Ummy ta gyada kanta alamar a'ah. Tana cigaba da jan carbinn ta. Marwaa ta cigaba da cewa,

"Ga amanar Safaa nan... Dan Allah karki bari tayi rashin uwa..karki bari Safaa ta wulakanta. Marwa ki kula mun da Safaa. Ban amince kowa ya rike mun Safaa ba fache ke Marwaa. Karki bari safaa ta tozarta. Na roke ki da girman Allah karki bari rikon Safaa yaje hannun wasu daban..... Sai nake ce mata menene hakan cuta ai ba mutuwa bace da sauran su. Ta sake nanata mun da, Dan Allah Marwaa ga amanar Safaa nan na bar miki ita har gaban abadan...Tana karasa fada ta fara wani irin tari.. sai na fito na gayawa likitan nan. Wannan shine maganar karshe da mukayi da Safaa ummy.. ummy ba zan iya rayuwa ba safaa ba. Ummy duniya ta mun zafi. Ummy kirjina na mun zugi da wani irin rada'di kamar zai ballo ya fado kasa ummy.. innnalillahi wa Inna ilaihi raji'un"

"Ki dai na kuka Marwaa. Kiyi hakuri. Allah ya jikan Safaa. Inshaa Allahu aljanna ce makoma agare ta. Kamar yadda ummy ta gaya miki...Safaa ta tafi, Safaa tadawo. Ga Safaa nan atare da ke. Sai kiyi kokarin cika alkwarin amanar data baki. Domin duk duniya ke da ummy me kawai zaku iya rike amanar Safaa. Kuma marigayiya Safaa ce ta zaba da ki kula da yar ta. Ke ta haifawa Safaa. Safaa yar ki ce yanzu. Safaa mallakin ki ce yanzu. Kiyi hakuri kowanne dan adam yana da KADDARar sa. KOWA DA IRIN TASA ne kawai. Allah ya bamu ikon cika wannan nauyi da ke kan mu mu dika gaba daya. Safaa ta samu alkhairi na tarin yabo daga bakunan jamaa kowa Yana fadin kyawawan halayen ta. In shaa Allah tata tayi kyau... Ki dai na zubarmata da hawaye." Aysha ta karasa fada tana Mai duban Marwaa dake rike da baby Safaa tana sauraron maganganun Aysha.

"Amin Aysha. Kin gama magana Allah ya saka da alkahiri kinji?"

"Amin ummy... Amin... Safaa amaniyata ce. Wallahi ummy hakuri da dauriya ce kawai muke yi amman baki daya duniyar tayi zafi astagfirullah Allah ya iya Mana"

"Allahumma Aameen.."

Haka dai sukayita maganganun su na tu'ajjabi suna kuma yiwa marigayiya Safaa addu'ar cikawa lafiya  da samun tikitin shiga aljannatul firdaws...

Sai bayan ishai aka sallame su. Da tulin magunguna da allurai. Domin bayan da karin ruwan da aka yi mata na karshe ya gama shiga. Likitan ya sake dubata inda dik tambayar da yayi mata sai kuka tana wasu irin weird acting. Atakaice dai tasamu depression. Ya Kuma dorata akan anti depressants na wata biyu.

Kawu Adamu ya taho da dan sahu. Su uku a baya an rike Safaa. Sai shi kawu Adamun a gefen Dan adaidaitan a haka Sika karasa har gidah.

Duk ba yan zaman makoki an tashi. Daman malama zuwaira tun ranar farko tace dan Allah kada ayi zaman makoki nan don bidi'ah ce kawai kowa yayiwa mamaci addua shikenan. Don yanzun gidan zaman makoki an mayar dashi sansanin gulma, Hira, wasu ma kasuwancin su kawai sike yi. Wata tawuce a na nuni da kasan atanfar ta. Ko a kasafce kudin kayan da ke jikin ka. Don hakan ba kowa sai yan cikin gidan kawai. Sai makota dake shigowa tsilla tsilla, Wanda basa nan akayi rasuwar da sauran su.

Aysha ta taya su suka gyaggyara dakin sannan tayi musu sallama ta tafi gidah.

Nanma marwa ta bude sabon shafin kuka hango kayan sawar safaadake kusada na ta ayar karamar drawer din su. Dakyar ummy ta lallasheta tadai na

Ummy tasake hadawa baby Safaa yar madarta a feeder tabata... Don madara aketa bawa babyn. Kuma Alhamdulillah an samu ta karba Tana sha. Don cikin Yan Kwanakin da aka haifetA ma tini har tayi yar kiba kadan. Gwanin ban sha'awa. Kamar su daya sak da marigayiya Safaa Kai kace kaki tayi ta tofar saboda tsabar kaman tayi yawa.

     °•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•

   Ahsan kuwa sai da ya shafe kwanaki Tara a asibuti yana jinya Kafin a sallame shi. Don da fari ma har an fata cure Rai akansa. Saboda suma ya dingayi yana kakkafewa jikin sa na wani irin kakkarwa.

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now