★★★

Da misalin ƙarfe takwas bayan sun gama dinining, Maleek ya shiga Dakin shakur, zaune ya tarar da shi a gadon sa rike da Qur'ani yana kokarin haddace surar da aka koya musu yau, waje Maleek ya samu ya zauna ya zuba tagumi yana kallon kanin nasa, duk da karancin shekarun sa, sai ya ji  kanin na sa ya burge shi matuka yanda ya bada himma yana karatu tamkar dan balarabe, sai da Shakur ya kai aya sannan ya dago kansa yayi murmushi, Maleek ya mayar masa da martani, karban qur'anin yayi daga hannun Shakur ya buɗe shafin Farko daga kasa, kurawa rubutun larabcin ido yayi, sai dai bazai iya karanta ko da harafi ɗaya ba, Shakur dake kallon sa yace "na koya maka? In fada maka nayi nisa sosai, malamin mu yace zan yi saurin yin sauka, yaro ka koya, ka iya na sallah, saboda malamin mu yace duk wanda baya sallah wuta bal bal ce zata ci shi" ya karasa cikin salon magana irin na yarinta.

"Koya min" Maleek ya fada yana mikewa wa shakur Qur'anin, kana ya matso dab da shi, suratul ikhlas suka fara da shi. Ya dan ji wuya kafin ya haddace aya biyu, zuwa lokacin dare yayi domin goma da kwata, mik'ewa Maleek yayi yayiwa dan'uwan sa sai da safe, a ransa yana jin daɗin ya fara iya karatun Qur'ani.

Shima Shakur dad'i yake ji ganin ya koya wa dan'uwan sa karatu gashi kuma ya iya. Abinka da kuruciya babu wayon nuna masa illar rashin zuwa islamiyya da baya yi.

***

A yau Alhaji Dawood zai dawo kasar, tun safe sai kara kimtsa gidan Sa'adah take, duk da cewa ba wani abu na datti, amma ta sauya wasu abubuwan saboda zuwan Alhaji, girki kala-kala suka shirya ita da mai aikin ta,  ta yi wa shakur wanka, duk da yace zai iya, amma ita gani suke har yanzu sun yi kankanta da yin wanka da kan su, zata yi wa Maleek shima ya ce zai iya, domin shi kam
yanzu ya fara jin kunya tana yi masa wanka saboda a ganin sa ya fara girma domin shekarun sa goma da watanin, gashi yana da girman jiki, murmushi Sa'adah tayi tace "Maleek You re still a baby, kabar ganin kana da girman jiki, wani wanka zakayi da kanka ya fita, oya zo nan" haka ya tsaya ta fara yi masa wankan, gaba-daya hankalin ta na ga jikin sa, wani murmushi ta saki da ita kadai ta san ma'anar sa, tana kintata yanda zai dawo nan da wasu shekaru..., kananun kaya ta sauya musu duka, sannan ita ma ta shige toilet din Dakin ta Domin kimtsa kanta.

Bayan Alhaji Dawood ya iso gidan sa,  murnar ganin sa hadi da gaishe-gaishe ne ya wanzu a tsakanin su, sannan ya tafi dakin sa domin yin wanka saboda warware gajiya...

Daddadare suna falo a zaune, shakur yace "Daddy ka fada mana surprise daka ce zaka mana idan ka dawo, ko Maleek?" Ya fada yana kallon Maleek din.
"eh daddy" Maleek ya fada.

Murmushi Alhaji Dawood yayi yace "surprise d'in dama shine kowa zai zaɓi kasar da yake son yin karatu tun daga degree har masters, idan kuma kun fi so a nan toh shikenan, sai na baku wani abu a matsayin gift din da na muku alqawari, cos I'm happy with you guys performance at school, shiyasa na dauki wannan alkawarin tun yanzu, da zaran kun karasa secondary school zaku tafi makarantar da kuke so"

Dam! Kirjin Sa'adah ya buga, idanun ta kyam kan Maleek tana jiran taji abinda zai ce...

Cikin doki Shakur ya fara cewa "daddy Ni Saudiyya  nake son zuwa, abokaina na class din mu nan zasu yi"

"That's good, Maleek kai fa?" Alhaji Dawood ya fada looking directly at him.

A hankali ya motsa labb'an sa yace "Ni University of salmanca dake Spain nake so daddy"

"Masha Allah, dukkanin ku kunyi zabe a makarantu masu kyau, duk da kai zaka yi nesa da gida" ya fada yana kallon Maleek dake dan sakin murmushin jin dad'in ganin daddyn su ya amince.

Sa'adah kuwa tamkar ruwan zafi haka taji an Watsa mata da jin amsar daya bawa Maleek, tana jiran ya ce kasar tayi nisa yayi karatun sa a nan amma sai taji ya amince, ta yaya zata juri yin nesa da shi, ina ma Shakur ne ya zabi kasar Spain ba Maleek ba, wani zafi da tukiki take ji a ranta, ga haushin Alhajin daya kamata, haƙa tayi fam kamar fanken daya sha uban yeast, bata ƙara sanya baki a hirar su ba, ta mayar da kanta kan plasma da ake hasko  India Film mai suna *ribbon* sai dai sam ba kallon take ba, tunanin yanda zata lalata tafiyar Maleek din  tun yanxu ta shiga yi...

MunayaMaleek Onde histórias criam vida. Descubra agora