MATAR SADAM
BY YOUNG WRITER
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
Da sunan Allah Mai rahma Mai jinkai .
*** *** ***
TARABA STATE GEMBU
Duk Wanda yasan gembu yasan kauye ne mai tarin niima most especially lokacin damina ko ina Ka kalla ciyayi ne sunyi shar dasu gwanin shaawa.
wata yarinya na hango da baza ta wuce 13-14 years ba tafiya take tana Wasa da duwatsu a hannunta sanye take da doguwar riga ta atamfa kafarta sanye da takalmi wanda dashi da babu duk daya domin kuwa duk kasa da chabi irin na ruwan damuna ya bata kafar kanta ba ko dankwali sai gashin ta irin na Fulanin asali da jelar ta sauka har bayan ta, duba nakai ga fuskarta fara ce sosai dan har veins dinta ana gani green dasu a both gefen skull da cheek dinta ga sajen daya zagaye fuskarta tun daga goshin ta har gefen kunnuwan ta ya kwanta luf ² kamar gashin jarirai , doguwar fuskarta mai dauke da dara daran idanuwa wadda gashin idonta masu kama dana wadda ta shafa mascara suka kawata, ga cute pointed noes dinta da shi ba dogo ba shiba gajere ba, dole idan Ka kalleta Ka Kara juyowa saboda baiwar kyau da Allah ya mata .
Wata yarinya da baza su wuce sa anni ba a shekaru na hango ta shawo kwana da dan gudu tana kwalawa wancan din Kira da " seenah! seenah! ki tsayani mana juyowa nayi ga wadda naji ana Kira da seenah tsayawa tayi da tafiya har saida wadda ke tsayar da itan ta karaso.
" cikin masifa ta fara magana wai ke yiha maisa kika iya aikin cin kai ne ki duba tun daga Inda kike kwalamin Kiya shin tashi sama zanyi ne ko mai ?
wadda aka Kira da yiha ce tace dalla can ke kinsan tun yaushe nake bilayin neman ki har gidanku naje hajjo tace bakya nan ni na dauka ma kina islamiyya dukda banyi niyyar zuwa ba saboda ban iya Inda ya biya mana jiya ba kin sanshi yanzu sai ya kama mutum ya nada masa na jaki amma dai haka saboda ke na shirya naje ina zuwa ajinku nan ma akace min baki zo ba shine fa nima na silalo na gudo a Kan kwanar nan na hadu da asiya take cemin yanzu taga kinyo tanan.
Kin gama bayanan naki zubaida ? Seenan ta tambaya, ganin rihar ta tsaya kallon ta ya sata jan guntun tsaki ta fara tafiya tana fadin " Allah ya kawo sauki dai, ace mutum idan ya faya magana ko jan numfashi ba yayi.
Binta riha tayi tana tambayar " wai mai yasa yau bakije islamiyya ba ?
"Tou Banyi haddar ba ta fada a takaice tana kara hadai girar sama data kasa.
" toh meysa ke da wani lokacin ma kafin ma azo wurin kin iya riha ta sake tambaya
"Tambaya kike ko neman sani ?
"duk Wanda ya Miki itama ta bata amsa. Shuru tayi ba tare data Kara cewa komai ba hakan yasa itama riha taja bakinta ta tsuke suka cigaba da tafiya can kuma ta sake cewa wai dan Allah ina kika je nai ta neman ki duk na kusan hada garin nan da yawon neman ki .
" nikam wai meye kike nema na sai kace na ci Miki bashi to naje bayan garine sai akayi yaya kuma" ?
" ba abinda akayi Allah ya baki hakuri ta fada ganin yadda seenah ta dau da zafi cikin jin haushin hakurin da riha ta bata tace da hakurin ya mutu sadakar nawa kika bada
dariya tayi da fadin goma wai waya bata maki rai ne kike ta faman kumbure ² kamar fanken da yaji yeast .
Saida ta sake jan tsaki sannan tace ni da wancan dan iskan ne gaja gara tsabar rainin wayo har ni mati zai tare a hanya ya hanani wucewa saboda shirme wai soyayya , ni wai mai sa wasu mutanen basu san mutunci ba kawai dan yaga ana sake masa fuska shine ya samu right da zai tare ni a hanya yana gayamin shirmen banza kinsan yadda ya kular dani kuwa Amma zan nuna masa wace seenah jikar hajjo.
YOU ARE READING
MATAR SADAM
General Fictionlittafin matar sadam littafi ne da ke kunshe da abubuwa da dama kama daga Kan ribar biyayya wa iyaye, zamantakewar aure, makirci, soyayya, kishi, zagon kasa D.D.S Ku dai kawai Ku biyo alqalamin young writer Dan ganin yadda zata Kaya TSOKACI Baya tay...
