LAILAH-DIZHWAR

Depuis le début
                                    

Itama Asiyar yanayin muryata Murmushi take.

_"Lafiya lau Amarya,ya gida ya jiki kuma"_

_"Wallahi lafiya qlau  Angode Allah ya saka da alkhairi ubangiji ya bada lada, ya kawo yara na gari"_

_"Ameen Ameen, muma muna godiya sosai,kuma muna nan muna jiranki"_

Dariya Lailah tayi me sauti ta yanda Asiyar tana jinta.

Bayan sun gama gaisawane ta bawa Ja'afar wayar tukun yayi mata sallama.

Taji dadi sosai, ko yanzu tana da guarantee akan bazata sha Wahala ba dan taga suna da kirki ba kamar yanda tayi tunani bah.

________
Maryam kuwa koda gari ya waye, Bayan tayi wankanta ta shirya ta fito dan yin breakfast, Saida taci ta koshi, ita kadai ce a dining din babu kowa,
  Babu abunda take tunani sai abunda ta gani daran jiya burinta taje ta tambayi Hajiya Babbah ko wace wannan din.

Tana gamawa kuwa ta nufi dakin Hajiya Babbah.

Tana shiga ta sameta kwance kan carpet wani me laushi ana mata tausa.

Zama tayi gefanta, yayin da taba masu mata tausar inkiya dasu fita.

Ba musu suka mike suka fita daga cikin dakin.

Zama tayi tare da gaida tah,

Amsawa tayi tana daga kishingidan tare da fadin,

_"Jiya hala bacci kikayi da huri? "_
   Hajiya ta tambayi Maryam.

Murmushi ta danyi tare da fadin,
_"Aa wallahi nadan fita na xagaya gidan nan"_

Shiru Hajiya tayi bata mata magana bah.

_"Hajiya nikuwa ina san na miki wata tambaya"_

Batare data kalle tabah tace da ita,
_"Ina jinki"_

_"Wacece wata farar mata doguwa haka, part dinta yana daga can wajan gate"_

Da sauri ta mike zaune tare da fadin,
_"Menene hadinki da ita?"_

Binta tayi da kallo tare da fadin
_"Babu komai ganinta de nayi, tana ta faman jan aji da iyaye kamar wata shegiya"_

Murmushi Hajiya tayi jin Maryam ta fadi haka sannan ta kara da fadin,
_"Shegiyar ce mana, itace Amaryar Memartaba"_

Murmushi Maryam tayi, sannan tace da Hajiyar,

_"Amma ya naga bakwa wata ma'alama da sauran matan sarkinne"_

_"Baki da hankaline, menene hadina da su, ai tsakanina dasu saide asiri"_
Hajiya ta fada tana kallan Maryam din.

Murmushi ta yi tare da fadin,
_"Lallai Hajiya, to aini a ganina koda kinyi asirin a banza tunda suma sunayi, ai in kana san ka yima mutun mugunta ka shiga jikinsa sosai kasan komai nasa tukun, in kayi haka toh daga baya dukkan abunda zakayi masa sai kayi masa, amma ku yanzu baku san cikin junan ku ba, bakusan yaya ko wacce take bah, bakisan ta yaya zaki kullah mata makarcibah, bakiji hausawa na cewa Makashinka yana gindin ka, ai wallahi in gaya miki, ki shiga cikin su ki san ko wacce me take kuma yaya take"_

Shiru Hajiya tayi tana kallan Maryam, kafin tace,
_"Gaskiya kika fada amma ta yaya hakan bayan ko wacce bata neman kowacce, yanzu in naje garesu bakya ganin zasuyi tunanin wani abun? "_

_"Haba Hajiya, yanzu ni me nake, kawai kibar komai a hannuna kina daga nan saide kiji komai daga gareni"_

Cike da fara'a Hajiya ta kalli Maryam din tare da fadin,
_"Gaskiyane, haka nake san mutun wanda yasan abunda yake, naji dadin wannan zuwan naki na tabbabata ta sanadiyarki saina cika dukkan burina"_

_"Insha Allah kuwa Hajiya"_

Nan suka tafa kamar sa'ar tah.

________
Anty Amarya kuwa farin ciki kamar ya kasheta domin ta ruga da ta gama abunda yake damunta, babu abunda take jira sai ganin saka makon aikinta.

Cike da farin ciki ta koma part dinta dan ita a tunaninta babu wanda ya ganta.

Da safe kuwa wanka tayi, tayi shiga cikin farin material yayi mata kyau matuka, tayi girki kala kala domin ta gayyaci Dizhwar yayi breakfast.

Bayan ta gama shirin ta, ta dauki wayarta ta shiga kiransa.

Saida ya jima be dauka ba tukun daga karshe ya daga.

Salama tayi masa danshi daga farko bema gane dawa yake wayar bah.

_"Dizhwar, kazo part dina kayi breakfast nasan baka ci komai bah dan nasan Husna bata nan"_

Jin haka yasa yasan Anty Amarya ce, harga Allah ya tsaneta dan bema san me zaice da ita bah.

_"Kiyi hakuri nayi breakfast "_
Abunda yace da ita kenan,ya kashe wayar sa.

Wani takaicine ya kamata dan bata san ta kirasa yayi mata haka.

Tana zaune cikin falonta rike da wayar ta tana me jin haushin abunda tayi masan.

Da Sallama taji an shigo falon  nata.

Jin bakuwar sallama yasa ta daga kanta tare da kallan me shigowar.

Riga da wandone a jikinta sai Karamin mayafi data yafa a saman kanta.

Binta kawai Anty Amarya tayi da kallo dan bata san ko wacece bah.

Zama tayi kan kujera tare da kallan tah,
_"Ina kwana"_
ta fada tana kallan Anty Amarya.

_"Lafiya lau"_
Itama ta fada dan bata san sanda hakan ya fito bah.

_"Nasan baki gane ni abah, bakuwa ce ni acikin gidan naku, Bakuwar Hajiya Khadijah"_

Jin haka Anty Amarya yasa ta saki fuskarta amma tayi mamakin hakan.
Hajiya Babban ce tace tazo ko kuma batasan yanda ake zaman gidan ba ta shigo, amma kana ganinta kaga wayayyiya.
  abunda Anty Amarya ta saka kenan.

_"Anzo lafiya? "_
Anty Amarya ta fada tana kallan ta.

_"Lafiya qlau, ya muka sameku?"_
  Itama Maryam din ta fada.

_"Duk Lafiya lau"_
Anty Amarya itama kallanta take dan gani take kamar wani abun aka turota tayi mata dan taga yarinyar idanta a bude yake, tamkar na Husna.

Shiru babu wanda ya kuma yima wani magana, can Anty Amarya ta kalleta tare da fadin,
_"Bara nasa a kawo miki fruits"_

Cikin Murmushi  ta furta,
_"Aa bana sha, a koshe nake"_

Tun daga nan babu me magana, hakan yasa Maryam ta zame ta kwanta kan kujera ta fara chat dinta.

Abunda ya bama Anty Amarya mamaki kenan,sai faman satar kallanta take.

Ahankali ta tashi ta nufi cikin bedroom dinta,

Binta da kallo Maryam tayi ta gefe, ganin ta shiga daki yasa tayi saurin tashi zaune, ta fara dube dube acikin dakin nata.

Tanayi tana kallan kofar dakin dan kar taje ta fito, koda taji kamar motsin mutun zai fito tayi saurin komawa ta zauna..





*ZEENASEER*

LAILAH-DIZHWAR Où les histoires vivent. Découvrez maintenant