Wajen dinning ta nufa, Food flasks din abinci ne a jere akan dinning table din.. Gefe daya da kayan tea da kofuna da plates, komai dai a killace an ajiye dukkanin abunda zaa bukata.

Kujera taja ta zauna. Ta dau plate ta zuba komai dai dai cikin ta. Ta hada tea mai kauri tana ci tana korawa da shayin.

Ahsan ya fito daga cikin dakin sa shima sanye cikin wani yadi kalar zaiba.. Bai sa hula ba. Kanannadadden gashin sa na fulanin usuli ya kwanta luf.

Tana daga zaune akan dinning ta jiyo kamshin tiraren daya sata saurin waigawa suka hada idanu tayi azamar janye idanun ta da sauri..

Ahsan ya tabe baki ya nufi wajen fridge ya bude... Shi kansa bai masan me yake nema ba. Amman tabbas zuwan nasa wurin firjin na da nasaba da kyawun da Marwaa tayi masa.

"Barka da safiya...." Ta fada kasan makoshi. Tunowa da hudubar da su anty kulu suka mata.

Ahsan yayi murmushi a sunkuyen dama yake.daya daga Kuma ya hade rai Yana sake tamke fuska.

"Lafiya" ya amsa a hasale..

Itama tabe bakin tayi ta mike tashige cikin daki. Tana barin wajen, Ahsan ya nufi dinning din. ya samu kansa da zama akan kujerar data tashi. Ni'imantaccen kamshin tiraren khumran dufra na kamfanin tiraren wutan yerwa incense and more ya gauraue ilahirin wajen da gewaye

Ahsan ya sake baje kofifin hancin sa yana shakar kamshin. Ya janyo plates ya debi komi . Kasa cin komai yayi. Kujerar dake duban tasa ce ke masa gizon Safaa.

Allah sarki da tana raye yanzun da ta kujerar ta matsar da ita daf da tasa. Zata zuba komai a plate ta dinga bashi har ya koshi tana wani ririta shi tamkar dan karamin yaro..

Hawayen da yake ta matsesu ne Suka bijere Masa suka zubo... Yayi saurin saka hannun sa ya gogesu,

"Allah ya Miki rahama Safaa. Allah yasa aljanna ce makoma agare ki... Ina kewar ki sosai." Ya shigaa fada cikin rauni.

Dakyar ya caccakuni abincin ya mike ya hada kayan daya bata ya Kai kitchen..

Har yayi hanyar fita sai Kuma ya koma ya kwankwasa dakin da Marwaa take .

Alokacin Kuma tana zaune akan gado. ta mikeda sauri dankwalin Taya zume ya Fadi batama lura ba tayi hanyar kofar ta bude.

Tsayawa yayi Yana duban ta. Musamman gashin kanta daya Sha Kananun kitso sai kyallin Mai yake. Ga jelar gashin hargadon baya.

Binta yay da kallo tundaga sama har kasa. Tayi Masa kyau ba kadan ba.

"Ina sauraron ka..." Ta fada tana juyar dakai. Anan ta hango dankwalin ta a gaban gado. Da sauri tadakko ta daura. Tazabga Masa harara kuma kamar shi ya cire mata dan kwalin

Tsiwar ta dariya take bashi ma. Dik da ya lura Kamar tayi laushi bayan rasuwar Safaa. Sanda take kawo baby Safaa wajen hajian su da idan suma sunje gidan su...

Da sauri ya kauda kansa.. hannun sa na shafo keyar sa yace,

"Akwai abunda kike bukata? Zan fita"

"Babu komai"

"Alright then" Ya fada Yana daga kafadar sa.

Ficewa yayi daga cikin gidan. Ta sauke ajiyar zuciya tana gyara zaman dankwakin ta. Ya kalle mata gashi. Sam bataji Dadi ba.

Da Rana ma haka aka shako food flask dauke da abinci. Marwaa ta zuba taci. Ta mike ta sake kakkauda abubuwa ta koma tazauna tayi jingum...

Yar wayarta ta zaro ta danno lambar ummy. Bugu biyu ummyn ta dauka Sika gaysa,

"Ya baby Safaa?"

"Tana Nan kalau gata tanata bacci"..

"Yauwa alhamdulillah"

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now