1

35 5 0
                                    

            💐💐💐💐💐💐💐💐               
            💐💐💐💐💐💐💐💐

                              1

               Rayuwa Kenan!
              Daga Ummu Afrah.

Wattpad @AsmauTuraki
      
Bismillahir Rahmanir Rahim.
Ya Rabbi ka bani ikon fadar Abun da zai amfanar da alummar Manzon Allah (S.A.W), ka tsare harshena da abunda zai cutar da ni da ku a duniya da lahira.

Safiya! Safiya! Safiya! Wai ina yarinyan nan ta ke ne, ana kiranta amma shuru kake ji kamar ba mutum ake kira ba, toh ko tana bandaki ne, ko kuma ta fara sana'ar ta ba. O ni haihuwar Gombawa, Safiya wai baki ji ina ta kwala miki kira ba, haba ace mutum idan ya fara barci kamar wani gawa, wlh ki daina irin wannan barcin. Safiya ta fito daki Gwaggo kiyi hakuri wlh na gaji ne, aikin gidan nan yawa ne da shi, har matsuwa nayi na karasa aikin nan na watsa ruwa na kwanta. Ni Azumi Allah ya kawo ni lokacin da mace zata ce wai aikin gida yayi mata yawa, kin ganni nan har noma nayi, kuma bai hanani aikin gida da kula da yara ba. To idan zaki yi aure kenan in shirya nemo maki mai aiki, tunda ke ba zaki iyaba, wlh gara ki gyara ni dai na gaya miki. Yanzu dai ki shirya kije wajen kakarki kin kwana biyu baki jeba, kafin tace an hanaki zuwa kin dai san halinta. Tabdi! Wlh Gwaggo kuke tsoronta, shiya sa ta ke gaya muku magana son ranta, amma ni da yake tasan halina, tsab muke kwashewa da ita. To mara kunya, kakarki dai ce, ni ba ruwana, maza ki shirya kije. Ni wlh Gwaggo dun dai kin matsa ne amma da ba inda zanje, in har tana son ganina tazo inda nake mana. Ke dai kika sani amma zuwa ya zama dole cewar Gwaggo Azumi.
         Safiya ta fito daga daki Gwaggo na shirya zan wuce, to ga kudin mota nan, bana son hawa mashin din nan, ki nemi tasi, wannan kudin zai ishe ki, ga wannan ki bata lemu ne, kar kije haka hannu na bugun cinya, hmmmm zamu dai sha lemu, dun nima sai na sha. Ke kika sani, Allah ya tsare, ya kare, kuma ya kiyaye, kiyi addu'a kafin ki wuce, ina gaida ta, to Gwaggo nagode.
          A hankali na doshi bakin titi, layin unguwar tamu ba kowa, hakan baya rasa alaka da ranar da ake kodawa, nayi akalla minti goma sha biyar kafin na samu tasi, minti ashirin ya kai ni gidan kakata dake kusa da specialist Hospital Gombe. Mai tasi na saukeni a kofar gidan na biya shi kudin shi, na doshi kofar gidan, da sallama na shiga, gidane madaidaici  ya kunshi dakuna hudu, da ka shigo gidan zaka fada tsakar gidan, wanda ke dauke da rijiya, da gefen da ake wanke-wanke, da ka wuce nan sai dakuna hudu jere suna fuskantar madafi wato inda ake abinci, akwai hanya ta gefen dakunan wanda zai kai ka makewayi wato bandaki. Na sake yin sallama a daidai kofar daki na farko, daga ciki a ka fito ana amsa sallamar.
          Yau kece a gidan namu lallai muna da manyan baki, cewar wata matashiyar mata wadda akalla shekarunta za suyi arbain da biyar, ta shimfida tabarma tana fadin cikin dakin zafi ba wuta, bari mu zauna anan yafi iska, zauna ga tabarma nan, na zauna nace Mama ina wuni, ya gida, ya zafi, ya aiki, ta amsa tana murmushi, lafiya kalau safiya, ya kakar taki, tana lafiya, na amsa lafiya kalau mama, Hajiya fa ko ta fita, tana nan bari na dibo miki ita, na dai ji tana fadin zata kwanta, tana cikin maganar sai ga wata dattijuwa ta fito hanyar bandakin rike da buta, akalla shekarun dattijuwar za su kai sabain da biyar zuwa tamanin, fara ce, tsayin ta matsaikaici ne, jikinta ya tsufa amma kuma bai yi tsufan tsoro ba, saboda kulawa da kuma abinci mai kyau, amma da ganin ta kasan tsohuwa ce, musamman gashin ta da yake fari tas.
