ZAZZAFAR KAUNA 131-140

Börja om från början
                                    

"Na gaji sakinta kawai zan yi kowa ya huta."

Zaro ido waje Moha yayi yana girgiza mashi Kai sai kuma ya kure shi da ido yana son tabbatarwa shin wannan maganar da gaske daga cikin bakin Najeeb ta fito ko kuwa? Koda bai da lafiya ne? tabbas bai da lafiya da yana da lafiya tabbas ba zai tab'a furta wannan kalma ba.

Wai saki,saki fa?sakin ma wai Zulaihat yake cewa zai saka,Ina son da yake mata ya tafi?Ina kaunar take?duka duka yaushe akayi auren da har maganar saki zata fara shigowa?auren da ko wata shidda bai yi ba ake cewa za'a kashe shi?wanann wani irin laifi ne tayi mashi mai girma haka?

Tabbas akwai abunda tayi mashi wanda ya tsaya mashi a zuciya har yake b'ata mashi rai har da zubda hawaye ga kuma saki da yake cewa zai yi ,shi abun ya tsorata shi sosai da yaji kalmar saki tana fitowa a bakin Najeeb,dafa shi yayi yana cewa.

"Yaushe ka fara shaye-shaye ban sani ba.!?"

Murmushi mai ciwo Najeeb ya sakar ma Moha,baiyi mamaki ba dan Moha yayi mashi wannan tambayar,dan ya lura kamar yana mashi kallon wani mahaukaci mahaukaci dan kawai yace zai sake wanda bata son shi..furzar da iskan bakinshi yayi mai huci sosai yana cewa.

"Moha amfanin mai zama da wanda bata sonka?gayaman dadin mai zama da wanda take kallon kwayar idonka tana gaya maka bata sonka bama iyakar bata sonka ba harda cewa take bata kaunarka sanann kuma ta kalli idonka tace daman ba dan Allah ka aureta sai dan wata manufa ta daban."

Shuru yayi yana jinjinar da kanshi jikin kujerar da yake zaune yana tura hannunshi saman lips din shi ya shafa a hankali yanda yaji yana mashi zafi kadan,d'agowa yayi yana kallon Moha yace.

"Ba wannan ba baka isa da ita ba,baka isa ka sata ba balle kace daina ta daina bata jin kunya bata jin komai ta kalli idon mijinta tayi mashi tsawa ko kuma tayi mashi tsaki ta gaya mashi duk abunda ta gadama."

Murmushi yayi yana cigaba da cewa.."Moha ka sanni kasan halina kasan abunda zan yi da wanda ba zan iya ba tabbas nasan ka sani sai dai baka san zan iya rabuwa da ita ba duk a tunaninka,bari kaji wallahi da gaske nike sai na sake ta taje ta auri wanda take so dan ba zan iya daukar rashin kunya ba,karda azo ayi abun kunya na karya yarinyar mutane azo kuma ana wata magana ta daban kaga maganin ayi karda a fara."

Murmushi Moha yayi yana cewa.."naji duk uzurinka Najeeb amman duk da haka bai dace kalma marar dadi irin saki tana fitowa daga bakinka ba,tabbas bata kyauta ba ai ko da ce bakomai bai dace ta dunga cewa bata sonka ba saboda abun ma bai dace ba amman kasan yanda za'ayi.?"

Girgiza kai Najeeb yayi bai ce komai ba yana kallon Moha,gyara zaman shi Moha yayi yana surbar tea sai kuma ya ajiye yana cewa.

"Tana sonka fa sosai."

Wani kallo yayi ma Moha yana cewa.

"Sona kuma?yarinyar da ke kallo idona tace bata sona ita sai na sake ta kake cewa tana wani sona,taya Kai kasan tana sona.?"

"Come down my friend." Dariya Moha yayi yana cigaba da cewa.." maida wukar bari kaji dalili na na cewa haka." Tsaki kawai yayi bai ce mashi komai ba sai dai zarara mashi Ido da yayi yana sauraren shi,Shima Mohar bai damu kin mashi maganar da yayi ba ya cigaba da cewa.

"Zulaihat na sonka Najeeb kuma tana kaunarka dalilina na cewa haka Ina ganin tsantsar sonka a cikin idonta ta kwantar da hankalinta ta fahimci son da take maka ne ta kasa saboda kawai a ganinta kaima ba sonta kake ba and sai yau na ida tabbatar da tana sonka Najeeb."

"Yau kuma? Mai ka gani har ka tabbatar da tana sona.?"

"Yau tun da suka shigo office dina na fahimci tana cikin damuwa,sai dai ban tambaye ta ba amman Ina lure da duk wani motsinta har muka iso gida ta wuce gida muka shiga namu gidan,bayan mun huta nike tambayar Darling maiye matsalar kawarta maike damunta? Kasan mai tace man.?"

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Där berättelser lever. Upptäck nu