Hijabin jikin ta ta zare. Wasu shegun kayane aciki riga da wando da sukayi matukar matse mata jiki. Dik halittin jikin ta sun bayyana.

Rayyan ya kasa nutsuwa ya matsa daf da ita ya janyo ta jikinnsa yana yawo da hannunsa a ilahirin jikin ta

"Gaskia ba karya ke din full option ce... Allah yayi halitta subhan:Allah. "

Zulfa'u tayi murmushi tana neman janye jikin ta rayyan ya hanata ta hanyar matse da jikin sa kam ya haura kan gadon da ita..

Nan ya shiga bata zafafan kisses yana touching ko'ina na jikin ta. Zulfa'u na maraba da salon da yake aika mata.. Daman ba sabon abu bane awajen ta domin ya saba taba ko'ina na jikin ta. Kawai dai bai rabata da mutucin ta ba.

A yammacin ranar rayyan yayi nasarar raba zulfa'u da virginity dinta. Ya gamsu iya gamsuwa Zulfa'u kuwa sai kuka take yi. Rayyan ya saka hannunsa yana shafa goshin ta dake tsattsagar gumi a hankali yace,

"Nagode zulfa'u. Yadda Kika shayar dani zumar ki. Wannan shine tabbacin kin amince dani kin yarda dani Kuma Zan baki mamaki ta hanyar auren ki da zanyi. Kedin kinfi matata komai da komai. Bantaba samun Kai na acikin farin cikin wannan yanayi da muke ciki ba. Da ace na san ki tunda fari da ke Zan aura.. Amma auren matata na karba amasayin KADDARA tah domin KOWA DA IRIN TASA... Zulfa babe... Kina jina kuwa?"

Tayi murmushi tana danne lebenta dake mata zugi tace,

"Rayyan yaushe zamuyi aure? Lokaci nata ja. Kaga dai na cika maka alkwarin ka na baka kai na in return Kuma kache zaka aure Ni. To yaushe ne zaka fito ka turo manya muyi aure?"

"Soon babe.. Nan kusa karki damu.. Akwai kayan da nayi ordering daga Germany me. Banso na gaya miki yanzu bama dandai kin matsa ne da surprise zan maki. Kayan lefe ne nasa ahado daga Germany saboda ingancin kayan su. Da sunzo zaa kawo sai kawai ago komai da komai . Gidan da Zan saka ki ma an kusa gamawa saura gyaran dakunan sama da kitchen din sama. Amma kasa an gama.... Zamuje ki zaba furnitures ma sai ayi furnishing gidan according to your taste.. kina ji na kuwa?"

Zulfa'u ta saki tattausan murmushi. Tana mai fasalta yanayin gidan a idanun ta. Cike da madaukakiyar murna tace,

"Ina sauraron ka Rayyan..."

"Za muje ma ki ga gidan idan mun bar nan.. ko bakyaso yau?"

"Ina so mana... Ina so" ta fada da sauri tana dariya.

Nan suka sake lulawa duniyar haramci... zulfa'u ta saki jikinta sosai jin rayyan yana fasalta gidan da zata zauna har da Karin zai Kai ta ta gano plus lefe da ake hada mata a Germany.

Sai da suka samu nutsuwa sosai... Su kayi wankan tsarki da ramakon sallah tukun sannan suka bar hotel din..

Rayyan ya biya da zulfa'u wani katon gidah dake a dex 2 crescent. Ta shiga ta gano komai na gidan tanata murna.

Ya biya ta tukubar nama ya saya mata dakwalan kaji da lemuka da fruits fal. Sannan ya kaita har kofar gidah ya sauketa.

Ta shiga gidah da murna Hamdiyya ta debo sauran ledojin a motar rayyan suka shjga daki suna kuskus. Tana gayawa Adabiyya haduwar gidan da rayyan ke gina matamm. Ta curo bandir din kudin nanma ta irga masu yawa ta bawa addabiyya ta dakko guda daya ta mikawa Hamdiyya. Suka shiga yi mata godiya.

   Tun daga ranar rayyan ya mayar da zulfa'u tamkar matar da yake aure.... Malama zuwaira ta samu Adabiyya da maganar Ina zulfa'u ke yawon fita ne haka sakaka ya kamata ta saka ido duniyar yanzu sai ahankali musamman ga ya mace.  Indai aurenta zeyi ya Kamata ya fito haka ko kawo kudi ne ayi

Adabiya tace babu komai rayyan ai aurenta zaiyi. Yana gini da kuma hado lefe ma a kasar jamus. Jin haka yasa malama zuwaira ta share su ta zuba musu Ido kawai...

Haka rayuwar ta cigaba da garawa... Lokaci nata shudewa..

