"Ta mutuuu" tace cikin kuka.

"Baban ku fa, ko wani daga dangin iyayen ku?"

"Doctor bamu da Kowa, bamu da Kowa sai kan mu"

"Ya Salam!" Likita ya fada cikin rashin sanin abin yi, domin bai san yadda zai mata wanna bayanin ba, gani yake tayi kankanta da yawa, ya kara kallon munaya yace "muje office dina" ya karasa yana barin dakin cikin sauri, Munaya ta kara kallon Amnah dake kwance kamar mara rai, sannan ta bi bayan likitan a sanyaye.

"Zauna" likita ya fada yana nuna wa Munaya kujera.

Kamar mai zama kan wuta haka ta zauna, a tsorace take matuka, likita yayi gyaran murya yace "am...i believe kin San cutar da kanwar ki ke dauke dashi ko?"

Cikin sauri ta daga kai alamun "eh".

"Good! A yanzu dai ta kai stage na karshe wanda take daf da rasa rayuwar ta matukar ba a mata aiki cikin gaggawa ba, domin shi Cancer yana undergrowing kullum ne, because is a disease in which the cells of a tissue undergo, uncontrolled (and often rapid) proliferation, it's Something damaging that spreads throughout something else, So the best shine a mata aikin, sannan sai ta cigaba da shan magunguna, domin shi karin ruwan nan da aka mata babu abinda zai kara mata a fanin cutar, sai dai ya kara mata karfi data rasa sakamakon aman da tayi, amma cutar na cin ta ta ciki, shiyasa dazu nake tambayar ki ko ina dangin ku, saboda kudin aikin ba kananu bane, I know you can't afford it alone, million uku da dubu dari tara ba wasa bane baby girl"

A firgice Munaya tace "do..doct....doctor! million uku da dubu dari bakwai aka ce wa Umma na last time"

Likita yace " gaskiya a da kenan, domin maganar da kike shekara daya data wuce kenan, yanzu kudin ya karu" daga nan bai kara cewa komai ba ya cigaba da aikin sa.

Munaya ta rufe idanun ta da tafukan hannayen ta ta fara rera kuka, ta mike zuwa gaban likitan ta tsugunna tace "dan Allah likita ku taimaka ku mata aikin nan, wallahi Allah zan nemo kudin duk inda yake na biya, Ni dai fatana ta rayu, wallahi zan biya, idan ma baku yarda ba muyi yarjejeniya, ku rike ta a wajen ku har sai na gama biyan ku sai ku bani kanwata, Ni dai ina so ta warke, dan Allah likita ka taimaka, ita kaɗai gareni..." Ta karasa cikin Muryar kuka mai narka zuciya.

Likita ya girgiza kai, yana kara tabbatar da yarintar Munaya, saboda abubuwan data faɗa bazai taba yuwa ba, tsari da dokar asibitin bazai taba yarda da hakan ba.

"Hakan bazai yu ba, ki Sani cewa ko iya kudin gado da karin ruwan nan dana yi wa kanwar ki aka barki dashi bazaki iya biya ba, You re even lucky kin samu ina duty ma da kika zo, da baza su karbe ta ba har sai kin ajiye dubu saba'in, which i know baki da irin wanna kudin, amma na dauki nauyin Hakan tunda baki da su, kuma kanwar ki na Cikin mayuwanci hali, abu daya dai zan iya taimaka muku dashi yanzu, magani za'a siya mata, wanda zai dan taimaka mata kafin a samu kuɗin aikin, but note kada a dauki lokaci Kafin a mata aikin nan, domin komai zai iya faruwa da ita" ya karasa maganar da rubuta mata maganin a farar takarda hadi da cewa "gashi bashi da tsada sosai i think bazai wuce dubu goma sha biyu da dari biyar ba, so ki siyo mata a pharmacy'n cikin asibitin nan a bata, but i repeat, aikin nan shine abinda sister'n ki ke bukata, magani bazai mata abinda ake so ba, so ki sa wanna a ranki"

Jinjina kai Munaya tayi, ta lashi busassun labb'anta kana ta fita daga office din likitan, cikin sauri taje pharmacy din, luckily kamar yadda likita ya fada 12,500 aka siyar mata, ta duba hannun ta ta ga saura 1,500 ta fita wajen asibitin ta ga wani provision store ta siyi yoghhurt mara sanyi sannan ta dawo cikin asibitin, direct dakin da aka kwantar da Amnah ta nufa, ta buɗe Kofar a hankali, idanun ta suka sarke dana Amnah dake kwance, tadan ji sanyi a ranta ta lumshe idanun ta cikin sakin ajiyar zuciya, ta kara buɗe idon, and then she saw Amnah smiling at her, ta karasa wajen gadon da sauri ta dago ta zuwa jikin ta tace "sannu Amnah, ya jikin ki, kin ji sauki ko?" Amnah ta gyada kai, Munaya ta sumbaci goshin ta da kumatun ta, sannan ta bude yoghurt din ta bata, Amnah ta kau da kai gefe, Munaya ta marairaice tamkar zata saki kuka tace "ki sha ko kadan ne ki sha magani kin ji" ta karasa cikin rarrashi.

MunayaMaleek Where stories live. Discover now