2

8 1 0
                                    

Rayuwa kenan by Ummu Afrah  
              Wattpad @AsmauTuraki                 
                                  2
Ina mata yan kwalisa, ku hanzarta ku garzayo Minour.gees_collection, an tanadar maku takalma da jakunkuna yan yayi, haka ma akwai laces, atamfofi, jallabiyoyi da duk wasu kayan kawa na mata da kuka sani, domin karin bayani a tuntubi 09069941241 ko kuma shafin ta na Instagram Minour.gees_collection. Za'a samu discount idan aka ce, daga wurin Maman Afrah ne.

Bayan Magrib tana zaune a palour tana cin abincin da Yaya Mu'awuya ya kawo mata, bayan ta sha korafin rashin son girki. Fried rice ne daya sha kayan lambu, sai coselow a gefe da cinyar kaza, tana ci tana shan Fanta daya hado mata da shi. Gefenta Gwaggo ce da Mu'awuya ke maganar rashin zuwan Mahaifinsu wurin su da kuma rashin son yaran su zauna wurinshi. Safiya dai na jin su bata sa musu baki ba, saboda matsalar mahaifinsu ba yau ya fara ba, maganar taki ci taki yankewa, tana gama cin abincinta tayi musu bankwana ta wuce dakinta ta kwanta. Washegari bayan Safiya ta gama duk aikace-aikacenta na gida, ta zauna tana taya Gwaggo gyaran zogale da zasu yi dambun shinkafa da shi na rana. Gwaggon ke gaya mata tunda ta kammala makarantar sakandare ya kamata ace ta nemi abun yi in karatu zata cigaba in sana'a zata yi tunda mijin aure be zo ba. Gwaggo ni dai na fi son in cigaba da karatu, kin ga ma sakamakon jarabawar mu ya fito ina son inje in ciro shi. To ki shirya idan anyi la'asar nan kusa damu ai akwai shagon computer sai kije ki ciro, a'a gaskiya Gwaggo ba nan zan ciro ba, kin ga wannan shagon dan karami ne, kuma maza sai suyi ta shigowa duk ka takura, amma kin ga wurin Alkasim Computer Center din nan, shagon akwai fadi sannan ga computers da yawa sai ka zaba, idan ma kana so za'a bari kayi aikinka da kanka, kin ga ai nan yafi ko? Sannan ina son in biya Dada eatery akwai abunda nake son saya anan. A'a kawai kice kwadayin ki ne ya motsa, ina ce babanki yana turo miki kudi kowane wata, to kiyi kwadayinki cikin kudin, ni kudin mota kawai dana ciro result zan baki, dun haka sai ki hanzarta ki gama abincin rana, sai kije da wuri kin san bana son kina yin dare a waje. To gwaggo bari ma na tashi na dora shinkafar ya fara sulala. Cikin natsuwa da kwarewa ta gama dambun shinkafa da yaji kayan lambu da zogale, tasa ma kowa a nashi cooler ta aje a dinning table. Bayan ta shirya taje wurin Gwaggo ta karbi kudin mota da kudin printing din result din, bayan ta sha gargadin ta kula da kanta ta tsare mutuncinta. Da isan ta shagon taje wurin reception tayi ma wanda ke zaune a wurin bayanin tana son tayi printing din result dinta kuma ta tura a email din ta, ya tambayeta ko tana son wanda zai taimaka mata, tace a'a zata iya da kanta, ya bata wani slip mai dauke da code numbers wanda zata sa a computer ya bata access tayi abunda zata yi. Ta nemi computer wanda yake kasan fanka ta zauna, a hankali take sarrafa computer har ta tura result din wurin printing, sannan ta fara kokarin tura result din a mail dinta. Wani sassanyar kamshi taji yana shiga hancinta, bata tantance wane irin kamshi bane taji sallama a kusa da ita. Amsawa tayi ba tare da ta kalli wanda yayi sallamar ba, ji taji anja kujerar gefenta an zaune, idonta na kan screen din computer ta cigaba da abunda take yi cikin kwarewa. Bayan ta kammala tana shirin mikewa tsaye taji ance dun Allah ki taimaka mun, sai ta juyo ta kalli mai maganar saurayi ne dan shekara ashirin da takwas zuwa talatin, shi ba baki bane, amma kuma skin din shi yayi kama da irin black arabs din nan, yana sanye da milky colour din shadda, ga hular nan da ake kira 'Jad dara' yasa, hannunshi akwai zoben azurfa da agogo baki, duk wadannan abubuwan na tantance sune a cikin seconds biyar, uhum lafiya, dun Allah so nake ki taimake ni ki duba mun result din sister dita, naga kema shi kika duba, ai da kayi bayani a reception zasu taimaka maka, to wai naga kema shi kike dubawa shiyasa nace bari nazo ki duba mun, kayi hakuri sauri nake yi, na juya na wuce wurin reception na karbi takardun dana yi printing, na tambayi nawa ne kudina, sai yace ai an biya, waye ya biya, wancan mutumin daya je wurinki shi ya biya, da ya baka kudin kuma sai ka karba, koda yake ai kai ka gaya mishi ko nawa ne. Rai na bace na koma wurin da mutumin nan yake zaune, na isko shi yana waya. Dun Allah Umma ki daina biyema yaran nan shikenan duk na fita sai sun san yadda suka yi suka sani aiki, a'a kiyi hakuri zan sayo, ya kashe wayar, nawa ne kudina da ka biya na baka, ya kalleni yayi murmushi, a'a ba sai kin biya ba, to dun me zaka biya mun kudin nace ma bani dasu ne, a'a hajiya baki yi kama da wacce bata iya biyan kudinta ba, ni dai dun Allah nayi. To nagode Allah ya biya.