Soyayya ce mai zafi dake tattare da kauna tacacciya marar gauraye Kuma Mai tsafta ce me wanzuwa tsakanin Safaa da Ahsan da Kuma Marwaa da Faysal. Lamarin sai dai ace mashaa Allahu. Domin tuni Faysal ma ya saka a ankawo kudin auren sa da Marwaa.

   A sussunkuye suke su biyun da bokitai da baaho agaban su suna wanki gefe daya kuma tilin kayan wankin su ne da na mahaifiyar su malama zuwaira...

Zulfa'u ta shigo cikin gidan da sauri tana rusa kuka tamkar wadda akayi mata mutuwa...

"Menene?" Safaa

"Zulfa'u menene?"

Inaa zulfa'u bata bi takan su ba ta shige daki. Adabiyya dake tsaye gaban rijiya ta bi bayanta da sauri tana tambayr ta,

"Zulfa'u menene? Lafiya ? Wani abun ne ya faru?"

Zulfa'u bata amsa ta ba ta sake baje baki ta zunduma uwar Kara Mai sauri tana mai buga kanta a bango..

"Wai dan uban ki ba zaki gayamun menene ba... Wata cutar likitan yace kina da ita ko kuwa?"

Zulfa'u ta Mika mata takardar hannun ta tana sharce hawayenta,

"Menene wannan din?"

Adabiya ta karbi takardar tana jujjuya ta tace,

“Wata cutar aka rubuta kinada ita ne ko ya ya?”

Zulfau ta girgiza kai hawaye d’aya na bin daya… Duk yan gidan sukayi dakin addabiyyaa ciki harda su safaa

Marwa ta karbu takardar a hannun adabiyya tana dubawa. Idanunta ta zaro waje tana bin zulfa'u da kallo tace,

"Ciki wata uku.."

Adabiya ta wafce takardar tana dubawa sai kace ta iya karatu ta kurawa takardar idanu tana rute bakinta da tafin hannu..

"Karya likitan yake. Makirci ne kawai ban yarda ba. Share hawayen ki ki Kira rayyanun yanzu ki sheda masa" adabiya ta mikawa zulfau wayarta Kan ta Kira rayyanun..

Gaba daya suka rude...jikin su yayi sanyi. Zulfa'u ta turawa rayyan sakamakon ta WhatsApp ya karanta yayi shiru.

Sukai ta neman sa a waya da layika daban daban yaki dagawa. Daga baya ma idan an Kira shi wayar sa akashe..

Haka suka dau tsawo lokaci ana neman rayyan gaba daya an kasa samun sa... Gidan daya kaita ana ginawa dayace nasa ne ashe karya yake na wani ba indiye ne bama agarin yake ba... Suka tattara suka hakura, Magana ta karade unguwar su dika Kan zalfau tayi cikin shege da saurayin ta mai daukar ta a mota.

Duk samarinta sun gujeta.. zulfau tasha kukan dana sani. Hakama Adabiyya mahaifiyar ta...

     :::::::::::::

Tafe suke a mota kirar Mercedes Benz.. Glk. Ahsan ne me tuka motar. Yayinda Safaa ke gaba tare da shi. Sai marwa dake baya..

"Kadan Kara gudu Mana" marwa ta fadawa Ahsan tana murguda baki.

Ya dubeta shima ya tabe baki yace,

"Gaskia kina takura Mana.."

"Zaku fara ko? " Cewar Safaa tana murmushi....

"Ai Faysal Yana kokari. Yarinyar nan sai a slow"

"Ko dai Safaa na hakuri da Kai ba. Domin Kai acikin jerin maza ma kana karshe"

"Lalle ma yairngar nan bari kiji Faysal ne ma ya temaka yake kula ki kawai"

"Ai namiji irin ka ko a kafa aka daura mun sai na kunce na wullar"

"Dan Allah ya ishe ku. Haba Kun cika mun kunne" Safaa ta fada.

Ahsan ya juya ya dankarawa marwa harara itama ta mayar Masa. Safaa ta tuntsire da daria sun saba dama ko yaushe sai sunyi cacar baki idan suka hadu... a haka suka karasa wani dankararren super Mart dake dauke da kowane irin Kaya na more rayuwa.

Wurin akwatuna suka nufa............


   ZAFAFA BIYAR UPCOMING PAID NOVELS... #2024 INSHAA ALLAH..

1-AMEENATUH: MAMUH GEE

2-KWANKWASON JIMINA (MAI WUYAR SHAFAWA) : NANA HAFSAT MX

3-GUDUN KADDARA: SAFIYYAH HUGUMA..

4_TSUTSAR NAMA...(ITAMA NAMA CE): BILYN ABDULL..

      

®️MX

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now