page 2

88 8 2
                                    

*THIS NOVEL IS DEDICATED TO BARRISTER BILKISU GARBA*

*GABA KURAA*

     *NA SADNAF*


*Page 2*

Siyama

     Matsar da yamin da warin bakinsa ya sani sakin ihuu ya cikani da sauri Yana "Wallahi zan kamaki ne"

Ya kinkimi jarkar ruwan ni Kuma na koma bakin k'ofa da sauri jikina na rawa.

Tsabar mugunta har luma min farce Madu yayi.

"Ihuun me kike yi"?

Naji muryar mama a bayana

"Faduwa nayi Mama"

Wani mugun harara ta watsa min tana "kawai Dan kin fadi shine kike neman fasa mana dodon kunne bani hanya na wuce kafin na ballaki"

Matsawa nayi da sauri ta shige ni Kuma nayi waje da saurina

Hankalina bai kwanta ba sai da naga Madu ya bar gidan duk da uban hararar da yake wulo min.

Har yanzu Ina Jin kamar hannunsa a kasana

Ban taba tunanin Madu ba zai iya taimaka mana ba lura da dadewar da yayi Yana kawo mana ruwa har abinci sallah da zakka haka idan Abba zaiyi kafin yayi wanan tafiyar daya Dade bai dawo ba Madu ake bawa.

Amma wai yanzu dan Ina Neman taimakon Madu, Madu ya kasa taimaka mana.

Hawayen daya zubo min na share na cigaba aikin da mama ta sakani Ina tuna shekaranjiya da yunwa ya kusa halaka  mu.

Dan ko sau dayan ma mama bata bamu komai ba.

Dan tun safe ta fice ita da wata kanwarta da itama bata da aikin daya wuce ta zage mu idan tazo.

Haka zasu yi ta ce nana shegu yayan Arna masu Kashi a Leda.

Zagin nan na matukar yimin ciwo dan har yaran makota idan Abu ya dan hadamu haka zasu ce mana yayan masu Kashi a Leda.

A ranar mun rasa inda zamu samu abincin da zamu ci.

Haka muka yi ta Shan ruwa Hisham baya jure yunwa haka idonsa ya kada yayi jajjur yayi rub da ciki.

Wajen karfe hudu Ishama ta kalleni tana "Siyama Anya ba kasuwa zanje nayi bara ba kila mu samu masu taimaka mana gani nake Koda mama ta dawo ba lailai ta bamu abinci ba"

Nidai tunda na taso nake balain tausayin Ishama dan kafarta daya a shanye yake siririri bai Kai kasa ba hakane yasa Idan za tayi tafiya sai dai ta rike gwiwar kafarta Mai lafiyar ta hau Jan kafar.

Zan iya cewa ba ta inda Allah ya rageta sai ta kafar amma ba laifi Ishama tana da kyau Dan kamanin Abbanmu ta d'auko har hasken.

Ni ce ma nake kama da momi da ba zan iya manta fuskarta ba dan ban Kai Ishama tsayi ba amma ina da dan jiki kamar na momi dan momi idan ba mantawa nayi ba tana da kiba Tafi mama.

Ita kuma Ishama siririya ce.

Hisham kuwa kamaninsa daban kamar dai ya kwaso kamanin momi da na Abba haka yake.

"Mu daure mama ta dawo din mu roketa ta bamu abinci idan bata bamu ba sai na fita na Nemo mana Ishama kinga ba lafiyar kafa gareki ba.

Duk da haka Siyama zan iya fita na nemo mana mutane ma sai sun fi taimaka min idan suka ga kafar tawa.

Girgiza mata Kai na Kara Yi Ina "karki damu Ishama in Sha Allah Idan mama ta dawo zata bamu tunda bata bamu abinci ba har ta fita

Da haka duk Muka rike cikinmu

GABA KURAA Where stories live. Discover now