page 19

2.3K 166 0
                                    

*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)

Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

19

Shammaz zaune a office d'insa duniyar habaki d'ayanta baqi take masa yarasa yazeyi akan zancen hafsat,sam mahaifinsa yaqi ya basa fuska,gaisuwar sa ma dak'yar yake amsawa,gashi gaba d'aya Haleemah ta gama rainashi zaman auren kawai sukeyi amma sam bajin dad'i har qasar take bari bada izininsa ba,yama rasa tayaya zeyi gashi dai hafsat yanzu kusan shekaru hudu da barinta qasar acewar Mommy ma takusa dawowa domin tace qasarta zata bautawa,amma duk inda yaje da zancenta ba sauqi har wurin hajiyar su wato kakarsa......

Sosai hafsat ta tara abubuwan burgewa ajikinta,yanzu batada wata damuwa ita da uncle say sambarka,duk da yabar qasar ya koma Niger amma koda wane lokaci suna maqale da juna awaya,sunyi wani sabo mara misaltuwa,kwance take acikin dakinsu tana karatun wani English novel me suna she's with me,khairii ce tashigo ta kalleta taja tsaki

"Allah hafsa kin shiga ukunki kekam,wannan wane irin karatun jarabane kikeyi haka? Kinfasa tafiyarmu nanda kwana ukune, amma meye naki na tsayawa karatun wani banzan novel,kofa kayanki baki had'a ba wannan zumud'in na uncle say duk gulmane abaki kawai ya tsaya bekai zuciba" bata kula taba,kuma sarai tasani bawai kulatan zatayiba wannan ne ya sanya taja wani tsakin ta shiga had'a musu kayan har hafsat,se zumud'in ta takeyi ita kadai tana mitar san banza irin na hafsat....

*NIGERIA*

Gaba d'aya hafsat gani takeyi tamkar mutanen dake yanga akan jirgin basu san ciwon kansu ba,sakkowa ajirki sekace wanda ya tasa tray na samosa agaba,se yanga sukeyi tamkar basa taka qasa,tun a airport na sultan muhammadu maccido dake garin sokoto ta fahimci sauye sauye da dama da aka samu a garin,idon tane ya sauka akan masoyinta uncle say,shekara d'aya kenan rabon data ganshi,takowa tayi a hankali taje har gabansa ta tsaya ta sakar masa lallau san murmushi,kankace meye wannan kuma idonta ya cicciko ta soma kwallan murnar ganinsa,a hankali ta furta "i so much miss u Baby say" murmushin shima ya sakar mata sannan ya ja hannunta ya riqa cikeda kulawa yace

"Rose kukan kuma na menene,daga had'uwarmu zaki fara ko Baby?" murmushinta ta fad'ad'a batare data dena zubar wahayen ba tace "Uncle say bakada labarin akwai hawayen dadi? sune nake zubarwa tsabar murnar ganinka" Janta yayi suka juya se mota,dama shi kadai yazo tarar su suka shiga suka wuce gidan abba haris kai tsaye,se labarin soyayya sukeyi cikeda qauna da tsananin murnar ganin junansu......

Satinsu daya agarin aka tsayarda ranar auren say da hafsat nanda watanni hudu masu zuwa,dama can tun tana india akayi tambayar auren kowa ma yasan da zancen auren.

*Bayan kwana biyar*

Tun da hafsat ta dawo basu hadu da yaa shaam ba har yau,gwara ma matarsa sun had'u a gidan daddy,shi kuwa yana sani yake gujewa ganinta sabida gudun karya tayarwa kanshi cutar so da ta jima tana addabar zuciyarsa,yau dai seda ya kira qaninsa da safe ya sanar masa cewa suna gida sannan ya shirya zuwa gidan na daddy,bashida lamarin hafsat ta dauki al'adar waje bata fiya fitaba seda yamma,wannannya sanya ta zuro doguwar rigar jallabiya ja har qasa tasha shape da bakin mayafi da uban qaton madubin ido,lips dinnan sunsha red lipstick,a hankali take taunar cingam dake bakinta tana yamutsa fuska,yau sam setakeji tamkar batada lapiya driver din na parka wa tafito a yangace zuwa cikin gidan daddy cikeda yanga, A hot na gidan ta hango yaa shaam lokaci d'aya qirjin ta ya mugun dokawa,adu'a taci gaba da karantowa ta dauke kanta tamkar bata ganshi ba,murya ya d'aga yace "Hafsa zo zan" qirjin ne yaci gaba da mugun dokawa amma bata ko waigo ba, yi tayi tamkar bata jishiba, shikuwa ganin haka kuma yasan sarai tana jinsa ya sanya yayi saurin tasowa yafara takowa zuwa inda take,ita d'inma sauri ta qara amma ina kan ta isa kofar dazata sadata da cikin gidan ya rigata,tsayawa tayi cak ta runtse idonta ta sauke wata nannauyan ajiyan zuciya,a hankali cikin sanyin murya yace

