ZAZZAFAR KAUNA 241-250

Start from the beginning
                                    

"Lafiya na ganka tsaye anan ko jikin Madam ne.?"

Girgiza kai Moha yayi yana cewa.."A'a kai naji ka fita cikin daren nan shiyasa na fito Ina tambayar lafiya ko jikin Zulaihat din ne har
yanzun.?"

Murmushi saki yana cewa.."yanzun dai sauri nike tana ciki tana jirana bari naje gobe zamuyi magana and karda ka manta Hajja fa tana gidan nan dan haka ka shigo kawo gaisuwa kan lokaci byee."

Shima Moha apartment din shi yana nufa yana cewa.."Okay Allah ya kaimu...eh haka Sweetheart ta gaya man ka taho da Hajja zan shigo goben in shaa Allah take care byee."

Bayan ya shiga ya taddata tana bacci ajiye kayan yayi saman center table yana zama gefen gadon ya dan yanjota jikinshi yana kissing dinta a hankali..sai kuma ya  fara tsotsar bakinta yana cewa.."wakeup Baby tashi kici danwaken tashi Myluv please."

Dan bude idonta tayi a hankali tana saukewa a kan shi tana tura hannunta cikin sumar kanshi sai kuma ta sakar mashi da kiss tana cewa.."Na koshi Hubby."

Stop yayi kallonta,kamar ya ta koshi?bayan ita tace tana son ci?zaunar da ita yayi yana dan shafata a hankali yake magana yana cewa.."Kalbi dan Allah ki rufaman asiri kici wannan danwaken,idan baki ci ba ulcer na iya kama ki kuma ni zan shiga matsala dan ban san ganinki a cikin halin damuwa pls wife."

Langwabewa tayi a jikinshi tana turo baki bata ce komai tana k'ara lumshe idonta tana son komawa baccinta ma..kin barinta ta koma baccin yayi yana cewa.." Dan Allah Kalbi tashi yauwa masoyiyata yar'albarka." Dakyal ya samu ya taddar da ita yana dauko ruwa da wani container ta kuskure bakinta ya fara bata da kan shi.

Loma d'aya tayi ta kauda kai tana rike hannunshi da yake kokarin Kai mata danwaken tashi tayi da sauri tana nufar toilet ta tara amai sai ta gama amanta ya kuskure mata bakinta har da wanka sai da yayi mata sanann ya fiddota ya saka mata wata pink night gown tayi mata kyau sosai.

Har ta fad'a dan duk yau abinci bai zauna cikinta ba...da ta ci yake fitowa zama yayi damuwa cikin fal a fuskarshi yana kamo hannunta yace.."gaya man mai zan girki maki please  Babyna." Sauke ajiyar zuciya tayi tana cewa.."wainar fulawa da manja Hubby ka cika mata yaji please." Tashi yayi yana cewa.."angama Gimbiyata yanzun zan maki please yanmatana karda kuma kiyi bacci just 10mn zaki bani."

D'aga mashi Kai tayi tana dauko wayarshi ta shiga gallery tana kallon pictures..shi kuma fita yayi ya fad'a kitchen ya fara had'a mata wainar fulawa in minutes ya gama koma ya fara toyawa yar kad'an ya had'a shiyasa bai wani dad'e ba ya gama ya Kai mata.

Batayi baccin ba da kan shi ya bata biyu taci tace ta koshi ya bata zobon ta sha d'aya yaci ya rufe mata ya bata magani ta kwanta wasa ya kama yi mata sai dariya take a haka har bacci ya kwasheta... kureta yayi da ido yana kallonta komai nata tausayi yake ba shi,bata da matsala ko kadan ka biyaiya ga kuma da natsuwa duk abunda yake so a wajen mace Zulaihat tana da shi shiyasa a kulle yake godema Allah da ya bashi mata ta gari.

Washe gari da kan shi yayi masu breakfast da taimakon Hajja wai wainar gero take son ci kuma shi bai iya ba sai da ya sha tsiya a wajen Hajja sannan ya samu dakyal ta hawo sama ta nuna mashi yanda ake wainar gero.

Haka ake ta rayuwa cikin Zulaihat ya cika saka aiki kullun cikin saka Najeeb da Hajja aiki cikin yake kuma suna yi..amman ita Hajja sai ta dunga tsegumi kenan tana banbani kafin tayi nata.

Dan duk safiyar duniya sai anyi mata wainar gero da Koko watarana kuma Kunun kanwa harda tuwon dawa duk saka take ana mata..abunda Hajja take ma fada d'aya ne yanda idan ta matsa ayi mata ba wani mai yawa take ci ba sai ta ci dan kadan tace ta koshi sai tai ta fad'a ta matsa mata ta k'ara ci sab'anin shi Najeeb din da tace ta koshi zai ce to mai kuma za'a kawo mata.

Yau aka tashi da haihuwar Zubaida ta haifi yaranta yan biyu maza murna iya murna anyi a wannan family Najeeb da kan shi yaje kano ya matsama Umma sai da ya daukota ya kawo ta taga twins dan tunda akayi aurensu bata tab'a zuwa ba.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now