chapter 2

1.4K 65 0
                                    

Washe Gari da safe bayan tayi wanka ta dauko Jakarta da takardun ta zata tafi lectures,falour ta fito nan ta hadu da yayanta,yaya Dan Allah ka sauke ni school pls yace muje toh,kinci sa'a na dawo daukar document din Dana manta da sai dai ki hau taxi,ai kuwa dai,jirginsu ummah har ya tashi,ayya zanyi missing din ummah wallahi,uhmmmm gobe zanyi tafiya,xanje Cyprus so zaki gidan momy kafin ummah ta dawo kinji,tab gidansu thunderstorm lallai akwai aiki,kinsan dai bazan barki ke daya agidan nan Ba ko bayan babu kowa so sai kiyi choosing between gidan momy da inna rabi,tab gwanda gidan momy so thousands da gida inna RABI ai bazata barni nah sake ba zata takura min neh kawai,but YAYA kwana nawa zakayi one week kawai fah zanyi tab kawai kace, lallai ma,ummah two weeks Abba one month kai kuma one week,su yaya al-ameen da Ameena da sista fatima kuma sai sun gama masters ni wlh na gaji da zama waje daya gwanda na gama Nima na fara ziyara dangi,dariya yayi yace naanaa kenan badai surutu Ba.
Yaya naji sai anjima,buda kofar tayi sannan ta fita ta leko ta window tace mai love u sweet broda bye bye,murmushi yayi sannan yayi mata waving ya ja mota ya fita daga makarantar.

Daga nesa ta hango Aisha da wasu Frdn dinsu awajan suna zauna a normal venue dinsu,tafiya take cike da takama kamar bazata taka kasa ba kai kace yar sarki ce ko shugaban kasa,saboda kasaitanta khadija CE ta taso tana cewa namsey ai na zata bazaki xo Ba wallahi nayi missing dinki two days din nan da baki zo lectures Ba,dariya naanaa tayi tace Nima haka bestie.waje ta samu ta zauna sannan tace Taita kinsan mene wallahi brox zai je Cyprus so zan dawo gidan momyna kafin ya dawo,wani irin ihu aisha tayi sannan tayi hugging dinta kice chilling tinx bari kawai,Allah yasa kar thunderstorm ya bata mana show,shi daya ke part dinshi ina shi ina samana eyex,yauwa gwanda,haka suka rinka fira suna raha atsakaninsu suna dariya har lecturer su ya zo suka shiga lectures. Bayansun gama lectures dinsu for the day neh suka tsaya bakin gate din A.B.U domin shiga adaidaita,kawai sai ga wani mota yayi parking agabansu,motar baka ce mai tinted glass,murtuke fuska naanaa tayi domin ta tsana mota ya rinka tsayawa wai zai dauke su lift abin na bakanta mata rai.tsaki tayi ta matsa daga wajan ta tsayar da mai adaidaita ta shiga tayi gama ko kula su Aisha bata yi Ba domin ta ga suna tsaye suna magana Dana cikin motar harda dariya,juyawan da aisha zatayi sai taga babu naanaa da khadija Wanda itama halinsu daya neh dariya tayi tace ma Fatima da Farida su shiga motar su tafi,Aisha tace kai naanaa rigima,yaya haidar ya kalleta yace daman naanaa neh ta Shiva adaidaita,ita tafi karfin shiga motata knan,dariya aisha tayi sannan tace a'a bata San kai bane domin duk cikin group dinmu wato shiners su biyun nan basa shiga motar samari da sunan lift,yanxu su duk zaton su wani saurayi neh ya tsaya daukanmu sai sa tayi gaba balantana data ganni ina dariya haushi ta kara Ji.


