ZAZZAFAR KAUNA 111-120

Start from the beginning
                                    

Murmushin gefen baki yayi da yaga har goma saura minti arba'in sai a lokacin ya tashi ya shiga wanka yana fitowa kuma ya zauna ya b'ata lokaci wajen shiryawa sai da ya dauki gayu iya gayu Shima sannan ya fito sai baza kamshi yake...kuma fuskarshi a sake take babu yabo babu fallasa,Koda ya fito zaune ya tadda parlo ta buga tagumi ko inda take bai kalla ba ya nufi hanya.

Da kallon banza ta Kara shi sannan ta tashi tana gunguni k'asa k'asa tana cewa..."wallahi sai mutun yasan wa ya b'ata ma lokaci,dan nima sai na rama wallalhi soon." Murmushi yayi kawai yana cigaba da tafiyarshi yana fatan ta rama din kamar yanda tace,abunda bata sani ba yana jin magana ko ya take dan kunnenshi jine da shi,ita kuma akwaita da maganar gunguni duk a tunaninta ba jinta yake ba sai dai ba haka bane ras yake jin ta sai dai kawai ya kyaleta dan bai da lokacin ta.

Koda suka shiga mota bai bar gidan ba sai da ya gama magana da gateman sannan ya dauki hanya tafiya take slowly,kamar ma bai son taka motar yake tafiyar kamar wani sabon tuki(learner) tun tana zuba Ido tana kauda kai har ta Kai da hakurinta yazo bango ko kallonshi bata yi ba gefe take kallo tace.

"Kaga Malan maza sauke ni nan bani bukatar ka k'arasa dani."

Banza yayi da ita ya cigaba da driving din shi yana Kara rage gudun motar,wani tsaki ta buga tana buga mashi tsawa tace..."Wallahi idan baka tsaya ka sauke ni ba zan balle marfin motar nan na fita kaji dai na gaya maka nace ni ka saukeni ko ana dole ne.?"
Yanda tayi mashi maganar without respect kamar ma tana bashi order yaji ran shi yayi koluluwa wajen b'aci,duk yanda yake son ya fita daga harkar yarinyar da kauda kanshi a kanta ita ke tsokaloshi dan bai zai iya talerance din rashin kunya ba,zai iya daukar duk haukan da zata yi mashi amman ba zai iya daukar rashin kunya ba.

Gangarawa yayi gefen titi yana kashe motar ya kuma sanya mata lock yana waigowa ya balla mata mari k'ara ta saki tana danne kumatunta dan unexpected haka yaji saukar marin kafin ta dawo dai dai taji ya ja mata kunne da karfi yana cewa.."Dan ubanki ni zakiyi ma tsawa?ni sa'anki ne?ni zaki yi ma tsaki a matsayina na mijinki?ai ko ba komai ban cancanci tsaki daga wajen ki ba tun da har na kasance malaminki,wato rashin kunyar taki har ta wuce tunanina ko?yaushe kika zama yar'iska marar mutunci haka? Zulaihatu ni Najeeb yau kike ma tsaki?wato dan Kinga ina raga maki shine abun naki yake gaba ko?"

Tureta yayi yana cewa.."duk yanda nike da mutun mudun yace zaiyi man rashin kunya tsanarshi nike,dan ni Najeeb bani zama inuwa d'aya da marar kirki da kunya kuma ni gidanmu ba'a koya man yi ma na gaba dani tsaki ba ko kuma tsawa balle rashin kunya."

"Karda kiga kina man iskaci Ina zuba maki Ido kiyi tunanin tsoronki nike ko wani abu ko d'aya,sai dai Ina guje maki ranar da zaki ji kunya,Ina guje ranar da zakiyi nadama marar amfani Zulaihat har yanzun kina cikin lokacin da na dibar maki ,idan har lokaci ya kure maki wallahi sai kinyi kukan nadama da idonunki ki shiga hankalinki tun wuri ki san abunda ke maki ciwo."

"Shashashar banza da wofi kin bani kunya kuma kinyi disappointed dina wallahi,yanda nayi tunani ba haka na gani ba ashe ke kura ce da fatar akuya ban sani ba?wallahi Ina nadamar aurenki da nasan aurenki ba zai kareni da komai ba sai rashin arzki da rashin kunya da ban aureki ba,ki sani ina sonki kuma ina Kaunarki har cikin raina Zulaihatu,na gwanmace na bari sonki yayi ajalina zai fiye man da wanann kayan haushin da takaici da kike man,tun wuri ki shiga hankalinki tun kafin dare yayi maki,ki bar ganin ina sonki da kaunarki kina man duk haukan da kika gadama wallahi zan iya hakura da ke ko da kuwa hakan zai zama ajalina dan ban daukar raini balle wulakanci useless."

Kuka kawai Zulaihat take,ga rad'adin mari ga kuma bakaken maganganu da yake jafar ta dasu,mai yake nufi da gidansu ba'a koya mashi yi ma manya rashin kunya ba?kenan yana nufin ita ba'a bata tarbiya ba a nasu gidan?jin ba zata iya shuru ba ace ya dasa mata kalamai munana a banza ta d'ago tana kallonshi hawaye na diga daga cikin idon ta tace.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now