page 17

2.3K 186 5
                                    

*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
Wattpadd@ 68billygaladanchi

*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                   17

Yaa shaam juyawa yayi zuwa gidansa,ransa a b'ace  yarasa dalilin sha'awar hafsat da Allah ya jarabeshi da ita,gashi sam shi har yanzu beji yana santaba,amma dai tunanin ta kullum dashi yake kwana yake kuma tashi.......hafsat har washe gari idan takira wayar uncle  say baya d'agawa duk hankalinta ya tashi, se messages take sending mai na ban hakuri sekace ita ta masa laifi,ganin dukta damu mero ta kalleta tace

" kulele lapiya dai?? Naga tun jiya kamar kina cikin damuwa?" lumshe idonta tayi sannan tace a wahalce "Uncle say ne yake fushi dani mero,sam yaqi ya saurareni" kallon nutsuwa ta mata take hankalin mero ya tashi,kaddai ace hafsat san wannan sayyeed d'in takeyi? Inko hakane wannan yarinyar taga rayuwa ita gaba daya kullum san maso wani takeyi,kuma a yanda ta kula koda tana san say din batamasan tana yiba,ta yiyu wannan karon da sabon salon daya zo mata

"Menene ya faru yake fushi dake har haka?" dafe kanta tayi sannan ta zayyane mata komai da ya faru ta qara da cewar

"Amma mero kinga ya dace ace wai ya d'auki zafi dani har haka? Bafa nice namar laifi ba,taya ma za'ayi laifin  wani can ya shafan?" nisawa tayi sannan tace "Tooh hafsat kinsan wani be iya fushi ba ta yiyu bawai fushin yake dakeba ranshi ne kurin a b'ace idan ya huce ze kiraki" kan wani yayi magana wayan ta ya soma qara,jikinta har rawa yakeyi ganin uncle say ne,da sauri ta d'aga ta kara a kunne,kasa magana tayi kurin ta sanya masa kuka me tsuma zuciya a hankali yace

"Rose menene kuma na kukan,ke komai bakida wani uzuri,kizo ina parlorn qasa a gidan daddy" zabura tayi ta suri mayafinta ta sauke da sauri,taje kusa dashi ta zauna tace tana sharar kwallah

" Uncle say im so sorry" kallonta yayi yace "meye na bani hakuri kuma me kika mun,naga cols dinki ne,inata fama attending patients jiya goda naje gida it was late i coul'nt col u back,yau kuma tun asuba aka mun waya muna emergency thereter,i had to go there wlhy kina raina,shiyasa da sauri ina gamawa da office nazo na ganki kiyi hakuri"  share k'wallan daya gangaro mata ta saka hannu ta share sannan ta kalleshi tace

"Ni na damu na zata fushi kakeyi dani,rabon danaci abinci tun jiya ma" zaro ido yayi yana kallonta "Wlhy ina ganin mutane masu wawta na dad'e sosai banga irinkiba hafsat,tayaya bakimun laifin komai ba zan soma fushi dake,maza tashi muje na siya miki abun dadi a season 7" murmushi ta masa tace "Karka damu zanyi samosa a gida" B'ata fuska yayi

"Lallai ki tashi mu tafi,banasan shashanci" ahaka taje ta sako hijab tazo suka fita,suna fita yaa shaam na danno kan motarsa acikin gidan,qwafa yayi yace aranshi lallai dani kuke zancen sena qulla maka sharrin dabakasan akwai irinsa a duniya ba !!!!!.....

    *Bayan wata d'aya*

Tun bayan da su poojah suka koma school yaa shaan yake cikin damuwa,da kanshi ya fahimci cewar lallai ko bayan sha'awa san poojah ya masa mummunan kamu ba kad'an ba, gaba d'aya mantawa ma yakeyi da wata haleemah a rayuwar sa kuma sam yadena bata kud'i hasalima baya kwanciya wuri d'aya da ita sun raba jaha ita kuwa dama ba sanshi takeba wannan ya sanya bata damu ba neman mazan datake kawai tasaka agaba tana samun kudad'e dama abu d'aya ya tsayar da ita shine asibitinsa daya saura ta k'wace masa,ganin kuma baya zuwa wurinta azatonta aikin da boka yace ze koma yine na ganin sun kwace asibitin daya kuma cewa lallai ne seya hanashi jin sha'awarta,wannan ya sanya hankalinta yake a kwance,yau shiri na musamman yayiwa zuwa gidan daddy akan maganar auren sa da hafsat wanda yake wannan kadaice mafita agareshi,koda yaje ga mamakinsa daddy haquri ya bashi akan lallai se idan hafsat dince da kanta ta amincewa komawa gidan sa amma muddin ba ita kesan koma masa ba toko lallai ya zame masa dole ya haqura,da wannan b'acin ran ya koma gidan sa.

   *INDIA*

Tun bayan rasuwar matar Dr. Say yake cikin tsananin damuwa,shidai sosai ba kadan ba yake santa over,yaji zafin mutuwar ta fiyeda tunanin me hankali,zaune yake a babban parlor ya rufe fuskarsa da littafin dayake nazari,tunani ne fal a ranshi na suhaila wanda sam bemasan cewar  hawaye sun fara gangaro masa ba,poojah kuwa tajima tsaye akanshi tana nazarinsa wanda shigowarta gidan kenan daga makaranta,a hankalibta sanya hannu ta janye littafin dake saman fuskar tasa ganin hawaye ya sanya ta danja baya a d'an tsorace,k'ura mata ido yayi itama din shi take kallo,zama tayi kusa dashi ta kalleshi cikin kulawa tace cinkin mutuwar jiki

"Uncle me kuka kuma? Meya sameka haka?" d'an juyar da kanshi yayi yace "Hafsat suhaila na,suhaila na nake tunawa,yaushe zan samu macen da zata mayemun gurbinta arayuwa?? Wlhy ina matukar kewarta" tausayin sa ne ya kamata tace jikinta a mace "Uncle say dan Allah ka rage damuwar nan,idan kana wannan kukan mu kuma muce me? Batun yauba na kula dakai sosai kake damuwa da rashin ta koka manta cewar Allah wanda yafi kowa santa mahaliccin ta shine ya karb'e abarsa,kuma arayuwa ba'a tab'a barin wani dan wani kuma Allah shi yasan dalilinsa na dauke rayuwarta alokacin daka fi buqatarta,dan Allah kayi hakuri" kallon ta yayi yace "Na sani hafsat wlhy na sani narasa dalilin daya sanya na kasa cireta araina,kuma kullum tunanina a duniya waye zata mayemun gurbin suhaila? Waye ze soni kamar yanda suhaila take sona,wa zata kula dani kamar yanda suhaila take kula dani?" riqo hannunsa tayi sannan tace tana zubar kwalla

"Nice nan zan maka dukkanin abubuwan nan daka rasa uncle say,meyasa bakasan kawa kanka adalci ne,had'uwana dakai had'in Allah ne sabida haka tun farkon had'uwa na dakai nakeji ajikina i meant for u and u alone,Ban tab'aji araina ina sanka ba ko kadan bantaba jin soyayyarka araina ba,amma kullum ina tambayar kaina menene k'auna? Banida mutumin danike matukar kewa sama dakai aduk fad'in duniyar nan,banida mutumin danike matukar tausayi aduk fadin duniyar nan sama dakai,banida wanda nakejin damuwar sa tawace har raina se kai kad'ai uncle say,banida wanda arayuwa nakejin tamkar zan rasa farin cikina idan yana fushi dani sama dakai,banida wanda arayuwa banida burin daya wuce naganni kusa dashi sama dakai,banida wanda nakejin zan iya sadaukar da dukkanin farin cikina akansa se kai kad'ai uncle say,banida burin daya wuce farin cikinka arayuwa,babu abinda yake qayatar dani se inganka cikin walwala,babu abu mafi soyuwa agareni se ganin farin cikinka inga kana dariya yafi komai saukarmun da nishad'i,a iya tunani wayannan abubuwan ba soyayya bace,k'aunace me zafin gaske,ada nayi tunanin so shine komai se yanzu danake rayuwa dakai na tabbatar wa kaina cewan so shirmene zallah,ada nayi tsammanin cewa akan soyayyar shammaz na shige halin da nashiga na ciwon zuciya se daga baya na fahimci cewar zallar mugunta,cin amana,cin zarafi dakuma wulakantanin dayakene ya sakamun ciwon zuciya,sabida soyayya ruwan shayi ce yana zubewa a qasa kuma sedai kanemi madarar ka rasa shimfidar ruwan banza kawai zaka gani a kasa,kauna kuwa kakkauran kindirmo ce sabida zubewar sa a qasa baze tab'a zama sanadiyar b'acewa kalarsa ba,itace nake maka zallarta,dan Allah uncle say ka k'aunaceni,dukkaninmu muna tsananin buqatar kulawar junanmu" sosai yake kallonta harya kasance ko qiftawa bayayi ya rasa dalilin sa najin komai tamkar a mafarki jikinsa gaba d'aya yayi sanyi,har yanzu hafsat yarinya ce bazata tab'a fahimtar saba idan yace mata kuma bashida hanyar daze bar zuciyarsa ta k'aunace ta sabida wasu manya manyan dalilai,batare dayace mata qala ba ya miqe yabar parlor d'in fuska kici kicin zuciyarnan sam babu dadi a jagule......

*kome hakan yake nufi,da Alama hafsat batada farin jinin masoya a duniya,ba wanda yatab'a cewa yana santa,sannan kuma ita sedai taso wannan taso wancan amma babu wata nasara,Allah ya temaketa dai,muje zuwa kuci gaba da bin alqalamin mom Nu'aiym.....

          

BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho BaneNơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