ZAZZAFAR KAUNA 151-160

Magsimula sa umpisa
                                    

"Kaji matsalarka ko?kaji shirmenka ko?Kai yanzun a tsakaninka ga Allah Moha ka rasa wa zaka sako a cikin shirmenka sai Seemarh? Seemarh fa Moha?kana nufin da girma na zan dunga yage baki Ina gayama kanwata kalaman soyayya kanwata din ma wai Seemarh,yarinyar da take ganin girma na da mutuncina tabbas yau na ida yarda hankalinka ragaigeni ni wallahi Zubaida tausayi ma take bani da take zama da kai kana da wannan halin Kai dai ga ka nan hankali hankali hauka hauka to sake wata ko kuma a bar plan din baki d'aya kawai."

Dan shuru Moha yayi yana kallon shi sai kuma ya b'ata fuska yana cewa.."ni din ne mahauka ci ko.?" D'aga Kai yayi yana cewa.."kusan mahaukaci mana Moha,inba hauka ba taya zaka ce nayi soyayyar karya da Seemarh bari fa kaji Seemarh matar aure ce kuma ni nan akwai aure tsakani na da Seemarh tun da ba ciki d'aya muka kwanta ba understand me Moha."

D'aga kafad'a Moha yayi yana cewa.." ka kawo uzurinka amman har na samu wani mafitar kuma Allah yasa shima yayi maka karda ka sake zagina dan kawai kaga na damu da damuwarka ai dole kayi man duk abunda ka gadama ai." Murmushi Najeeb yayi yana cewa."sorry nawa ba zan sake ba ai nima ai na damu da damuwarka idan baka damu da damuwata ba wa zai damu da ita tun da wanda zan ma gaya ma damuwar bata bukata ta a rayuwarta Kuma dai kasan su Ammie su ba cika maida Kai sukayi da wani concentrate akan damuwar mutun ba idan ba babba bace."

"Yeah! Haka ne kuma ni cewa nayi mai zai hana mu dunga yin wayar a matsayin saurayi da budurwa idan kuna tare muna message ya kaga wasan zai kasance." Kure Moha da Ido Najeeb kawai yayi yana tunanin anya Moha ba kwayoyi ya fara sha ba?Kodai wannan sanyin da ake ya fara rudashi daman yasan shi bai son sanyi ko kadan,kallonshi yake sosai yana son gano Ina matsalar take ya ke ta soki burutsu sai kace wani wawa.

Ai ko wawa ma baya haukan da Moha yake yi a yau din nan,taya zasu wani kama wayar soyayya bayan shi bai da muryar mace?shi da yake da murya irin ta ingarman mazajen nan a haka zai kama waya da shi yarinyar ta koma yi mashi kallon banza yana soyayya da mace mai murya maza babu langwasa murya balle kuma azo ga yar'shagwabar nan da ake ta soyayya sai kawai yayi tsaki yana cewa.

"Heyy Mr Man I beg please get out of my office."

Dariya Moha ya fashe da ita yana k'ara gyara zaman shi sai dariyar shi yake, daman yasan da wuya ya karbi wannan shawarar amman kuma dolen shi yayi accepting dinta , Dan ita ce last chain din su a wannan plan din nasu,haushin yanda yake mashi dariya yaji wato haukan dai ne yake da gaske kuma ya rasa a Ina zaizo yayi shirmenshi sai a office din shi yazo ya hanashi aikin da ya dace yayi, yana ta yi mashi wawanci tsaki yayi yana cewa.

"Dan Allah Moha ka tashi ka barman office kaje office dinka ka kira matarka tazo kayi mata haukanka ko kuma ka kwasheta kuje gida sai kayi haukan nasan ita zata iya dauka,ko kuma nace ta saba da wanann wawancin naka ni dai kam ba saba ba balle kace."

Tsagaitawa da dariyar shi Moha yayi yana cewa.

"Ai Najeeb a wajenka na koyi hauka da wawancin my friend c'mon tsaya kaji yanda abun zai kasance sai ya ma fi show akan wata Seemarh dan sai yanzun naga tsab zata iya yi mana hauka da shirme tunda kasan ta da wasa ,sai ana maganar gaske ta maida ta wasa da dai Meelat ce kuma daman nasan ba zaka yarda a saka Meelat a maganar ba shiyasa ma ban kawo ta ba."

Dan shuru yayi yana hutawa saboda da dariyar da yayi sai kuma ya dauko ruwa mai saukin sanyi a freeze ya sha yana zama ya kalli Najeeb ya fara cewa.."haba Najeeb sai kace ba wani dan Boko ba haba Dr ne fa kai?Dr fa Najeeb amman ace baka san komai na technology ba?abun kunya ne wallahi wasu ma suji halin da ake ciki kamar ka dai baka san ana chanza voice ba a waya haba mana just voice dina zan chanza ba Ina da waya Smart phone ba.?"

D'aga ma shi Kai kawai Najeeb yayi yana kallon shi yana son yaji karshen wannan game din dan shi mamaki Moha yake ba shi sosai,Ina yasan ana chanza murya a waya? tambayar da yake ma kan shi kenan,Dan shi yasan kullun dai suna tare basu rabuwa ada harda bacci a room d'aya suke yi da suna kano amman duk bai san ana chanza voice ba sai yau to shi wa ya koya mashi ana wani change of voice a waya,cigaba da cewa Moha yayi.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon