ƊANƊANO

10 2 0
                                    


          *ƊANƊANO*




______________"Sameera kenan!, Ban san me ya sa kwakwalwar ki ta bijiro da wannan bahagon tunanin a kai na ba".

"*Aure!!!"*.

Ta faɗa da wani irin tone da yasa Sameera kara tsira mata ido, cikin wani irin yanayi ta cigaba da cewa

"Wannan kalma ce ko in ce lamari ne da baze taɓa faruwa ba a rayuwar Jannah, da aure da kuma rayuwar Jannah kamar gabas ne da yamma kin ga kuwa ba ta inda gabas da yamma suka taba haɗuwa kuma ba zasu taɓa ba har tashin ƙiyama".

A hankali ta juya ta cigaba da shirin da take yi bayan ta kawo nan a zancen ta yayinda ta bar Sameera cikin tunani yayinda take ƙoƙarin fasa kalaman Jannar cikin kanta tana fahimtar su ɗaya bayan ɗaya.

Sunkuyawa tayi tana ɗaure igiyoyin takalmin da ya kasance baki me tsini sosai kana ta cigaba da cewa

"Jannah ta buɗe ido ne ta tsinci kanta cikin wata irin rayuwar da ke kin sa wacce ce ba se na miki bayani ba, irin rayuwar da kowace mace take neman tsari da ita, uwa ke duƙufa wajen bawa ƴaƴan ta kariya da katanga daga gare ta ta hanyar basu kyakkyawar tarbiyya, iyaye maza ke sa ido tare da addu'a cikin sallar su kan Allah ya tsari zuri'ar su daga irin ta, yayye maza ke tsayin daka wajen kiyaye ƙannen su daga afka mata, al'umma ke gudu da kwashewa wanda ya jefa kan sa cikin ta, se gashi....se gashi..".

Dakatawa tayi daga maganar ta ɗago tare da zuba idanun ta cikin idon Sameera da ta bada dukkan hankalin ta kan ta

"Ni *UWA* tace ta sani a harkar dumu dumu, *MAHAIFIYA TA* da hannun ta ta ta kawo ni a sani a harkar *KARUWANCI*, ita dai da kika ji ina kira da UMMA itace ta bani dukkan wani license din zama *GAWURTACCIYAR KARUWA*, training na karba har na tsawon shekaru goma duk akan *KARUWANCI.....!*

Hannun ta biyu ta haɗa ta jimƙe cikin juna idanun ta na kaɗawa daga fari tas me ɗan maiƙo zuwa jajajaja na ɓacin rai da ƙunar zuciya, murya ƙasa ƙasa me ɗauke da takaici ta ɗora da

"So da yawa takan ɗora masa dukkan laifi wanda a da nima na yarda da hakan tun da ya kasa kulawa da ni ya gudu ya bar ni bayan ya samar da wanzuwa ta, sedai daga baya na fahimci itama me son kan ta ce, duniya kaɗai take kalla haka kuma makomar rayuwa ta bata ɗaɗata da ƙasa ba tun da har zata iya jefa neman ni cikin wannan sana'ar, sedai  ya zuwa yanzu duk wannan baya gaba na, abinda na sani shine..".

Wata bazawarar dariya tayi wadda bata ɗauke da komai face alwashi ziryan

".....kome take so ta tara ta samu, matsalar ɗaya ce da ban taɓa sha'awar *KARUWANCI* ba, ina ƙyamar dukkan wata ƙazanta se gashi kuma zina ita ce mafi ƙololuwar *ƘAZANTA*, Sameera kin san na tsani mazinaci , wannan shine kaɗai abinda ya taka min burki da Kasancewa sananniyar karuwa a duniya, amma kuma da hakan ba ta samu ba se na zaɓi abinda nake ganin ze fisshe ni.....".

Matsawa tayi dab da Sameera har suna jin hucin numfashi juna kafin ta datse haƙoran ta waje ɗaya ta furta kalmomin cikin wani sauti me ratsa zuciya

".....*SATA da DAMFARA!!"*.

Ta bayan Sameera ta miƙa hannu ta ɗauki karamar pistol ɗin ta da ta ake kan mirror ta soka a ƙasan rigar ta jikin ɗamammen wandon ta kana ta ja baya kaɗan tana ƙara gyara zaman rigar ta.

Cikin takunta ta juya ta nufi ƙofar fita daga ɗakin, seda ta kama ƙofar ta buɗe sannan ta juyo ta dubi Sameera da har lokacin take tsaye tana kallon ta batare da ta motsa ba

"Na fita operation, ki kula".

Da haka ta fice bayan ta sakar wa Sameera kyakkyawan murmushin ta tare da rufe ƙofar...............!!!!










Ya kuka ji wannan salon?, Na tabbata ya ratsa ku ko, Well, zan iya cewa baku taɓa jin irin wanann salon ba domin na tabbata shi ɗin na daban ne kamar yadda alƙalami na ma ya fita Zakka.

Salan wanna labarin ya banbanta da na kowa har kuwa da ma labaru na na baya, wannan yazo da sabon tsari da zubin da bana rantsar ze kayatar da ku ya kuma nishadantar tare da fadakar da ku a lokaci ɗaya.

Kamar dai yadda kuka sani, wannan labari ze zo muku ne daga alkalami na *NI OUUMMEY* marubuciyar littafin*RASHIN HAIHUWA*, wanda duk kuwa ya karanta littafin rashin haihuwa base na fada masa wace Ni ba ko ya zubin tafiyar alkalami na yake dan se dai ya bada labari............…..…..................................................dan haka nake cewa ku taho muyi tafiyar nan tare baki daya ta yadda zamu nishadantu mu kuma faankantu tare baki daya......!!

Sedai fa littafin nan is not free, PAID BOOK ne @₦500 only!.

Ga masu bukatar ƙarin bayani zasu iya tuntubar wannan number 👇
09013101854

Wadanda kuma zasu yi payment zasu biya ta wannan account number 👇

9013101854
Rabiatu Abdullahi
Opay.

Se a tura shedar biya zuwa ga wannan number 👇

09013101854

Kar dai ku manta, wannan littafi ze fara zuwa muku ne a ranar 20th April 2024 insha Allah.

Kar ku sake a yi wannan tafiyar ba ku, duk wadda ta bari aka yi ba iya kuwa zata yi missing ba kadan ba.

Ouummey ✍️.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Apr 24 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ƳAR DAMFARA Where stories live. Discover now