ZAZZAFAR KAUNA 31-40

223 7 0
                                    

*🌺DA'IMAN ABADAN*🌺
        _ZAZZAFAR KAUNA_
*~HOT LOVE AND FATE STORY~*

*BOOK THREE*

_STORY AND WRITING BY_
_©JAMEEY YAR'MUTAN KANKIA❣️_

_MANAZARTA WRITERS ASSOCIATION_

_Ban yarda yan YouTube su daukar man labari su mai dashi audio ba tare da izini na ba!yin haka babban laifi ne idan kana bukata yi man magana kai tsaye! 08160508316_

https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

*31-40*

Turus tayi ta kama kuhu tana kallonshi turo baki tayi tana yin wajen shi cikin hanzarinta,tana isa wajen ta fisge cup din da ke hannunshi tayi tana kallon sauran kadan ya K'arasa shaye mongo juice din..sakin cup din tayi saman carpet din da ke malale a parlon tashi yayi yana damkota yana cewa.

"Yaushe na zama abokinki har haka?nace yaushe na zama abokinki.?"

Furzar da iska mai zafi yayi yana mata wani kallo ranshi b'ace yake to the over akan abunda yarinyar tayi mashi ya ma rasa mai zai mata yaji dadi mai zai mata ko yaji sanyi a zuciyarshi? tambayar da yake ma kanshi kenan sakinta yayi yana turata ta fadi kasa darsam kallonta yayi yana nuna ta da tsaya cikin kaukausar murya babu alamar wasa a cikinta yace.

"Tun wuri ki dawo cikin haiyacinki karki yarda na fara daura hannuna a kanki ba zaki ji dadi ba,kuma daga yau ki k'ara daura abinci ba dani ba a gidan nan zan baki mamaki."

Tsaki yayi yana bar mata wajen,ta tsorota sosai da lamarin nashi na yau dan ya koma mata Najeeb din da ta sani a baya...ya koma mata wani ingarman zaki,hawayene suka zubo mata tana sharewa can kuma ta tashi tana cewa.

"Allah ya saka man."

Ko takan plate din bata bi ba ta koma room dinta ta fad'a saman gado tana sakin kuka mai cin rai,wani irin zafi da rad'adin marar adadi zuciyarta take mata,neman yunwar tayi ta rasa ga wata sabuwar tsanar Najeeb da taji tana mamaye lungu da sako a zuciyarta.

Tana cikin kukan Bacci yayi awon gaba da ita,bacci take rum da ciki kallo d'aya zaka yi mata ka gane bata jin dadin baccin sam baccin kawai take..tana sauke numfashin bacci kamar mai shan majinar kuka.

Tunda ya shiga room din shi yake zagaye-zagaye yana sakawa da kamcewa yake tunanin wani irin hukunci ya dace yayi ma yarinyar ta fara bashi tsoro,dan kuwa rashin kunyarta tayi yawa har ta wuce tunaninshi,wani irin rainine wanann yana shan abu ta anshe ta yadda k'asa haka kurum.

Wanka kawai ya shiga yana fitowa ya dawo parlo yana kallon yanda ta bar wajen bama ta gyara inda ta b'ata ba..kwafa yayi yana girgiza kai ya dauko mopa da kanshi ya gyara wajen ya maida plate din kitchen sanann ya dawo ya kashe duk abunda ya dace ya kashe ya kullo gida ya hawo sama.

Har zai shiga room dinshi sai kuma ya kalli room dinta yaga yau bata kulleshi ba kenan kamar yanda ta saba,dawowa yayi da baya yana shigowa a room din nata...wani sanyaiyen kamshi ya dakar mashi hanci lumshe ido yayi yana K'arasa shigowa.

Tsaye cak kamar wanda aka dan nama STOP haka yayi yana kare mata kallo,furzar da iskan bakinshi yayi ya mai hard'e hannayenshi a saman kirjinshi zuciyarshi na bugawa da sauri sauri rintse idonshi yayi ya bude yana mai tafiya a hankali a hankali kamar wani barawo haka yake tafiyar sand'o sand'o har ya ida karasowa a bakin gadon.

Murmushi yayi yana daukarta cak daga kwanciyar rud da cikin da tayi tana mai da mata kwanciyarta yanda ake son ko wane mutun ya kwanta...daura babban yatsanshi yayi saman lips dinta yana dan shafawa a hankali sai kuma ya dan K'ara hawa saman bed din a hankali ya daura bakinshi saman bakinta ya sakar mata Frenckiss a kan lips.

Lumshe Ido yayi yana tura hancinshi a tsakanin wuyanta ya zuko kamshinta yana mai k'ara bude hancinshi ya na shakar kamshin har wata har natsuwa ta fara saukar mashi,dan a rayuwarshi yana son kamshi bama kamar kamshin Zulaihat shi komai nata sonshi da kaunarshi yake, matsalarta d'aya rashin kunya da tabbata da ta koya a rana tsaka.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Unde poveștirile trăiesc. Descoperă acum