🥀🌺🥀FAHIMTA.. 🥀🌺🥀Part 12

Start from the beginning
                                    

Rukayya kam ganin kallon da zainab taimata saita 'Kara fusata dan atunaninta kallon raini ne, saboda yanayin idanun zainab d'in tamkar na mai jin bacci suke duk da girmansu, amma kowani lokaci a lumshe suke,
    Batasan lokacin data zabga mata mari ba, aikuwa itama tana sauke hannunta tanajin tafi a tata fuskar har sau biyu, saida taga taurari juyawa tayi taga wani mai 'karfun halin ne yai mata wannan'barin makauniyar har biyu?

      Cike da Mami takalleshi Ma"aruf? Kamareni?

tafad'a cike da jinzafinsa had'i da mamaki, an mareki yabata amsa a harzu' ke, nan gaba abunda yafi mari ma zanmiki dan nakula dabbancin naki kullum gaba yake, kuma ina mai gargad'inki kan wannan yazama na 'karshe da zakiyi gigin ta'ba lafiyar zainab dan wlh bazan lamunta ba,....

Yana gama fad'in haka yaja hannun zainab daketa faman kuka mota yabud'e yace tashiga'ko'karin shiga take Rukayya tacafkota wlh ba inda zakatafi da ita saidai kartaje makarantar idan dai sai kakaita maci amana kawai mamakin Rukayyar ne yakamashi had'i da takaicinta, murmushin takaici yayi yace cakamata hijab d'inta.... tayi banza dashi kamar bada ita yake ba, 'ko'karin janyeta yake, amma tana turjewa to wai ina zaku??

Zai bata amsa sai yaji muryar mum nacewa Kai lafiya? Mai yasamu Baby na, ta'karasa tajanye zainab daga hannun Rukayya, zainab jinta a jikin mum yasa tasaki kuka mai cin rai, hankalin mum yasake tashi, tadubi Ma"aruf, lafiya? Maike faruwane, wai mum dan kawai zankai zainab ta hafiz shine ta fito tana masifa..... Eh ai dole inyi masifa taya da sassafe zan ganka damace bazanyi tunanin wani abu ba,? Tunda nidai bansanta ba, kuma jiya ma ba a d'aki d'aya muka kwana ba to yabazanyi tunanin ko d'aukota kayiba?...... Innalillahi kawai yake nanatawa a ransa zuciyarsa cike da takaicin Rukayya baita'ba tsanar ta da halayyarta irin yau ba Sam batada kunya ko kad'an, mum ma bakaramin baci ranta yayi ba saidai hakan baihanata ce mata, wannan d'in bawata bace kanwarsa, kuma abunda kike zargi ba haka bane, yata ba Yar banza bace, mum taja hannun zainab suka shige gida,

Ma"aruf kuwa cike da tsanarta yadubeta yace... Kin kyauta da kika saka bacin rai a fuskar mahaifiyata saidai ina miki albishir da wannan abun da kikayi bashi zaisa nakasa aiwatar da 'kudirina ba.... zare ido tayi tadubeshi bangane mai kake nufi ba,?

     Wani kallo yaimata..   Zaki gane mai nake nufi...... Wuceta yayi,

Ba'kinciki da tunani ne yaiwa zuciyar Rukayya yawa wanda ko break fast bata tsaya yiba, tad'auko mayafinta da jaka,

      Makullin mortar Ma"aruf tad'auko, dama ita batazo da mota ba ganin ba a 'kasar zasu zauna ba,........

          Gurin boka tanufa kai tsaye dan ko Maryam bata nemaba wannan karon,

Da zuwa tafara'kundume'kundume, kamar yadda ake idan akazo gurin, wata mahaukaciyar dariya yasake, babbar ta kazar ubanka, shine abunda Rukayya tafad'a had'i da jinjina masa hannu, wata dariya shima yayi had'i da lailayo gundumemiyar ashar yazabga mata, godiya nake boka, d'an nanu,

    Fuska yatamke maike tafe dake 'kanwar shaid'an?(wa"iyazubillah, Allah karabamu da mugunji)

Zuwa nayi akan al' amarin mij..... Hannu yad'aga mata, duna yasanar dani komai mai kike so ai masa,

boka sonake amaidashi Bawa na sai yadda nace haka zaiyyi kar yaji maganar Kowwa sai tawa ko kara nace karya tsallaka...... tsawa yadaka mata wanda saida ta firgita, yace indan wannan angama sai mai kuma,?

   d'azu naganshi da wata yarinya..... Takwashe duk yadda sukayi tafad'a wa boka, karki damu dan wannan zansa aljani tamu yayi mun bincike inyaso sai asan yadda za'ayi,kud'insa tazube masa,

    Wata ashar tamaka masa wacce itace matsayin godiya, dariya yayi wacce saida dajin ya amsa, tashi kitafi yadaka mata tsawa wacce tasa tasaki fitsarin da ya matseta tsabar tsorata da tayi,

      Bata dawo gida ba sai bayan sallar magrib, Koda tadawo batasameshi ba dan yana masallaci, itama hakan yaimata dad'i, direct bedroom d'in ta tashiga wanka tayi ta kwanta dan tagaji sossai, ita sallah dama ba yinta ake ba,
.......................................................

Mum tunda suka shiga gida take rarrashin zainab,
har tasamu tayi shiru, sannan tabarta d'akinta tafito tana fitowa taga Ma"aruf yashigo wani kallo taimasa wanda yasa jikinsa yayi sanyi,

mum kam kitchen tashige tasoma aikinta,

      Harta fito yana parlour a zaune, ganin tana shirin hawa sama ne yasa yayi saurin isa gareta had'i da Kiran sunanta,

Lafiya?

tafad'a Fuskarta a
tamke, dan Allah mum kiyi ha'kuri..... Kamar jira take....... inyi ha'kuri kace ko? to naji zanyi ha'kuri amma kafad'awa matarka tafita a harkar yata,

      Harkai ma dan mu'amala dakai ba dole bace,

saboda kishin banzanta zata sabauta mun ya to bazan d'auka ba, lallai kaja mata kunne tafita harkar zainab domin zainab amana ce a gurina kuma duk wanda yanemi yaci zarafinta wlh sai inda 'karfi na ya'kare,

    Shidai ha'kuri kawai yake bata dan yaga yadda ranta ya'baci,da'kyar yasamu ta sauko,

*Wannan kenan*

Rukayya na cikin bacci taji kamar ana Kiran sunanta,

idonta cike da bacci tabud'e su, wata razananniyar'kara tasaki wanda badun yayi saurin rufe mata baki ba da duk al'umar gidan suntashi,

       Cikin muryarsa mara dad'in saurare yace...... Kibani had'in kai burin ki yacika na juya mijinki kamar waina a tanda, matu'kar kika yarda dani, zan baki duniya a tafin hannunki zan maidaki maccen da tafi ko wacce macce daraja agun mijinki zansa yatsani mata zansa yadaina ganin kowace macce a matsayin macce zansa yasoki ya girmama ki.......

tunda Rukayya tayi tozali da boka d'an nanu, gabanta ke bugawa har lokacin da yafara magana wayoo itakam tashiga ukku ta ina zata soma had'a jiki da wannan 'kazamin? ,ta ina zata iya bawa wannan Jikinta?


Ina..... itakam duk jarabarta bazata iya kwanciya da wannan abun ba............

*To fa ga'koshi ga kwanan yunwa*😱






_Xinnee smart_

*Follow me on Instagram* @xinnee smart

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Where stories live. Discover now