chapter 12

73 5 0
                                    

🍇MunayaMaleek🍓


_By NoorEemaan_📚✍️


Masu min Sharing, jazakallahu Khair, Allah ya biya ku da aljanna.💖

Xii...
(12)

Matsalar da Maleek ya fara fuskanta a dalilin giyan da Sa'adah  ke bashi da maganin bacci shine  *weak brain* kwakwalwar sa ta dawo bata ja sosai, a makaranta ma  baya wani kokari, bayan kaf makarantar yana sahun son gaba a masu kokari, abin ya damu *class teacher* din sa, ta kira shi staff room tana masa tambayoyi ko zata gano wani abu, amma har ta gama amsar shi ita ce "nothing ma" dole ta sallame shi ya tafi.

Bayan  sun gama exams din third term, ya zo a karshen shekara,  wanda kuma yayi daidai da end of the year party da makarantar ta shirya, iyaye, teachers, manyan baki dalibai sun cika makarantar, aka gabatar da party'n cikin tsari da burgewa, bayan Dalibai sun gama gabatar da cultural dance na kabilu daban-daban, sannan aka fara kiran daliban da suka fi  k'ok'ari ana basu gift cikin karramawa, class by class, har aka zo kan yan class din su Maleek.
Maleek dake zaune cikin dalibai a tsabtatacciyar Uniform din sa, ya riga ya sa a ransa cewa shine zai zo na ɗaya, sabanin haka sai ya ji wani suna, bai fidda rai ba yana jiran a kira shi a matsayin *second postion* still wani aka kira, suka kalli juna shi da Shakur, kiran sunan wata yarinya da aka yi a matsayin ta uku ya katse musu kallon da suke wa juna, nan kallo ya dawo kan Maleek musamman dalibai da malaman da suka san kokarin sa, suna tunanin what happened this time around? Amma class teacher din su ta san za a yi haka shiyasa Bata yi mamaki ba, Maleek yayi kasa da kansa, ya ji hawaye ya cika idanun sa, saboda hango wasu dalibai da suke nuna shi suna dariya, dama akwai masu jin haushin  kokarin sa,  ya saka hannu ya goge hawayen, jijiyoyin kansa suka fito radau suka kwanta a gefen kansa, alamun ransa a bace yake, bai kuma fahimtar komai ba har aka tashi  taron, Sa'adah da itama ranta ba dad'i, domin ita ce duk shekara take amsar wa Maleek gift cikin alfahari, a yau ma ta riga ta san cewa zai ci, shiyasa ta dau wanka cikin rantsatsan lace, ta shirya ta zo, saboda a san uwar su Maleek bata wasa bace, amma sai taji sabanin abinda ta saka rai, domin yanda ake yabo da koda Maleek a duk lokacin da za a bashi gift ba karamin fasa mata kai yake ba, wani zubin ma idan ta kawo su makaranta haka malamai zasu ke yabon sa a wajen ta.
Jiki a sanyaye ta karaso wajen motar da driver ya kawo ta yana jira,
Su Shakur kuma  suka tafi classes  din su domin karbo report book din su.

Tana nan tsaye tana jira, class teacher din su Maleek ta zo tace "Good day ma, kamar yadda kika sani sunana miss blessing, class teacher din su Maleek, a gaskiya ban ji dadin yanda performance din ABDUL-MALEEK DAWOOD BULAMA ya yi kasa ba, nayi kokarin jin ko akwai wata damuwa ko wani abu da yake hana shi karatu amma yace min ba komai, shiyasa nace bari na Miki magana tunda ku iyayen sa ne, zai iya sanar da ku wani abu dake damunsa ko ke hana shi karatu"

Sa'adah tayi saurin cewa "TOH  shikenan Nagode Anty, zamu tuntube shi, in Sha Allah za a samu improvment next term, thank you"
Da haka suka yi sallama, ko kadan son zuciyar ta bai sa tayi la'akarin cewa  abinda take masa da maganin da take dirka masa bane  ya janyo wanna sauyin daya wajen Maleek, har yake kokarin affecting brain din sa.

Tana nan tsaye, ta hango su sun taho hannun su rike dana juna, yanda Shakur  ke magana da Maleek  zai sa mutum ya gane cewa rarrashin dan'uwan sa yake,  bayan sun karaso wajen ta , duk suka mika mata result din, ta bude ta ga Shakur ya zo na uku, amma ba overall ba, Maleek ta bakwai, lallai dole Maleek ya damu, ko ta biyu baya zuwa, domin karfafa masa guiwa tace " my boy ka yi kokari kaji, worry not, everything will be fine ok?"

Ya girgiza kai yace " I'm sorry mum, ban yi kokari ba, nima ban san abinda yake damuna ba"

Tausayin sa ta ji  sosai, amma ta kasa yin la'akarin cewa ita ce sanadin matsalar sa.

MunayaMaleek Where stories live. Discover now