ZAZZAFAR KAUNA 161-180

Start from the beginning
                                    

Shima wankan ya fara ya fashe jikanshi da turaruka ya jura jallabiya ya fito direct kitchen yana nufa dan hakanan kawai taji yana son cin indomie da sardine yana shiga ya daura takunya ya fara aikin da ya kawo shi...bayan ta gama wanka ta zauna ta shafa cream sai turaren da ta fashe jikinta dasu ta samu wata riga ta saka sai wandon rigar da iya ka cin shi saman cinya ta saka yan rigar wanda a dai dai cibiyarta ta tsaya cibiyarta a waje take.

Gyara gashinta tayi tana parking din shi ya tsaya saman gadon bayanta, samun lipstick mai shinning tayi ta shafa ma bakinta sai ya Kara fiddo da Kyaun da tayi dan ba karamin kyau kayan suka yi mata ba..hula ta dauka tana daurama kan ta ta jefe sweet a baki ta fito parlo tana dan shafa cikinta saboda da yunwar da taji tana addabarta, kitchen kawai ta nufa dan samun ta girka indomie dan kwadayin indomie da sardine taji kawai tana son ci nan take.

Tafiya take a hankali tana wakar zabina taurarowa a hankali tana rera wakar har wani lumshe Ido take dan tana son wakar sosai dan kalaman da suke cikin wakar suna cire mata kewa ba kadan ba..Dan jam tayi da ta shigo kitchen ta gan shi sai kuma ta dan turo baki tana mai cigaba da wakarta tana cewa.."Allah ya jikaina idan har ba Kai wa'adin rayuwata yazo karshe." Dan lumshe ido yayi yana budewa ya sauke su a kanta sai kuma ya dauke kan shi gabanshi yana faduwa da sauri da sauri,dan wani irin bala'in kyau tayi mashi ji yake kamar yaje ya rungume ta ya shanye dan karamin bakinta da take rera wakar soyayya da shi ,ga har cikin zuciyarshi yake jin kalaman da take firtawa na wakar suna shigarshi.

Duk da ya nuna baison da shigowarta ba amman kunnuwanshi suna a wajenta haka ma hancinshi dan har dan lumshe ido yake idan ya shako kamshinta...sosai kamshinta yake sakar mashi natsuwa daman shi gwanin son kamshi yana son kamshi sosai yana son kamshinta dan rasa takaimaiman irin kamshinta yake, dan kamshinta dabam yake da na sauran.

Tunda yake bai tab'a jin kamshi mai dadi da saka zuciya natsuwa irin nata ba..har k'asan ranta taji rashin dadin yanda yake nuna mata ko kular nan da yake mata,cizewa tayi tana tsayawa kusa da shi ta kunna gas itama ta dauko tukunya ta daura saman wuta tana zuba ruwa.

Cikin natsuwa take komai kamar yanda ya nuna bai san da shigowarta ba haka itama ta nuna bata san da mutun a cikin kitchen din ba..Dan bata fasa duk abunda tayi niyar yi a kitchen din ba,bayan tayu giretin din kayan miya ta zuba a ciki sai ta nufi wuka zata dauka dan yanka albasa da yake har albasar tama fiddo ta gyarata wankawa kawai zatayi ta zuba.

Daman tunda ta dauko albasa shima ya dauko ta shi ya gyara dan har ya manta da ana saka ma Indomie albasa saboda shigowar da tayi komai sai ya kwance mashi,tayi mashi kyau iyakar kyau ga fararen cinyoyinta da suke ta glowing suna daukar mashi Ido ji yake Ina ma zata bashi daman da yau sai ya nuna mata irin son da yake mata,amman yasan yanzun yana tab'a ta zata yi mashi rashin kunya tace mashi ma daman sha'awarta yake shi kuma kalmar da yafi tsana ta fito daga bakin ta kenan.

A tare suka kaima wukar farmaki kowa yana son ya dauka,har hannunsu yana hadewa da na juna wani irin shock suka ji lokaci guda da wata irin kasala da ta dirar masu,a tare suka d'ago Kai suna kallon juna Ido cikin Ido sai kuma can ta dauke kanta tana son dauko wukar amamn ya rigata dauka sai wani cize fuska yake,itama rike wukar tayi tana turo baki gaba tana ta shagwabe fuska sai wani tura mashi boobs dinta take tana langwabar da Kai gefe.

Duk wani kuzarinshi neman shi yayi ya rasa ya kuma kusa kasan yin control din kanshi,ga kamshinta da yake ta shige mashi hanci yana Kara sakar mashi da wata irin sha'awarta zazzafa ganin gab yake da yin abun kunya sai ya sakar mata wukar yana barin kitchen din da sauri.

Da kallo ta bishi sai kuma can ta tab'e bakinta ta kashe wutar da ya daura tukunyarshi ta fara yanka albasarta tana sakin murmushi sai kuma ta kalli hannunta ta Kai hannun a hancinta tana shakar kamshin shi lumshe ido tayi tana cewa.."Ina sonka Mijina." Wani murmushi tayi tana sauri ta karasa girka indomien ta taje ta zauna tasan yana parlo tana son ta cigaba da ganin shi dan yayi mata kyau sosai.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now