      Tana shigowa tsakar gidan ta ajiye butar tana fadin wa nake gani haka, murmushi nayi nace aljana ce, ta rike baki tace  kiga abunki ke kadai, wadda ta kira da mama tayi dariya tana cewa kin zo kenan zaki dameta, Hajiya ga tabarma na shinfida mana saboda ciki zafi, gashi har yanzu ba'a kawo Nepa ba, tace nima nan zafin ya hanani barci, ta zauna akan tabarmar tana fuskantar Safiya, yau kin tuna ni kenan, wata nawa rabon da kizo gidan nan, nayi murmushi nace, ai kin san inda nake, da kin so ganina da kinzo ai.
       Ta bata fuska naki naje din, me zan tsinta idan naje gidan Aisha, nace idan kinje wajen ta kika je, ko wajena, matsalar ki kenan masifa kamar kin fi kowa, shiyasa bana son zuwa wurin ki, mama ta aje kwanon ruwan sha gabana tana fadin, ku dai in kun hadu sai kun yi fada, wallahi mama Hajiya ce, ita a komi sai ta nuna ita masifaffiya ce, O ni Hafsatu! Yanzu safiya ni kike cema masifaffiya, toh karya nayi, in kowa yaki gaya miki ni dai dole in gaya miki gaskiya, kin cika masifa, wato ke ba kyajin tsorona ke nan, toh Hajiya meye abun tsoro, masifa ce zaki yi nima na iya sai muyi, ba shikenan ba. Allah ya shirye ki Safiya, Amin tare dake Hajiya.
       Na mika ma mama dake gefen tabarma ledar lemun nace mama ga tsarabarki ke kadai, tayi murmushi ta karba tana godiya tare da fito da lemun daga cikin ledar. Hajiya tace Kawunki Bello kika hanawa lemu bani ba, na juyo nace kedai kika sani. Ban dade sosai ba nace to Hajiya ni zan wuce, dama zuwa nayi na gaisheki, to bari na baki kudin mota, nace to ki kawo masu kauri, ta fito daki dauke da Leda tace ga wannan ke nake ta ajiyewa, na karba nace to nagode, ta sa ke miko mun kudin tace gana mota, Allah ya tsare ya kare, duk wanda ya nufi zuri'a ta da sharri Allah ya nuna mai abunsa, a gidansa, a dakinsa, Amin Hajiya nagode. Da kike addu'ar nan na kalleki kamar wata ustazuwa, kefa safiya abun arziki bai karbeki ba, mama ta fito daki da Leda, safiya ga wannan ba yawa, mungode kwarai ki gaida kakarki. Na amsa tare da godiya suka raka ni har bakin kofar gidan.
Koda safiya ta isa gida Gwaggo na tsakargida ta shimfida tabarma tana sauraren radio. Ta karasa wurinta ta zauna, Gwaggo radio ake saurare, eh naga zaman kadaici zai dame ni, kin same su lafiya, lafiya kalau suke, kowa na gaida ki har da masifaffiyar, wai ba zaki bar halin nan naki ba koh, kakar kice ko kina so ko baki so, ni dai ba ruwana, hmmmmm naji ni dai ga tsaraba na samu, ledar da Mama ta bani hijabi ne mai kyau kalan danyen haki, ledar Hajiya kuma Atamfa ce yar Ingila mai kyau shima, to kin gode Allah ya amfana. Gwaggo me zamu girka abincin dare, ki nemi abun da zaki ci, ni dai ina da sauran fura dana dama dazu shi zan sha. Bari na kira Yaya Mu'awuya Allah yasa yau zai zo, in roke shi ya biya wurin Aroma Restaurant BCJ yayi mun takeaway, yace miki yana da kuddi ne, ai akwai Eco bank main branch a kusa da wurin sai yayi withdrawing, balle yanzu kowa yayi upgrading, kusan duk wajen kasuwanci in dai babba ne suna da nasu Pos, Atm card zaka basu suyi withdraing kudinsu a dawo maka da card din ka. Bari dai na kira shi.
  Wacece Safiya, ina iyayenta suke, meya sa take zaune da kakarta ta gefen Uwa, alhali kakarta ta gefen Uba na nan da ranta, me ya kawo wannan habaicin dake  tsakanin safiya da Hajiya, ku biyo ni domin a cikin littafin Rayuwa kenan, domin amsa muku tambayoyinku.
     
Follow
Vote
Comment and
Share

💐💐💐💐💐💐💐💐 Rayuwa Kenan! Daga Ummu Afrah.                 💐💐💐💐💐💐💐💐Where stories live. Discover now