"Kila ma ke yake so kanwata"

"Allah ya kiyaye ya rufa asiri ko maza sun kare a duniya bana fatan hulda da irin wancen"

Dan adaidaita sahun ya sake kecewa da dariya yana gyara zaman mudubin side mirror yace,

"Ai kwa wallahi binmu yake a baya. Gaskia ya mato da san wata acikin ku" Yana nuna musu motar saurayin dake biye dasu ta baya ta cikin mudubi,

"Amma wannan ko nacacce to meye dalilin bin namu?"Aisha ta fada

"So yake ya fadi maku zuciyar sa mana to ai ni ya hurgeni da zafi zafi kan daki karfe .  Haka ake son gwarzon namiji" cewar dan adaidaita

Ita dai Safaa dariya ta kyalkyale da ita tace,

"Ko Aisha ko Marwaa wata acikin ku inaga ya kamu da so.."

"Allah ya rufamin asiri da yardar Allah bani bace... In kinji ana hate at first sight to abudna ya faru da ni kenan akansa. Gaba daya bai kwantamun ba... Banà kaunar sa"

Aishaa ta tuntsire da dariya tace,

"Oho dai, Ni dai na tabbatar 'da ya daga cikin ku yake so... Ina cikin ku wa zaice Yana so na? Ke dai Allah ya samu adanshin ku kawai ya dandana mana irin farin jinin ku"

Marwa ta daga hannu ta dada mata dundu a baya. Safaa dai dariya tayi tace,

"Allah ya shirye ki Aisha.."

"Wahalalle ai kuwa bin namu yake... Iska na wahalar da mai kayan kara" Marwaa ta fada ganin motar saurayin tana biye dasu har cikin titin unguwar su..

       Hannun sa daya akan sitiyari yana biye dasu a motar sa... Murmushin fuskar da ya fadada alokacin daya tuno bakinta data bude tana dariya ta shiga cikin adaidaita sahun..

Ya samu kansa da saka dayan hannun sa yashafo kasan keyar sa...  Ya kamu da kaunar yarinyar da yayiwa kallo daya bisa ka'ida...

Tsukukun layi ne, Dakyar motar sa ta shjga ciki Kasancewar tana da girma da Kuma Fadi ba lefi.

Ya hango Dan adaidata sahun daya faka a kofar wani gidah Marar bene dai dai haka na marasa karfi.. ganin sun fito daga cikin adaidaita hakan yasanya shima saurin fitowa daga cikin motar tasa har hular kansa na faduwa a kasa..

"Yanzu Wa zai cika mun kudin acikin ku?" Cewar Dan adaidaita sahun daya dakko tsunma Yana faman goge gogen cikin adaidaitan nasa.

"Ni ce Ina zuwa." Marwa ta shiga bubbude littafin ta ta zaro gudar nera dari data manne da jikin littafin ta tana Mika masa

"Angode Kawas" Aisha ta mata godiya

"Mungode sissy.... "

"Dalla kumin shiru, godiyar meye haka? Nima tun darin da kawu adamu yace na rike chanjin nance fa last week"

Dan adaidaita da shegen tsegumi ya leka ya hango saurayin Yana murmushi yace,

"Gaskia ba dan sauri nake ba dana tsaya naga ya wasan zai Kare.. mutumi na fa dagaske yake."

"Matsalar ku ce Kai da shi din." Marwa ta bashi amsa.

Ta shige cikin gidah da sauri. Aisha ma ta musu sallama ta tafi. Saafa ce ta shige daga karshe bayan dan adaidaita sahun yaja ya tafi.

Shi dai Yana tsaye Yana kallon su har suka shjgye cikin gidah. Ya jingina da motar sa na wasu mintina ya gama tabbatarwa da lalle gidan su ne..

Ya nufi wajen samarin daya ga suna zaune tun dazu a bakin kofar gidan Sina hira da butar shayin buzaye agaban su suna dafa shayi.

Hannu ya basu sukayi musabaha yace ,

"Dan Allah abokai na yar tambaya Zan muku idan Babu damuwa"

"To Allah yasa mun sani" Cewar daya daga cikin samarin.

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now