page 36

2.7K 201 7
                                    

*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

36
Da madarar yaje asibitin,gwajin farko aka tabbatar itace,hafsa tasha baqar wahala sabi acikinta aka yayyakan yaron cikin kusan 6 month ya soma girma sosai, haka aka ciro mata shi,kuka kam tasha shi,muhammad kuwa be duba dan gantakar dake tsakaninsa da zee ba ya sanya aka damqeta zuwa police station daga ita har qawarta haleema kuwa......

Ammy taji sauqi ba laifi sedai kam ita nata yazo da gaddama sabida hawan jininta ya tashi sosai kuma yaqi sauka,sedai adua,a bangaren hafsat kuwa kwance take tana sharar kwallah,ba wai wahalan datasha ba mutuwar yaron cikinta, sosai ta qwallafa ranta akan wannan cikin, tana nan khairii nata mata sannu sega muhammad nan, ficewa sukai gaba daya suka bar musu dakin, da sauri ta miqe zaune,shi kuwa ya kama hannunta ya riqe tausayinta ya sanya ya kasa maganq,rungume shi tayi tace

"Yaa muhammad nashiga uku nq" tsamm ya qara matse ta ajikinshi yanajin tsananin tausayinta da sabuwar kaunarta na ratsa ilahirin jikinshi

"Noo plss hafsat stop saying that baki shiga komai ba se alkhairi inshaa Allah sharrin su ze koma musu ne ki barsu kawai" ita batasan meya faru ba ta dago kanta ta kalleshi "su waye yaa muhammad?" be damu ba ya bata amsa "Su zeezee mana itana da matar yayanki haleema,sune sukayi poisoning naku keda Ammy da madarar da kukasha,kuma wlhy tunda suka mun asarar baby na sesun gane shayi ma ruwane wlhy" kasa magana tayi tsabar mamaki poison kuma? Ta nanata a ranta,ga mamakinta kuka taga muhammad yanayi sosai kuma,kasa yin kukan tayi ta soma bashi baki

"Hafsat tsabar zainab batada hankali zatayi kisa,kisan ma wai mahaifiyata data haifeni da kuma matana mafi soyuwa agareni da yaron danafiso tunkan zuwanshi duniya,yanzu gashi tamun asaran shi wlhy sena hukuntata sena gane cewar doka tana aiki har cikin gida" Itadai bata iya magana ba sam.

Bincike ya nuna cewar ita zainab batasan guban na kisa bane,haleema ne takawo mata a zuwan na zubar da cikine kawai,sannan batasan cewar tare da Ammy za'a shaba,ita kuwa haleema tasan na kisa acewarta tunda take da shaam hafsat ce take takura ta,yanzu dan taga ita bazata sameshiba shine ta hadashi da wata can ake wulakntata ita, tunda ta gane mijin Qawarta ne hafsat ta aura se kawai ta dinga zugata akan su hallaka hafsat,ganin bazata yadda da kisa ba ya sanya ta bullo ta hanyar a zubar mata cikin ashe fa dama kisan ne.......hafsat sun dawo gida duk sun samu lapiya,anan kuwa aka soma zana court inda atake sanida duk sunyi confessing aka yankewa zee zaman gidan kaso na wata uku ko tarar kudi naira dubu dari biyar yayinda aka yankewa haleemah zaman gidan kaso shekaru ashirin, tun a cotun ta haukace ta soma sambatu kuwa iri da iri, kamar wata zautacciya duk wani mugun aiki datakeyi haka ta dinga fada kuma tunkan ajata zuwa gidan kason Allah ya amshi ranta acikin dubannan mutane,wannan abin ya daga hankalin zeezee yayinda mahaifiyar haleema ta haukace a take ta wurgar da zani tayi waje,shammaz kam beso hakan ba sam yaso yaga tuban haleema ta koma ga Allah amna yazeyi haka Allah ya tsara tata kalar rayuwar,yayi kukan abubuwan data masa musamman daya kasance tana bin maza wanda ya dade yana zargin hakan, Zeezee kuwa ba irin hakuri daba ta baiwa muhammad ba amma yace sam baze hakuraba ya saketa saki daya......