   Na fito bakin titi na hau adaidaita zuwa Dada Eatery, muna isa na biya shi kudin shi na shiga wurin, da gaskiyar Gwaggo kwadayi na ne ya tashi, wurin sun yi suna wajen sayar da Grilled kaza mai dadin gaske, nayi order Babbar kaza daya da Chi- exotic manya kwali 2. Nasa ayi mini takeaway din shi, na karbi kayana na fito waje, a bakin kofar nayi kicibis da wani zai shigo, nayi saurin matsawa baya Allah yasa na rike ledojin gam da sun zube, na dago fuskata naga waye keson ture ni haka, biyo kuma kayi? Tambayar da nayi masa kenan. Nima sayyayya nazo yi, ba biyo ki nayi ba. Kiyi hakuri ba ture ki naso yi ba, hankalina yana kan wayata ne, ya matsa baya, bismillah ga hanya, na wuce shi cikin rai na ina cewa, ba wani haushi ne ke damunka dun ban duba ma result ba. Na fito bakin titi na tare adaidaita ya kai ni gida.
   Safiya Umar 'ya ce ga Alhaji Umar Isma'il, ma'aikaci ne a Water board dake jahar Gombe. Hajiya Farida ita ce matarsa wadda ya aura tun yana sana'ar sayar da shaddodi kafin ya fara aikin gwamnati. Gwargwado akwai zaman lafiya a tsakaninsu, dun matarsa ta kansance bata hangen abun gidan wani, tana karban duk abunda ya kawo hannu bibbiyu, shima a nasa bangaren yana kokarin ganin ya kyautata mata, ana haka har tayi haihuwar farko ta samu yaro namiji aka sa masa suna Mu'awuya. Yaron ya tashi cikin gata dai-dai gwargwado be rasa komai ba, ana haka Ismail ya ba Farida kudi ta fara sana'a, dama tana da ra'ayin sayar da kayan kwalliya, dun haka ya amince taje kasuwa ita da kawarta Jamila suka saro sarkokin manya dana yara. Ta fara tallata kayanta wurin yan uwa da abokan arziki, haka idan zata je buki tana zuwa dasu ta tallata ma mutane, kuma gwargwado ana samu, haka dai ta rinka yi har Allah ya buda mata, har mutane daga wasu jahohi suna sayayya wurinta tana aika musu, haka ma tana sayar ma masu hada lefe, sannan akwai masu zuwa su sara a hannunta. Mu'awuya nada shekara bakwai Allah ya sake ba Farida haihuwa ta haifi 'ya macce aka sa mata suna Safiya. Safiya ta taso a cikin gata sosai dun a lokacin Umar ya samu karin girma a wurin aiki, albashi ya karu kuma dama be yar da sana'ar shi ta sayar da shadda ba, ya nemi wani amintaccen yaro shike kula da shagon, idan Umar ya tashi wurin aiki sai ya biya ta shagon ya dudduba kayyakin da aka sayar, wanda za'a sake saro wa da yadda abubuwan shagon ke tafiya.
