ZAZZAFAR KAUNA 171-180

Start from the beginning
                                    

Yana fitowa ya tadda ta zaune parlo tana yin breakfast, kauda kan shi yayi yana wucewa kitchen dan samun abunda zai ci dan shi Najeeb bai wasa da cikin shi yana cin abinci sosai ma dan sai yaci ya nak yake barin abinci idan ya samai shi... cous-cous yayi jalop yaji kayan lambu da sardine ya zuba a plate ya dauki ruwa ya fito ya zauna yana fara ci cikin natsuwa.

Miyau ta hadiye kuttt tun yana kitchen kamshin abincin yake kawo mata ziyara take ji taliyar da ta dafa ta fice mata a rai ba abunda take son ci saman da cous-cous din da ya girka.. kallon cous-cous din take tana tunanin yanda zata yi ta samu ko spoon d'aya ne tayi.

Tasan halin yan kayanta tasan shi in and out bai son wasa balle kuma raini ,kuma tasan wanann raini ne ita bata girka mashi ba a matsayin shi na mijinta ya kuma girka ma kanshi ace kuma wai zata ci,dama ace zaman soyayya suke wannan normal ne... Amman suna wannan zaman na doya da manja amman kuma tace zata ci mashi abinci tasan ta ballo august.

Ganin yanda yake cin abinci kamar ana mashi dole ko kuma ba dadi ohoo,ko dai harda cin abincin sai anyi mashi yanga dan ta lura yanzun ya maida komai nashi yanga sai kace wata mace,ajiye plate din hannunta tayi tana daukar spoon ta rike tana ta shi ta nufi wajen shi a hankali take tafiyar tana wani karkardawa kamar wata macijiya haka take juya jikin.

Sakin baki yayi yana kallon ikon Allah ganin direct wajenshi tajo ga kuma spoon a hannunta kamar wata mayunwaciya,tsaye tayi a gabanshi tana turo baki sai kuma can ta tsuguna k'asa tana langwabar da kanta gefe sai turo baki take...kwarewa ya kusa yi yanda take cinno mashi bakin tana wani shagwabe mashi ba karamin kyau hakan yayi mata ba har bai san sanda yace mata.

"Lafiya dai ko.?"

Kallar tausayi tayi mashi tana dan yarfa hannu cikin shagwabar ta tace mashi.."Dan Allah ka dan dan'man Koda one spoon ne nayi please." mamakin Karfin halinta kawai yake wai ya bata,ya bata fa tace?ita ta girka mashi da zata wani ce ya bata tsaki yayi ganin rainin wayau yana kokarin shigowa sai ya gama kanshi bai sake kallonta ba ya cigaba da cin cous cous din shi.

K'ara marairaice fuska tayi tana cewa.."haba Hubbyna dan Allah ka bani nifa ce taka fa." Kusan sakin plate din yayi sai da yayi hanzarin rike abinci wani irin sanyi yaji ya zirarci zuciyarshi Koda kuwa dan ya bata cous-cous tace mashi Hubby taji dadi sosai,amman bai nuna mata ba sai ma kauda kanshi gefe da yayi ya yana cigaba da abunda yake ganin yana niyar cinye couscous din tayi sauri anshe plate din tana yin baya tana cewa.

"Allah ba zaka cinye wannan delicious din Kai d'aya ba, haba Hubby Kai ko dan tayin nan na ido guba babu ai wannan ba zaman amana bane." Ta ida maganar tana d'age mashi gira  d'aya da kashe mashi Ido tana mai Kai spoon a baki ta fara ci, lumshe Ido tayi tana kallonshi tana jingina mashi tace.

"Wooow."

Harararta yayi yana nufo ta da gudu tayi hanyar room dinta bin ta yayi yana cewa.."Kee tsaya ki bani abinci na." Makale kafad'a tayi tana cewa.."Allah ba zan bada ba idan baka koshi na ga sauran taliya nan sai ka ci."kwafa yayi yana cewa.."ce maki nayi ki bani abinci na ko.?" Girgiza mashi kai kawai tayi tana Kara loma,har wani lumshe Ido take tana wani karkarda Kai,tsaye yayi ya kama kuhu yana kallon yanda take cin abincin har wani lumshe ido take hakan da take sai ya Kara mata kyau ma.

Girgiza kai yayi yana sakin tsaki ya nufi hanyar room din shi,dariya tayi tana cewa da karfi.."God bless you Babe,ka iya delicious fa." Murmushi kawai yayi yana shigewa room din shi ya wanko bakin shi ya fito yana nufar wayar shi ya dauka yana nufar hanya.

Fitowa tayi da size bag din ta tana bin bayan shi ta shiga motar sai wani boye dariyar mugunta take, ganin yanda ya wani hadiye rai sai wani cin magani yake a dole bai ji dadin cinye mashi couscous da tayi ba,wayarshi ce ta fara ringing sai kuma ya saki murmushi yana kallonta ta gefen ido.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now