page 3

137 8 0
                                    

*THIS NOVEL IS DEDICATED TO BARRISTER BILKISU GARBA*

*GABA KURAA*

     *NA SADNAF*


*Page 3*

Kasa mik'ewa nayi tsaye saboda tsananin tsoron daya rufeni dan har fitsari na saki Ina daga kwancen

Haskeni wani yayi da cocilan Yana "Kaga yarinya fa Ina ganin lokacin data shigo kaga iirn yarinya da Madu yake San lalatawa ke tashi mana"

Ya daka min tsawa

Amma sai na kasa tashi dan jikina wani irin rawa yake

Ihuun madu kawai ke tashi dan waje suka yi dashi suka yi ta duka

Wanda ya haskeni da cocilan ya matso kusa dani shi da wani Yana "Ni dai ko Yama yi wa yarinya nan wani Abu ne naga ta kasa tashi

"Aaa ba abinda ya Mata gaskiya dan tana shigowa na ganta na fada muku kaga Yar yarinya da ko nono babu a kirjinta tashi mana naga da kafarki kika zo wajensa"

Wanda ya karbe maganar ya daka min tsawan daya sa naji kamar kirjina ya fado kasa.

Na mike zaune Ina k'ok'arin kare fuskata daga haskenin da suka yi"

Ya fusgoni waje yana cewa sauran
"Kaga karamar yarinya data zo wajen Madu ke Mai kika zo nema a wajensa"?

Kamar numfashina zai fita da naga yadda duk suka yo kaina kowa na fadar albarkacin bakinsa.

Madun da nagani kwance shame shame Kansa a fashe yasa naji kamar duniyar na juya min dan gani nake nima haka zasu min.

"Mai kika zo nema a wajen madu daddaren nan"

Wani ya fusgoni da balain k'arfi "Nazo ne ya bani kudi na siya mana abinci yunwa muke ji bamu ci komai ba tun safe"

Nace kamar zan shidde dan har lokacin karkarwa nake

"Ina iyayenki suke Ina ne gidanku"?

"Ai ba wanan tambayar zamu tsaya yi mata ba muje kawai ta Kai mu gidansu dan karka yi mamaki San zuciya ya Fito da mitsitsiyar yarinya nan ba lailai iyayen ta ma sun san ta fito ba"

Har lokacin Mai maganar na rike dani gam  wasu Kuma suna kan Madu wai sai sun Kai shi wajen Yan sanda dan haka yake lalata Yara kanana"

Zubewa nayi a kasa da naga sun dage akan na Kai su gidanmu

Cikin ihuun kuka na fara rokonsu da "Dan Allah karku  fadawa mama abinda nayi kasheni za tayi wallahi abinci ne bamu ci Madu yace nazo zai bani kudi"

"Wanan yarinya fa karya take ban yadda da ita ba kawai mu kaita gidansu idan ma hakane zamu ji a can"

Duk yadda naso rokonsa basu ko saurareni ba haka suka figeni Ina kuka har muka karaso k'ofar gidan su wajen hudu suka bini.

Wanda ya rikeni ya hau buga gidanmu da k'arfi.

Kafin ya sauke hannunsa Ishama ta Bude k'ofar dan idan har na fita haka take zuwa ta tsaya"

Yadda naganta a tsorace tana binsu da Kallo yasa Na fashe da wani sabon kukan.

Inda ta yo kaina da saurinta tana "Siyama Mai ya faru"?

Ke jeki kira mana Babanku"

Wani daga cikinsu yace.

Nidai kuka kawai nake dan  nasan Mai kwaceni a hannun mama yau sai ya shirya.

Ji nake kamar na ciji Wanda ya rikeni na fita da gudu

Koma ina ne gwara na tafi kawai ma na huta

Amma ba zan iya ba saboda Ishama da Hisham

"Dan Allah kuyi hakuri idan laifi ta muku abinci ta fita nemo mana dan Allah"

GABA KURAA Where stories live. Discover now