Sosai hafsat ta tsorata da abubuwan dasuka faru, kallonta muhammad yayi sosai yagano tun fitar sa tana wurin daya barta,zama yayi kusa da ita ya kamo hannunta yace cikeda kulawa

"Hafsat dan Allah ki mayarda komai ba komai ba,inshaa Allah zaki samu wani cikin,kuma ire iren su haleemah bazasu sake samun galaba akanki ba,Allah baze bari ba kinji" kwantar da kanta tayi saman qirjinsa tace

"Ba wannan araina yaa muhammad tsoron duniya kawai nakeyi wlhy,ni a rayuwa mena yiwa haleemah dazata bini da wannan sharrin ban tab'ajin banji zafin mutuwar koda kiyashi ba kamar yanda sam banji zafin mutuwar haleemah ba, abubuwan data aikata sun firgitar dani ace arayuwa mutum ba Allah a ranshi? Baya tsoron mutuwa baya tsoron had'uwarsa da Allah sam,baka gudun cin hakkin mutane ka mayarda neman maza kamar shan pure water da aurenka,sata sekaje beran masallaci, yaudara ba komai bane,ni naji tsoro wlhy" kallon sosai ya mata

"Nagodewa Allah daya bani ke a matsayin mata,yanzu zan qara da wani mamakin akan halayyar dan adam, zainab da kika gani yar aminin mahaifinane tana soyayya da wani saurayi aka ce seta aureni suna matuqar san juna kamar me,nima kuma inada budurwata sunanta khaleesat, kinsan yan siyasa suna dasan auren hadi tsakanin yayan masu kudi haka mahaifina ya dage akan sena auri zee, nasha zagi a wurin zeezee ba iyaka azatanta santa nake amma duk bana kulata,sabida mahaifina daya bani amanarta,saura kwana biyu daurin aurena da ita taje gun wannan saurayinta,ina zaune khamal yamun waya akan ya ganta hotel ita dashi sun shiga daki,mukazo nida shi a mota muka kwana haka kuwa se 10 na safe suka fito atare daga dakin ita bata ganni ba amma nina ganta sarai, haka na roki kamal akan ya bar maganar iya mu, aka daura aurena da zeee, har mukayi wata daya da sati biyu ban taba kwanciyar aure da ita ba,bansan meya sanya zee ta kawomun kanta ba sedaga baya,bayan ta haihu na fahimci cewar ta gano tanada ciki ne yasa tazomun kar wani abin ya taso,sabida na lissafa ba'a haifar yaro da 8 month kenan haduwar ta da wancen ta samu shigar ciki,haka akazo Nu'aiym se rikidewa yake yana komawa tsohon saurayinta sannan da karfi da yaji ta sanya na maidashi gun mahaifiyata, sam banajin qin yaron se tausayi dayake bani sabida nasan bashi da gadona,kuma uwar ma ga cutar dashi,se nabi ta musulunci tunda akace idan har 6 month sun cika sannan aka haifi yaro koba naka bane anbar maka shi, har yau dum raini. Wayon da zee kemun bata san na san da wannan ba,in taqaice miki yau shekaru na hudu cur banyi kwanciyar aure da zee ba sam bata bari,roqona take in saketa taje ta komawa saurayinta,abinda ya sanya ban saketaba sabida indai zataje tofa sena sanarwa duniya yaronta ba nawa bane,sabida in tabbatar har D.N.A tst namana nidashi wani lokacin an tabbatar ba jinina ajikinshi ,so yanzu ke me zaki kira wannan? Mezata cewa Allah?"

Mom Nu'aiym

Se haquri ina busy ne kuyi manage da wannan.

BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho BaneWhere stories live. Discover now