Dan matsawa yayi kusa da bed din yana dan bubbugawa a hankali,baccin yayi nisa kuma ga dukan alamun tana jin dadin bacci,duba da hakan da yayi sai taji bai iya tada ta daga baccin,samun waje yayi saman kujerar room din ya zauna ya fiddo wayarshi ya shiga Twitter dan ganin labarai.

Ya dade a wajen har shidda tayi amman  ya kasa tadata duk da Kiran sallar mangariba da ake yi amman ji yake ba zai iya tada ta ba,tashi yayi ya shiga toilet din cikin room din yayo alwallah yazo ya shimfida carpet yayi sallah,yana cikin azakar ta bude idonta a hankali.

Murza idon tayi tana shafa inda take, firgigi ta tashi zaune tana sauke idonta kan shi da yake addu'a,mamaki take daman a office take bacci nan ba a gida ba? lokaci ta duba taga 6:50 ,duk bacci take kuma maimakon ya tadata shine ya barta tana ta baccin asara Allah ma yaso tayi la'asar da sai abun yayi mata yawa.

Murza idonta kawai take tana sunburo baki gaba,bayan ya gama sallar ya nade carpet ko kallonta bai yi ba ya taitara kayanshi ya nufa hanya,dan gutun tsaki tayi tana shiga toilet ta wanko fuskarta da bakinta ta zura hijab dinta ta dauko jikarta ta fito,tsaye ta ganshi bakin office din tana fitowa ta wuce shi bata ko kalle shi ba.

Da harara ya raka ta yana kulle office din ,da yake bata manta gudun da yayi da ita ba dazun ba shiyasa bata wani shiga baya ba,gaban mota ta shiga sai wani shan kamshi take,inda take bai kalla ba balle ya nuna yasan ta na yi dan alkwari yayi ma kanshi bai sake shiga harkarta balle har ta rainashi ko kuma tayi tunanin wani abu na daban.

Ko da suka dauki hanya bai fasa yin gudu ba saboda yana da abun yi ,dan haka ba zai biye mata ba ya kama jan mota kamar ta yan koyo, tsaki yaja yana duba irin b'ata mashi lokaci da tayi tun daga gun zuwa har zuwa yanzun dan ba dan ita ba dan tun wajen 5 yana cikin gida yana hutawa ko kuma yana gidan su zai gaida su Mom.

Tabbas ba zai iya biye mata ba ya zama unserious a banza a wofi dole ya samo mafita kam...bayan sun iso gida  ya kwaso kayanshi ya wuto cikin gida ,wanka kawai ya shiga yana fitowa ya shiga kitchen ya daura girki...shinkafa da wake ya girka har da hadin salad dan daman shi Najeeb ba daga ba wajen iya girki duba da basu zauna gida ba rabin rayuwarsu a makaranta suka yi ta shiyasa ya iya girki tun da shi bai cin abincin waje yana da kyama.

Itama wanka ta fara yi sanann tayi sallah tana zauna har aka kira sallar isha'i ta tashi tayi sallar ta fara shirin bacci,sai da ta gama sannan ta saka ma room dinta key tana dauko cake da yoghurt ta zauna ta fara ci tana kunna data,tana shiga cikin whatsapp tayi karo da message din Zubaida tana shiga ta karanta abunda tace sai tayi tsaki tana cewa.

"Matsalarta daga ita har shi,taje tai ta son shi da kanta zatace ta fasa saboda bakin halinshi." Dariya Zubaida tayi tana cewa.."Amman Sis ni abunda ke bani mamaki d'aya kishin da naga kin nuna a fili kin kasa boyewa ."

Tsaki ta tura mata tana mata voice tace.."kin manta ko ba kishi ba..nidin ce zan nuna kishin wanda ba sona yake ba?Allah ya tsareni yo kishin mai zanyi maiye abun kishi a wajen shi balle har nayi.?" Emoji din mamaki Zubaida ta turo mata tana cewa.."Nima abunda na gani kenan Sis Babu So Mai ya kawo kishi.?"

Sunburo baki kawai tayi bata ce mata komai ba dan ta bata haushi sosai da ta wani ce tana kishi,to dadin mai lasa wuta?ko tana kishin kowa ai ba zata yi na Najeeb ba dan ta hanga ta hanga ita bata ga abunda za ta yi ma kishi ba, wanda zata yi ma kishin yana nan dai zuwa soon amman ba dai Najeeb ba, kashe datar kawai tayi tana kwanciyarta duk da ba bacci take ji ba,amman ta gwanmace ta sauka da ta tsaya online Zubaida ta tura mata kayan takaici da bakin ciki ba dalili ta sayar ma kanta b'acin rai da kudinta .

★★

*GUSAU 🥀*

Kallonsu Baba yayi yana cewa.."komai ya wuce Allah ya yafe mana baki d'aya,Allah kuma ya k'ara shirya mana zuri'a ya karesu da karewarshi,amman Kakata kinyi kuskure kuma kin kunya tani a idon duniya komai dai ya wuce ba amfanin a maido da hannun agogo baya,kuma Alhamdullahi abun dadi tun da shi Abdulkadir yace yana sonki da aure a shirye nike da na aura mashi ke."

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now