"Hafsat ya kwana biyu" bud'e idonta tayi a hankali batare da tayi magana ba,tana kallonshi ta cikin gilashin idonta,ya kuma cewa

"Bazak gayarda yayan naki ba?" hannu ta saka ta zare madubin idonta sannan ta lumshe manya manyan ida nuwanta tace "Yaa shaam ina wuni,ya kwana biyu?" murmushi yayi shima hade da daura hannunsa saman qirjinsa yace "Lapiya qalau hafsat yaushe agarin?" murmushin itama tayi tace

"Au baka masan zanzo ba aikuwan na cika tara,seka biya" wani dad'i ne ya xiyar cesa ganin ta sakko,besan kuwa nan umarnin yaa say kawai take bi ba abun beyi wani damuntaba,dak'yar ma take masa murmushin,shikuwa se dadi yake ji ya kalleta sosai

"poojan dady an girma fa sosai yanzu" murmushin takumayi tace

"yaa shaam d'in daddy kuwa ya zama tsoho tunda qanwarsa ta girma" Murmushi yayi ya shafi gefen fuskarsa "Ki shiga ciki yan matan Yaa shaam" wata dariya tayi me cikeda ka raina kanka ta wuce ciki kawai....

Tunda yaa shaam yaga hafsat na sakar masa fuska se kawai ya qudurta aranshi shine ze angwance da ita,da wannan har tunaninsa ya kaishi ga zuwa ya ziyarci Innah wato kakarsu ta wurin iyayensu maza....

Zama yayi ya saka mata uban kuka,akan wai ai asiri aka masa ada,yanzu kowa yasan yana san matarsa Amma abba haris dasu daddy sun hanashi sun baiwa wani har an saka rana nanda watanni hud'u,Innah kuwa tacika fam ta fusata,i da take shiga batanan take fita ba akan za'a hanawa magaji mata,aikam tana da rai basu isaba,da wannan tayi kiran kowa da kowa a gidan ta!!!!

Kallonsu tayi bayan kowa ga natsa yana saurarenta tace dasu "Dama akan zancen hafsat ne da Magaji,tayaya dukkaninku kunsan airine yayi tasiri akan shi a wancan lokacin yanzu zece yanaso amayar masa da matarsa hankalinsa ya dawo jikinsa amma tsabar bakusan muhimmancin zumunci ba zaku rufe ido ku baiwa wani inada rai banma sani ba,to wlhy kunyi kadan kunji na gaya muku,na baiwa shaam auren hafsat tunda dama saku d'ayane a tsakaninsu,kuma na dawo ma da bikin wata me fita" kallonta Abba haris yayi cikin rudu yace

"Innah dan Allah karki taso da wannan maganar yarinyar nan yanzu ta samu wanda takeso,kuma bazamu zamo qananun mutane ba munyi magana kuma mu dawo muce dasu wai amfasa,dan Allah ki rufa mana asiri maganar nan tunkan ta tashi daga nan mu barta" kanwar haris me binsa ma tasa baki kowa dai yayi magana tana jinsu seda duk suka gama sannan ta kallesu tace

"Dukkaninku nan baku isa kun sauyan ra'ayi ba,sannan idan qaranta kuke gudu ni nan bana gudunta,ku sani wlhy ko yau na mutu duk wanda ya sauya wannan maganar tsakanina dashi Allah ya isa ban yafe ba" zaro ido sukayi dukkansu suka shiga lallami da ban baki,amma qememe tace dasu acikinsu ma wanda ya kuma tada zancen bata yafe ba,indai ba akan zancen bikin bane,kar wanda yazo mata dashi kuma kartaji sun sanar wa Alhj wato mahaifinsu" ai gaba d'aya mamaki ne ya damqe ilahirin su,suka silale d'aya bayan d'aya.....

Mom Nu'aiym ce

BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho BaneWhere stories live. Discover now