"Kanwata..."

Saafa ta juyar da fuska tana kallon sa.. saurayin zulfa'u ne sai dashare baki yake yana jujjuya mukullin motar sa,

"Ina wuni?" Tace dashi daga inda take tana dan kasa da Kai,

"Kira mun zulfa babe pls"

Abbas ya murtuke fuska yace

"Sai ka Kara gaba, bacci take..."

Mai motar yayi murjushi yana dartse labban sa yace,

"Kai ake gayawa haka.... Ko karfe nawa zanzo zulfa'u na fitowa tadi waje na."

Saafa ta shige cikin gidan bakinta dauke da sallama.. mahaifiyar su malama zuwaira ta amsa alokacin ta debo ruwa a rijiyar cikin gidan na su, Saafa ta karasa da sauri ta karba...

"Zulfa'u ana sallama dake...."

"Dan anacen Abbas bai tafi ba kenan anfa gaya masa bacci nake"

"Eh shima bai tafi ba. Amman wannan me motar nanne dake zuwa k...

Bata jarasa ba zulfa'u ta mike da sauri jikin ta nabari itada Adabiyya mahaifiyar ta ta.

"Rayyanu ne ko?" Adabiyya ta fada tana murmushi, zanin ta na kokarin faduwa saboda tsabar farin ciki...

"Wai rayyanu... Rayyan ake cewa fa iya.." zulfa'u ta gyara mata tana wani gatsina

"Maza ki shirya ki fita dan ubanki kinbar dan mutane tun dazu yana jira"

Zulfa'u ta shige daki da sauri ta sauya Kaya ta dakko mayafi ta yafa ta shafa hoda da jambaki tanata murmushi ta fita wajen

Abbas baki bude yake duban ta ganin tafito ta wuce shi tamkar batasan da mutum awajen ba don saura kadan ma ta take masà dan yatsa ya janye da sauri,

"Zulfa'u akace bacci kike?" Ya tambayeta muryar sa har tana in Ina

Zulfa'u ta dube shi tana girgiza kai ta karasa wajen rayyan tana nuna Abbas da yatsa tace,

"Dan Allah ka tafi ni ka isheni da naci wallahi. Sai da safe"

Abbas ya Kada kai ya da dubi hannunsa na dama rike da Leda baka dauke da awarar daya sayo mata ta dari. Ya bar wajen da sauri ransa a bacee,

"Wai waye wannan?" Rayyan ya nuna Abbas da yatsa yana kallon zulfa'u

"Rabu dashi wani nacacce ne wallahi dan kasan layin mu"

"Saurayin ki ne kenan"

"Ina da Kai ya zaai na kula wancen?"

"Gaskia ne." Ya fada yana lashe kasan lebe

"To me Zan samu yammata na?"

"Abubuwa da yawa Amma fara siye baki tukunna... " Ta amsa shi tana kanne Ido daya

Rayyan ya zura hannu a aljihu ya debo kudi Yan dari bibiyu na dubu biyar ya dora mats a Kan hannu ya sake janyo bakar Leda a kasan sa ya Mika mata ta karba Tana duba ledar dake tashin kamshin naman gas meat..

"Godiya make honey"

"To a sallameni...."

Zulfa'u tayi murmusuhi Tana gyara zaman da tayi...a kujerun bayan motar suke a zaune..

Rayyan ya rufe motar ruf, Dama ga glasses din motar bakake ne, Na waje bayaa gano cikin motar sai dai na ciki su gano waje.. nan suka shiga sheqe ayar su shida zulfa'u. Sai daya tabbatar ya wanki kudin sa da naman sa ajikin ta sannan ya jange ta daga jikin sa yana gyara zaman rigar sa yace,

"Zan tafi."

"Har zaka tafi ?"

"Madam na jira na agidan biki zan dakkota"

Zulfa'u ta yamutsa fuska jin ya ambaci matar sa tace,

"Ka fara ko?"

Ya saka hannun sa ya lakuto habarta yace,

"Nagaya miki ba sau daya ba ... Zan sake maimaita Miki akaro na ba adadi.. Ni fa ke nakeso nake Kuma kauna.. baa yadda zanyi ne don an aura mun ita ne, ta zamar mun karfen Kafa.bakiga sai nazo wajen ki nake samun nutsuwa ba zulfa babe?"

"Hakane"

"To ki kwantar da hankalin ki na gaya miki akwai abunda nake shiryawa sayya kammalu Zan sallameta ke Kuma na auro ki ki shigo ciki ... Ke nake so ba ita baa me zanyi da ita inada kamar ki uhm?"

Ya fada yana shafa fuskar ta...zulfa'u sai dadi ne ke sake ratsa ta ta saki tattausan murmushi..

Rayyan ya sake Kai mata sunba sannan ya bude motar sukayi sallama ta fice ta shige cikin godah shi kuma yaja motar ya tafi

Zuciyar ta fes Kalaman rayyan na dada faranta mata rai,

"Nagaya mikii ba sau daya ba ... Zan sake maimaita Miki akaro na ba adadi.. Ni fa ke nakeso nake Kuma kauna.. ba yadda zanyi ne don an aura nun ita ne ta zamar mun karfen Kafa.bakiga sai nazo wajen ki nake samun nutsuwa ba zulfa babe?..

"To ki kwantar da hankalin ki na gaya Miki akwai abunda make shiryawa sayya kammalu Zan sallameta ke Kuma na auro ki ki shigo ciki ... Ke nake so ba ita ba me zanyi da ita inada kamar ki uhm?"

Ta runtse Ido tana ayyano ranar da zaa daura mata aure da rayyan rabun ranta...






#FREE BOOK
#NOVELLA (SHORT NOVEL)

    



  ®️MX

KADDARA!!!💔 KOWA DA IRIN TASA👯👨‍❤️‍👨💍 (COMPLETED)✅Where stories live. Discover now