MALEEK!!!
Tun bayan faruwar al'amarin nan ya rasa  nutsuwar zuciya, domin har sai ya sha barasa, tunanin sa ya gushe yake samun saukin zuciyar sa, ga Shakur da har yanzu baya kula shi abin ya ƙara damun sa.
Kamar yau zaune suke a dinning table su ukun, har da mummy, sai dai zaratan samarin babu annushuwa a tare da su, mummy dake serving din su breakfast  sai a yanzu ta lura basa hira cikin kaunar junan su kamar yanda suka saba, Domin tun bayan dawowarta daga gidan malam ta shiga damuwa mai yawa, domin har karyan rashin lafiya tayi ta dinga zaman daki, domin idan tace zata bari su hadu da Maleek  a ranar da abin ya faru komai zai iya faruwa har ta kai ta tona rufaffen sirrin dake zuciyar ta, wanda hakan zai sa komai ya lalace mata har ta kasa cimma burin ta.
Ganin shirun yayi yawa yasa tace "daddyn ku yace next week zai dawo" ta fada hoping zasu yi murnar da suka saba a duk lokacin da daddyn nasu zai dawo kasar, amma sai ta ga sabanin hakan, Shakur ne ya yi Karfin halin cewa "Allah ya dawo da shi lafiya" kana ya dire mug din hannunsa, ya mike hadi da cewa "na tafi mummy" bai jira amsar ta ba ya fita, nan mummy ta kara tabbatar da cewa something is fishy, Amma ta san bazasu fada mata abinda ke faruwa ba, domin ba a shiga tsakanin su, tun suna yara masu rike sirrin junansu ne, ta gwada Maleek dake juya cokali cikin mug mai dauke da coffee  tace "my boy meya faru tsakanin ka da dan'uwan ka?"

"Ba komai mum" ya amsa hadi da mike wa shima ya fita.
Mummy tace " i Said it, na san bazai faɗa ba, haka zalika dan'uwan sa" sai ta mike zuwa wajen window ta yaye labulen, daidai lokacin da Maleek ke kokarin bude motar sa, Shakur daya zo ta baya ya ɗan buge shi a baya, Maleek ya juyo, Shakur ya jefa masa hararan wasa, and then Maleek smile widely hadi da rungume dan'uwan sa, domin yasan tunda yayi hakan ya sauko daga fushin da yake dashi.
Shima Shakur ya rungume shi, domin yayi missing din sa kwana biyun nan, duk da ya ji matukar haushin abinda Maleek yayi, amma dan'uwan sa ne , is only brother, kuma hannun ka baya taba rubewa ka yanke ka yar, komai munin halin sa jinin sa ne" ya raba rungumar da cewa "muje ka fara ajiye ni a school sai muyi magana a mota" Shakur ya karasa maganar da zagayawa bangaren mai zaman banza.
Mummy ta koma da baya ta zauna kan kujera, ta na jin ina ma ina ma ta ji abinda suke cewa, ta shiga duniyar tunanin hanyar cimma burin ta.

A nutse yake tuki kan kwalta, Shakur ya kalle shi yace "ka min alkawarin ka daina shan giya"
Maleek ya rage gudun da yake, yace "zan yi kokarin dainawa Shakur, ka san I'm addicted to it, dainawa bazai yiwu a take ba, but zan yi iya kokari na wurin dainawa"
Shakur ya jinjina kai, ya san Maleek baya karya dan a so shi, kuma shi mutum ne irin open minded basa boye abinda ke ransu, duk da ba surutu ne da shi, a lokuta da dama ya kan kuma ce "Bazan taba yin abu domin wani ba"

"Amma kayi kokari saboda lafiyar ka da Allah, kasan haramune ko?" Maleek ya jinjina kai.
Shakur ya kara cewa "Sai alkawari na biyu amma sai Munaya ta dawo aiki zan faɗa maka, ina jin rashin lafiyar kanwar ta ne yasa bata yi resuming ba, amma hopefully zata iya dawowa this week"

Maleek ya dage kafadar sa, daidai lokacin da suka iso *Nile University*  inda Shakur ke lecturing, Shakur ya sauka suka yi sallama.

****

A hankali Cikin rashin kuzarin  da har yanzu bai dawo mata  ba take tafiya, sanye take da dogon hijab dinta onion color, Saboda yanda tunani ya mata yawa ko nisan tafiyar bata gani, kafar ta yayi bututu. BAYAN ta iso Company'n Maleek Nura mai gadi ke tambayar ta ko lafiya kwana biyu bata zuwa, ta ce masa lafiya a takaice, bata ko biyewa surutun  sa ba, ta nufi bangaren da office din Maleek yake, a yayin da take taka matatakalar benen komai daya faru a ranar ya shiga dawo mata, ta daure zuciyar ta domin bata son yin kuka, bayan ta isa ga kofar glass ɗin tana jiran kofar ta buɗe a lokacin ta hango Maleek zaune a had'add'en office din sa cikin sigar suit looking so smart and handsome as ever, taji mugun tsanar sa ya kara cika mata zuciya, har take jin tamkar ta rufe shi da duka, daidai lokacin da kofar ta bude kanta, a daidai lokacin ne Maleek ya dago rikitatun idanun sa ya zuba wa Munaya ko motsa su baya yi, fuskar sa dauke da wani yanayi da ba zai  fasaltu ba, Munaya ta  tako zuwa tsakiyar office din sa, ta fito da hannun ta dake cikin hijab mai dauke da ledar kuɗin nan  ta jefa masa har ya daki fuskar sa, raunin ta ya fito fili Sosai, ta fashe da kuka, ta kasa daurewa tace "I hate you with passion! Azzulumi Ga kudin ka nan na dawo maka da shi, Amnah is dead, kanwata ta mutu, meya amfanin kudin ka a gareni, nayi nadamar baka budurcina, Allah ya saka min abinda ka min ban yafe maka ba Maleek!" Ta karasa maganar cikin dacin murya, kana cikin sauri ta juya ta bar office din.

MunayaMaleek Onde histórias criam vida. Descubra agora