🥀🌺🥀FAHIMTA 🥀🌺🥀Part 7

Beginne am Anfang
                                    

     To zainab inason Jin ta'kaitaccen tarihinki saboda bana d'aukar mutum aiki batare da sanin daga Ina yake ba duk da dai uwani tafad'a mun ke yar kano ce, amma zanso ji daga bakinki dan zanfi gamsuwa,

      Sunana zainabu kamar yadda nafad'amiki, kuma ni marainiyace, banida kowwa sai kakana wanda yahaifi Mahaifina, ina zaune tare dashi da matarsa wacce........ sai kuma tayi shiru tana hawaye,

       Tausayinta ne yakama hajiya Aisha, cike da tausayawa tace.... kifad'amun komai kinji yata tunda naganki naji hankalina ya kwanta dake kid'aukeni tamkar mahaifiyarki,

Nan zainabu takwashe komai tafad'a mata, take tausayin yarinyar yasake kamata, dan Allah yayiwa hajiya Aisha tausayi kamar me?

      Zainab kiyi ha'kuri da rayuwar dakika tsinci Kanki a baya, kid'auka zuwanki gidannan alkhairee ne kuma insha'Allahu zantaimaki rayuwar ki, inafata kina sha'awar karatun boko, kai ta gyad'a mata, to Masha'Allah,

    Insha'Allah nayi al'kawarin tsaya miki kiyi karatu, cike da farinciki zainabu taimata godiya,
.......................................................

Cikin sati biyu aka gama yiwa zainabu wacce tadawo zainab komai nashiga makaranta, a primary six aka Sakata, makarantar private ce ta masu kud'i, haka kullum driver ne ke kaita yad'auko ta,

     Rayuwar zainab dai tacanza gaba d'aya, yanzun sam bata cikin damuwa, tamaida hankali sossai a karatun ta dan sam batada burin da yawuce karatun dan dashi ne take ganin zata taimakawa kanta da malam,
.......................................................

Mummy....... Mummy, zainab ce ke' kwalawa hajiya Aisha kira, harta isa Kitchen , a kitchen tasameta tana tafaman bada umarnin ayi wannan ayi wancan,

Mummy fa kinaji inata kiranki.. tafad'a cike da shagwa'ba dan azamanta na wata d'aya da sati d'aya a gidan sun saba sossai da mum, dan mum mace ce wayayya, wacce ta iya zama da mutane,hakan yasa basu jimaba zainab tasaba da ita, tun zainab nace mata hajiya kamar sauran maikatan gidan,taita mata fad'a had'i da fad'in bata dauke ta mahaifiya ba shine zainab tabata ha'kuri, nan tace ta ha'kura kuma daga ranar tadinga kiranta mum dan haka yayanta ke kiranta, take zainab ta amince dan sossai take ganin 'kimar matar dan haka take ganin ba abunda bazata iya yimata ba,

    Yar mum lafiya wannan kira haka? Mum sonake infad'amiki yau zamuje quize d'in danace miki zamuyi da others schls, inaso kiyimun addu'a,

    Murmushi mum tayi to Allah yasa ayi lafiya a'kare lafiya yasa Baby na tayi nad'aya, dariya zainab tayi, amin amin mum ur prayers is always making me happy, addu'o'in ki suna sani Jin ni ba marainiya bace mum, I love you so very much, dariya mum tayi mai had'e da tausayi, garki damu zainab inatare dake insha'Allah bazakiyi marai ci ba, ta'karasa fad'a tana shafa kanta,mum bari intafi Kar inyi latti, OK Baby, au zainab namanta ban fad'a miki ba yaufa yayanku zai dawo, wani irin fad'uwa gaban zainab yayi sai dai kuma batasan dalili ba danhaka kawai sai tabasar da fad'in Allah yadawo mana dashi lafiya, can't wait to see him, dariya mum tayi....... tafi dai karki makara, OK mum byee, adawo lafiya..... Da kallo mum tabita ha'ki'ka tana tausayin rayuwar yarinyar,sossai take Jin 'kaunarta a ranta,
......................................................
Waya yakeyi da kb lokacin da jirginsu yasauka baiganshiba, wai kb kana inane? amma ai tunkafun mu' karaso nakira ka... nidai kana Ina?..... gani abayan Mr M M...... Juyawa yayi yaganshi sai dariya yake masa, Shima Murmushi yayi dan ba kasafai abu kesakashi dariya sossai ba,

mtss Kaidai kb idan baka zolayi mutum ba bakajin dad'i,... dariya kb yayi to ai Kaine mutumun kacika gaggawa..... no nibanada wata gaggawa bnsaniba dai ko son ganin zainab ne kesani gaggawa,? Ya'karasa fad'a lokacin da yake shiga motar,

            Motar tayi shiru kb, tu'kinsa kawai yake yayinda ma'aruf, ke faman sana'ar tasa waton kallon picx din zainab yana Murmushi, kb ne yajuya yadubeshi,

