, a ransa ya'kudurce wa aurenta ba gudu baja da baya,

Washe garin ranar da aka d'aura aure Amarya da ango suka lula yawon honnymoon,.....








_Xinnee smart_

*Love u so much my masoya* 😍💋❤

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now