Umar yasa yaran shi a private makaranta, shi ke kai su, kuma ya dawo dasu. Kwanaki nata wucewa, shekaru nata ja, kwatsam wata rana lokacin Safiya tana Jss2, shi kuma Mu'awuya ya zana jarabawar sa ta karshe a Secondary School, Umar ya dawo dasu yana fadin yau celebrating za'ayi Mu'awuya ya kama Secondary dun haka, yau restaurant za'a je aci abincin dare. Suna shiga gida suka iske Farida kwance akan kujera, duk tayi zufa, jikinta har wani jijjiga yake yi, da sauri suka yi wurinta suna tambayar ta meke damunta, amma ina tayi nisa bata ko jin su, ba shiri Umar ya sungumeta sai cikin mota, bai tsaya ko ina ba sai a Musaba Clinic lokacin ma ya lura ashe safiya na cikin motar da ita aka zo, ma'aikatan wurin sun karbeta cikin sauri  suka fara bata agajin gaggawa, Umar da Safiya suna tsaye sai ga Gwaggo ta shigo hankali tashe, Mu'awuya na bayanta, suna nan jigum-jigum, sai ga likitoci biyu sun fito daga dakin da aka kai Farida, kai tsaye suka isa wurin su Gwaggo, suka sa Umar ya zauna dun tun dazu ya kasa zama, cikin tausasa kalamai lokitocin suka gaya musu sunyi bakin kokarinsu amma Farida rai yayi halinsa. Umar banda hawaye babu abunda yake yi, mutuwar ta zo masa kai tsaye, lafiya kalau ya rabu da ita da safe da zai wuce wurin aiki ko ciwon kai bata ce mishi tana yi ba kuma bega alamun wani abu na damunta ba, mutuwa kenan idan lokaci yayi babu jira. Gwaggo salati kawai take yi hawaye na zubo mata, Farida kadai ce 'Yar da Allah ya bata bayan ita ko bari bata taba yi ba, tun bayan rasuwar mahaifin farida Malam Inuwa bata sake shiga rudani da tashin hankali irin na yau ba, shikenan wanda ya bata Farida yau ya dauke ta. Ana cikin haka sai ga Hajiya mahaifiyar Umar ta iso, tana ganin hawaye fuskar Gwaggo ta rafka salati tana tambayar meya faru?
Babu wanda ya iya bata amsa kowa hawaye fuskarsa, Mu'awuya ne yayi karfin halin rike ta ya zaunar da ita, na tambayeku meya faru ba wanda ya masa mini, kai kuma kana zaunar dani, Hajiya Mama ta rasu cewar Safiya, ai sai ta mike kai Mu'awuya da ka kira ni bace min kayi kun dawo makaranta kun ganta kwance ba lafiya, dama ta dade bata da lafiya ne? Innalillahi wa innnailaihir rajiun! Allahu Akbar Farida Allah ya gafarta miki, Allah yayi miki rahama, ba komai tsakaninmu sai alkhairi, Allah ya haskaka kabarinki. Taje wurin Gwaggo tana fadin, Azumi dole kiyi kuka, Allah ya sanyaya miki, ya bamu hakurin jure wannan rashi, insha Allahu can zai fiye mata nan. Haka aka dauki gawar farida aka wuce dashi gida, aka yi mata wanka, aka sallaceta, aka kai ta gidanta na gaskiya. Umar yayi kuka a fili har a zuciya, rasuwar farida ya girgiza shi sosai, be taba kawo mata mutuwa nan kusa ba, tsawon shekara ashirin sun yi zaman lafiya da farida duk da ba'a rasa sabani tsakanin ma'aurata, amma nasu da sauki, tunda basu taba zuwa wurin iyaye sulhu ba, baya tunanin zai samu mata mai hakuri da son zaman lafiya kaman farida ba. Bayan addu'ar uku ya bar yaran wurin Gwaggo Azumi kamar yadda ta bukata, ma'aikaciyar asibiti ce (theater nurse) amma yanzu shekara biyu kenan da tayi retire daga aiki. Ta bukaci a bata yaran su zauna wurin ta kafin Mahaifinsu yayi aure su koma wurinshi. Koda ya gayama Hajiya bukatar Gwaggo kai tsaye tace dama ai ita ya kamata ta rike su, wannan ai sai ita, ni ina zan yi kula da kattin yara, ka bar mata su har sai ka sake wani aure sai ka dauke su, amma dai duk wata ka kai musu abinci da duk abunda suke bukata. Kar ka bar ta da dawainiya kaga taimakon ka tayi, dun in bata karbe su ba, da yanzu muna nan muna cigiyar wanda zai dauke su. Kallon mahaifiyarsa kawai yake yi dun ya saba da halinta. Yace to Hajiya insha Allah haka za'a yi.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 17, 2022 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

💐💐💐💐💐💐💐💐 Rayuwa Kenan! Daga Ummu Afrah.                 💐💐💐💐💐💐💐💐Where stories live. Discover now