SU WAYE SHINERS

Leader din wannan group din itace Khadija Ibrahim Halilu wato naanaaa kuma duk acikinsu itace karama saboda kokarinta a primary school a pry three ta shiga js1 kuma tayi wace ss2 yanxu haka tana 300 level are jamiar Ahamdu bello university Zaria idan take karanta industrial chemistry,shekarunta yanxu baza suwuce 18 ba kyakyawace ta karshe,batada haske ita wankan tarwadace tanada hanci da baki dan madaidaici da manyan idanuwa wato sexy eyex tana da Dan tsayi sannan ga uban shape sai sa Bata fiya sa gyale Ba idan zata makaranta saboda kallo amma duk ranan da take jinyin rashin mutunci ranan take yafa gyale,sai sa duk Wanda ya ganta da gyale toh baya shiga harkanta donmin ya San cewa sai yayi Dana Sani amma duk da haka mutane na sonta suna girmamata donmin bata Ba maza fuska barta dai da shekiyancinta,amma fa akwai Dan banza masifa ga tsoro sannan bata da zuciya,sun biyar Allah ya azurta was iyayenta itace auta uku mata biyu maza mubaraq ne babba sai alameen da ameena su yan biyu ne sai Fatima sanna khadija wato naanaa sunan kakarta taci ta wajan babanta su asalin yan bauchi ne zamane ya Kawo su Kaduna Zaria mah donmin mamarta likitace tana aiki a teaching hospital Zaria babanta kuma business man neh sai sa bai fiya zama ba,mubaraq kuma pilot neh su al-ameen kuma medicine suka karanta gynecologist said Fatima tana karantan mass communication dukkansu akasar waje sukayi karatu naanaa neh kawai bata son fita waje sai take karatu a naija,sai Aisha habibu halilu cousin Sista din naanaa neh babanta Da baban naanaa uwa daya uba dayane su hudu aka Haifa haidar ne baban sai faisal sai aisha kafin umar da Abdulkaereem suma twin ne.kakansu naanaa yaransa shida ne da Alhaji ibrahim sai inna rabi sai habibu sai umar sannan Hassana da hussaini.Fatima da Farida twins neh suma cousin dinsu Aishace babansu ne umar kuma duk acikinsu babu talaka kowa na da kudinsa iya gwargwado amma dady wato Alhaji habibu duk yafisu kudi,sai khadija Abduljalil hamza bestie naanaa wanda suka fara js1 tare anan suka hadu da juna,tun daga nan jininsu ya hadu kullum suna manne da juna har yanxu da suke jami'a idan itama khadija industrial chemistry take karantawa sauran ukun kuma nursing suke yi,sunan shiners ya kafu ne watarana lokacin suna first year a makaranta lokacin za'ayi matriculation toh shine suka saka wani gown dukkan su iri daya kala daya,purple gown neh mai pink flower yana da dogon hannu suka yi rolling pink veil ajikin gown din an rubuta shiners kuma yana kyali sai kowa ya juyo yana kallansu san da suka shigo wajan taron donmin sunyi matukar kyau sosai,mutane dayawa suka hada baki wajan cewa wow! SHINERS toh tun daga ranan ake kiran su either aisha shiner,Farida shiner,naanaa shiner ko deeja ko fatima shiner,kuma dukkan su sun bama Nana 4yrs interval domin dukkansu are 22 yanxu amma idan ka gansu zaka zata they are her mate.wannan kenan

CIGABAN LABARIN

Murmushi yayi amma baice komai Ba Farida ne tace yaya wai ni yaushe yaya Faisal zai dawo neh,ba ya gama masters dinshi Ba ko,eh fari ya gama amma yana wasu abubuwan ne amma cikin satin nan zai dawo amma babu Wanda ya Sani sai ni domin surprise yake son yin mah momy,ai akwai bidiri don wlh yana dawowa zan diro a bude jaka dani kafin ya zube ma naanaa duka tsaraban domin nasan shi da wannan naanaa five and six neh nai raba su sai ya shirya,fatima tace aikuwa dama suyi aure kawai donmin shakuwarsu yayi yawa,hada rai haidar yayi jin an fadi haka,duk yaji ranshi ya jagule amma bai San dalili Ba,Aisha tana ahankalce dashi domin tun jiya daya ga naanaa ta lura ya fada tarkon sonta Wanda shi kanshi bai Sani Ba,aranta tace akwai show knan,lokacin an sauke su fati agida sunyi kwanar layinsu sai Aisha tace yaya kansan meye yace a'a, naanaa zata zo gidanmu tayi 1wk kafin ya mubaraq ya dawo daga Cyprus,murmushi ya saki Wanda bai ma San yayi Ba ta kalle shi tace lallai kam da sauranka,kuma kasan sunan da ta saka maka,yace wani suna kuma dariya tayi sannan tace thunderstorm dariya mai sauti lallai ta raina ni zata gane ai,azuciyata nace zaku gane dai.daidai nan yayi parking suka buda kofa suka fito suka jero suna tafiya suna labari irnta yan uwan nan,dining suka yada zango Aisha na cewa am really famished, cooler ta fara bude wa tare da zuba abinci,momy neh ta sauko domin daji karar motar haidar,cewa tayi mayunwata duk kun ki aure sai cinye min abincin gida kuke yi,dariya Aisha tayi sannan tace yaya yaki ya bude mana fili domin so nake muyi rawar shoki da bela abikin shi amma yaki amma ai zamuyi abikin yaya nura tunda bikinshi saura two weeks neh,momy ankon mu daban mu shiners sai sa va mai gani sai ranan,ace the whole khadija zatayi aure ai dole muyi abin zo a gani,gaskiya kam barin ma naanaa Wanda bestie ta ne zatayi

KANA SONAWhere stories live. Discover now