"Eh an daura miki aure... Ba mu isa mu aurar da ke bane ko ya ya?"

"Ba haka nake nufi ba kawu. Kawai zancen ne ya daure mun kai. Saboda ko zuwan Faysal na karshe ba muyi maganar ba." Idanun ta sun cika taf da hawaye. Muryar ta sai rawa take yi.

Kawujo yayi shiru bai ce komai ba har ta karasa. Domin daman abunda ya shigo da shi gidan kenan domin yayi musu nasiha dukkanin su. Ya kuma tausashi Marwaa abisa daurin auren ta da akayi bata da masaniya.

"Ina sauran mutanen gidan baki daya? A shimfida tabarma kowa ya zauna. Zamuyi magana."

Malama zuwaira na kofar dakin ta tana zaune akan wata kujerar karfe karama. Ta goye baby Safaa a bayanta tanata bacci.

Hamdiyya ta shimfida tabarmar duk suka zazzauna akai. Kawujo yayi gyaran murya. Ya fara addu'ar bude taro. Bayan ya kammala ya basu hakuri sosai abisa halin ko in kula da mai gidan su malam Muhammad yake yi tamkar ba mata da 'ya'yan sa na sunnah ba. Sam baya basu hakkokin su. Kowa rayuwar sa yake tamkar gidan haya. Ya tabbatar musu da cewa komai yazo karshe yanzu. An yankawa malam Muhammad wani sashe na gona dake kauyen su zai je yayi noman rani ya fara sayar da su. Abunda aka samu zai dinga daukar dawainiyar gidan baki daya. Sabuwar rayuwa kenan.

Ya nuna zulfa'u da yatsa bayan ya karasa. Itama ya shigaa yi mata nasiha da jan kunne hadi da hakan ya zama izinah ga sauran kannen ta masu tahowa. Ya kuma alakanta gurbatar rayuwar zulfa'u ta samo asali ne ga rashin halin ko in kula da mahaifin nasu yake. Sun zama tamkar akuyar sake. Sam ba jan kunne ko kulawa irin wadda uba ke bawa 'ya'yan sa musamman 'ya'ya mata na tarbiyyah..

"Kin ce kin tsayar da Abbas a matsayin wanda Zaki aura ko?" Ya fada Yana nuni da zulfa'u

Ta gyada kai tana cewa,

"Eh kawu.."

"Toh Alhamdulillahi... Zan samu malam inuwa (mahaifin Abbas) don ayi auren awuce wajen kawai. Ina fatan hakan zai zamar miki izinah ko ince wani babban darasi na rayuwa. Ki ma godewa Allah da Abbas din bai guje ki ba. Don lalle ya cika dan halas mai yin soyayyar gaskia. Idan wani ne duba da tarin rashin kirkin da akace kina Masa. Da tuni bazai Kara waiwayn ki ba. Ina muku fatan alkhairi Allah kuma yasa da anyi anyi kenan..."

"Aameen kawu.." suka amsa baki daya.

Kawujo ya sake gyaran murya Yana muskuta zaman da yayi yace,

"Marwaa.... Faysal mai neman ki a baya yanzun Allah ya rubuta Aysha dai wannan makociyar ku ita zai aura amadadin ki..."

Marwaa ta Mike dasauri tana dafe kirji. Kanta ya mata nauyi kamar zai rabu da jikin ta ya dawo kasa. Saboda tsananin tashin hankalin data shiga. Jiki da murya na mata rawa. Saboda kwakwalwarta harta fara hasaso mata abunda take tunani. Cikin firgici tace,

"Kawu bangane ba? To wa aka aura mun? Kawu Faysal shine saurayi na fa. Wanda Zan aura. Kawu idan kuskure akai awarware auren na su mana.. "

"Babu wani kuskure duk da sanin mu akayi. Hasalima ga mahaifiyar ki nan tananan akayi komai aka gama. Itace ma ta bawa Faysal ko ince tayi masa tayin auren Aishan. Amman sai bayan da aka gama yanke zancen faysal yahakura ya barwa shi...

"Shi wa kawu? Ummy har da ke a Wanda suke boye mun? Ummy auren dole zaku min?"

Hawaye ne ya balle mata ta shigaa rera kuka ta karasa gaban kawu tayi gurfane kaman mai neman gafara. Hawaye Shabe shabe tace,

"Kawu dan girman Allah a raba auren nasu da akayi. Wallahi Faysal shine wanda muke soyayya kawu ku mun kowane hukunci amman dan Allah banda na rashin auren Faysal. Kawu dan Allah..." Ta riko kafafuwa sa. Ruwan hawayen ta na diga Masa a kafafuwan sa.

Kawujo yayi shiru. Tausayin ta ya kamashi kwarai matuka. Hakama ummy da baki daya ji take tamkar ta tauyewa Marwaa hakki. Sun shigaa tsakanin tashin hankukaa.

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Tempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang