🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 14

Start from the beginning
                                    

Zainab kam tunda taji mai mum tace, 'kirjin ta ke bugawa, yayin da wani sashin na zuciyarta ke cewa, hmmm Allah sarki mum ai daidai shi kenan mum, domin kuwa sunyi tarayya gurin mugun Hali, dan da kinsan halin d'anki da bakiyi sha'awar had'a ni dashi ba, sam bashi da nagartattun hallayan da a kullum kike mun addu'ar Allah ybani miji mai su.......

dafata da mum tayi ne yasa tadawo wa duniyar tunanin data lula,

Yata" karki damu kanki matu'kar baki amincewa auren ba, to nayi al'kawarin bazan had'a ba, dan kema yata ce kuma kinada yancinki dan haka bazan tauye ki ba, zan nemo masa wata, dama dan ganin ke munsaba nasanki nasan halinki kuma ke d'in tarbiyyata ce shiyasa nafi sha'awar had'a wa dake,

tunda mum tafara Magana zainab ba tace komai ba saida taga tana 'ko'karin tashi tace.. Mum... dakatar da ita mum d'in tayi, had'i da shafa Fuskarta tayi mata murmushin ya'ke da yafi kuka ciwo,

Fita mum tayi.. batare da tasake cewa komai ba,

Shiru zainab, tayi tana tunanin itakam kokadan, batajin son Ma"aruf a ranta taya zata fara rayuwa da mutumin da bataso,?

babbar matsalar ma, matarsa, itakam, batason matar ko kad'an, kamar yadda ta fahimci itama ta tsaneta, babban damuwar ma auren mashayi Allah yatsareta,

Wani dogon numfashi taja lokacin da ta tuno da rabin ranta, da har yau take azabtuwa da rad'ad'in sonsa,

Anya zan iya rayuwa ba dakai ba kuwa,? ta tambayi kanta,

mtss wata zuciyarta ce tayi d'an tsaki tace lallai iska na wahalar da mai kayan Kara, (ni kuwa nace musamman idan ya d'ebo da yawa☹) to da kike wannan zancen zainab a ina zaki ganshi wanda kike wa wannan son,?

Kuma ma kikasani ko shima mashayin ne?

dasauri ta girgiza kai tana mai kwa'bar zuciyarta da tadaina wannan tunanin, a fili tace kuma ma ai ko mashayine idan munyi aure na gyara abuna, insakashi a hanya, ta yadda ko zaisha giya sai dai yasha ta 'kaunata,

To amma yanzun ya zanyi da mum? taiwa kanta wannan tambayar, to ai tace idan banaso shikenan,

Lallai zainab bansan bakida hankali ba sai yau, wata zuciyar ta ce ke fad'a mata haka, ci gaba tayi da ce mata, yo idan ba rashin hankali ba, zainab matar da ta maye miki gurbin komai da Kowwa na duniya yau itace zata nemi alfarma a gunki ki kasa yimata?

Haba zainab?

girgiza kai tafara yi bayan ta gama sauraren zuciyarta, hawayene yafara sauka akan fuskarta, mum bata cancanci haka daga gareni ba, wlh tafi 'karfin komai a guna matu'kar bata'kyamaceni ba ni bai kamata in' kyamaci d'an ta ba..... bata gama tunanin ba ta tashi da gudu tanufi d'akin mum d'in,

Samunta tayi tana amsa waya, tana ganin zainab tayi sallama da wacce take waya, 'karaso mana zainab kika tsaya a bakin'kofa kamar wata ba'kuwa,?

'karasawa zainab tayi tazauna a'kasa kanta a sunkuye tace, mum fushi kikayi?

murmushi tayi tace kinta'ba ganin wanda yake fushi da yarsa? Yar ma kamar tawa? ni ba fushi nake dake ba, ki kwantar da hankalinki kinji? ai na fad'a miki sai da amincewarki,

To mum ai na amince,

da gaske kike zainab? Mum tafad'a cike damamakin jin haka daga gareta,

gyad'a kai zainab tayi alamun Eh "

Allhmdllh" Allah nagode maka, ha'ki'ka nasan bazan ta'ba dana sanin za'bawa d'ana ke amatsayin mata ba, Inafata Allah yasa wannan had'in yazama had'in alkhairee,

Ngode nagode zainab, kingama mun komai Allah yayi miki albarka, amin mum, saidai Kidaina mun godiya nifa yarki ce maison yin biyayya a gareki wlh mum yadda nakejin ki araina ko mahaifiyata sai haka,

Cike da tsananin farinciki mum tarungumeta tana dad'a samata albarka,
.......................................................

Kuka sossai zainab, keyi bayan takoma d'aki, wanda abubuwa da dama suka Sakata yinsa, rashin iyaye, da rashin gata na ba wanda a yau zata nuna tace nata ne, abun namata ciwo sossai, Allah ya isa, Baba Larai dan kece sanadin rasa farinciki na, ga tsananin so dake d'awainiya da ita tarasa ina zata tsoma ranta taji sanyi,



ga wannan 'kaddararren auren, akwai aiki sossai a gabanki zainab, tafad'a wa kanta,........
.......................................................

Shirye shiryen biki mum keyi gadan gadan, inda shima Ma"aruf ke, 'ko'karin kammala gininsa, da yakeyi a scorpion road, saboda mum tamatsa masa lallai yayi yagama gini domin acan Za akai amarya, dan haka yake aikin ginin ba kama hannun yaro duk da har yau baisan wacece amaryar ba sam shi hakan bai dameshi ba,

Dan bata gabanshi,

Yau saura kwana hud'u d'aurin aure amma Rukayya batasan wainar da ake to yawa ba, dan tanacan London tana she'ke ayarta,................



😍💃🏻😍 *KUYI SHIRIN ZUWA* *BIKI DAI* *DAGA CAN* *RUKAYYA TAYI MUKU ICCE* 😂


_Xinnee smart_ 👌

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now