  Aboki kana bani mamaki,

dame fa? Ma'aruf yatambaya batare da yadubeshi ba haka kuma baidaina kallon picx din ba,

          Kawai dai yadda naga kakwarewa son wannan yarinyar shine abun yake ban mamaki, musamman idan natuna da irin manyan big girls d'in dake azabar sonka daga ba'ka'ken Fata zuwa jajayen Fata amma kai sam hankalinka baya kansu sam, unfortunately kawai sai naji kacemun kana son wannan yarinyar wai kasan lokacin da kafad'amun ina a tsaye ne amma saida nazauna dan nikam bana tunanin akwai abunda zaija hankalinka akan yarinyar, yah she is beautiful for Real but I don't think that is the reason why u easily fall in love with her, coz nasan kaga kyawawa daban daban harma wad'an da suka zarta ta a kyau da komai,in fact she is too young to be in love with, first of all ma yarinyar fa yar gidan matsiyata ce  her father is a very poor man...

Wani irin duba yaimasa wanda saida yaji shakkarsa, tunda yafara maganganunsa baid'agoba sai yanzun.... Tsayar da Motar nan.... Kb katsai da Motar naceeee...... Yadaka masa wata uwar tsawa, wanda kb baisan lokacin da yaci burki ba, ma'aruf sassau'kane amma fa bai iya fushi ba take idonsa suka rine izuwa ja, tsabar zuciya..... Kallon kb yayi... Kb wai saboda nace kakaini gidansu zainab shine katasani a gaba kana fad'a mun ba'ka'ken magan ganu?

No Ma'aruf understand me ok? Bawai ina nufin bata maka raibane...... Look kabeer, kasaurareni dakyau, inaso kagane inason zainab and that is never going to change, dakake maganar naga yanmata kalakala suna sona waye waye to ni tarbiyarsu sam bata mun ba ta zainab taimun dakake maganar wata yarintarta ni bata dameni ba, matsawar dai ni bazata ce namata tsufa ba to nima bata mun yarinta ba,

Koda kake tunanin wai ba abunda nagani a jikinta kb ba jikinta nakeso ba ita d'in nakeso kb zancen arzi'ki kuwa band'auka kana cikin mutanen nan masu wannan banzar tunanin ba dan atunani na da talaka da mai kud'i duk Allah ne yayi su dominkuwa shi dakansa ubangiji yanacewa (inna'akrama kum indallahi atqakum) to danmmi zakayi tunanin nafi 'karfin zainab kabeer? The only thing that I want u to know or anyone else to know  is that I love her and that is never going to change OK?
      Yana gama fad'in haka yafita daga Motar dasauri kb yabishi yanata bashi ha'kuri, da' kyar yasamu ya hakura shima saboda tunanin da yayi na kb ne kawai yasan gidan su sahibar tasa, badan haka ba ai da shida kb haihatan tunda yaciwa abarsonsa mutumci........
.....................................................

Shiru yayi ransa a jagule tun bayan dawowarsa daga gidansu zainab inda yasamu ba'kin labarin da Sam baiji dad'insa ba, wai zainab bata nan bama tagari to inataje??

         Tambayar da yakewa kansa kenan, wayarsa taita ringing harta katse, bai sani ba saida ga baya yaga miss call ganin number mum ne yasa yakira,

Wayar mum dake hannun zainab tana buga candy crossh, ce tayi ringing dakin mum din tanufa dasauri dantakai mata, Jin wayar takusa katsewa ne yasaka tayi tunanin d'agawa, Sunan my son datagani ne yasa tayi Murmushi dan tasan d'an lelen gidan ne, Assalamu"alaikum, tafad'a a tausashe tana jira a amsa shiru bai amsa ba wanda a 'bangarensa kuwa ya amsa amma shi kansa bazaice yafidda sautin amsawar yadda yakamata ba baisan dalili ba haka kawai yaji gabansa yafad'i,...... Yana tunanin ko meye dalili yaji takatseshi ta hanyar cewa hello hello can you hear me?

      Ina mai wayar? ya fad'a a kasalan ce, inda a gurin zainab yazama rainin hankali take taji ta tsaneshi, haushinsa yakamata dama yana jinta yayi banza da ita? Dama miskilancin da mum ke yawan fad'in yana da da gaskene? shine zaifara gwada mata? Tabd'i nikam Sam baimunba duk da mum nayawan fad'in he is a very good and Nice person, but for her yet he isn't at all, muryar mum ce tadawo da ita daga duniyar tunanin zucin data Lula,

   Baby kirana a Kaine? Eh a.... Tafad'a a dan daburce wayar tami'ka mata kawai ta tafi,

mum kam bata lura da daburcewarta ba, kar'bar wayar tayi sukaci gaba da magana yayin da zainab ta tafi ranta a 'bace da wula'kancin wannan d' an na mum, mtss tasaki siririn tsaki a ranta tana sake Jin haushinsa.....................................







_Xinnee smart_

🥀🌺🥀FAHIMTA.... 🥀🌺🥀Wo Geschichten leben. Entdecke jetzt