ZAZZAFAR KAUNA 91-100

Start from the beginning
                                    

"Ni ban gane nan ba Dejarh karda Uncle Bash ya dawo yayi man fad'a,yi man kinji please." Waro Ido Dejarh tayi tana cewa."kin manta yana gane note dina da naki kina son nayi yayi bulala  ko.?"

Girgiza kai Nana tayi tana cewa..okay yi man spelling sai na dunga rubutawa please." D'aga Kai tayi tana gaya mata tana rubutawa gwanin burgewa,suna cikin homework Mama ta fito tana sauri tace.

"Bayin Allah kuyi hakuri na barku zauna da yake kun tada na kusa karasa girkin ne shiyasa ga yaran nan ba wayau ne dasu ba..ba komai suka iya ba balle na bar masu." Ko kadan Mama bata lura da Jidda ba da yake tayi k'asa da kanta tana kukan zuci tun da Mama ta fito.

Ajiye masu ruwa Mama tayi tana murmushi dai dan bata gane Ammie ba,karfin hali kawai tayi tana ajiye mata ruwan da ta fito dashi daga kitchen,amman ita dai sai taji gabanta yana faduwa balle duniyar nan da tazo karshe babu amana da yarda a cikinta.

Mama na kokarin yin magana Baba ya banko kofa ya shigo ko sallama babu haka ya tsaya a gaban Ammie yana mata wani kallo can ya nuna mata kofa cikin fushi yace..."Maza ku tashi ku bar man gida,karda na sake ganinku a cikin gidana har abada idan kuma ta kuskuren sake shigo man gida wallahi wallahi sai nayi mata abunda har ta mutu ba zata tab'a mantawa da ni ba."

Kuka Jidda ta rushe da shi tana d'ago kanta,da sauri Mama taja baya tana innalillahi wa'innalaihirajiun can kuma ta durkushe a wajen tana rushewa da wani irin kuka...wata irin tsawa Baba ya buga masu yana nuna mata kofa yana cewa.."Zaki fita ko sai na tsine maki albarka." Tashi Ammie tayi tana cewa .."Haba Kai ko Alhaji Abdullahi abi komai a sannu komai sai yazo da sauki amman fushi da tsunuwa ba naka bane,ai nasa farinciki zakayi da godema Allah dawowar ta gareku ba tsinuwa ba."

D'aga mata hannu Baba yayi yana cewa.."Baiwar Allah cikin girma da arziki tin ban Kai bango ba ku fitar man daga gida, Jiddarh dai ce ko?tuni na sallama ma duniya ita na barta da duniyar da ta zab'a,dan ni tuni na fiddata daga cikin 'ya'yana dan haka karki sake dangantani da ita."

Kuka ta fashe dashi tana cewa.  "A'a Baba karda kayi man haka,kayi hakuri ka tsaya ka saurari uzirina  wallahi Baba ba zan sake ba dan Allah Baba karda kayi man haka."Tsaki Baba yayi yana shiga wani daki,da belt ya fito a hannunshi yayo kan Jiddarh ya fara zabga mata a jiki,ganin yanda yake bugunta kamar ba shi bane ya haifeta yasa Mama ta shiga tsakaninsu tana bankade Baba tana kare Jidda tayi mata rumfa tana cewa.

"Kashe ta zaka yi Abdullahi.?"

Kuka Mama ta fashe da shi tana cewa.."wallahi ba zan zuba maka ido ba ina kallo ka kashe man ita ba." Nunata da yatsa Baba yayi cikin fushi yana cewa.."Aisha maza ki ban waje." Banza Mama tayi mashi tana Kara shigar da Jidda jikinta tana kuka Jidda na kuka haka ma Ammie,ida shigowa su Dad sukayi saboda izinin shigowa da Bash yayi masu,da sun ki shigowa tunda Baba yace karda su shigo mashi gida,amman Yaya Bash yace su dai shigo ai shi yace su shigo karda su damu da duk furicin da Baba yayi masu yana cikin fushi ne shiyasa.

Wani kallo Baba yayi mata yana cewa.."magana fa nike maki Aisha,ni nan Abdullahi nace ki matsa ki ban waje na koya man wanann yarinyar hankali."

Kin matsawa Mama tayi sai ma cewa da tayi.."babu inda zani matsa wallahi sai da ka koya mana hankalin tare,amman ka sani ba zan matsa ko nan da nan ba,haba mana bawan Allah Kai da zaka yi murna dawowarta gida ka gode ma Allah da maido mana da hankalinta har ya karkarto ya dawo gida,hannunka baya tab'a rubewa ka yanke."

Tsaki Baba yayi yana lallata masu belt su dukansu ya had'e yaita zabga masu ganin abun ba mai karewa bane Bash da Muhd suka shiga suna kallon Baba cikin takaici da b'acin rai da Kuma zuciya da ta kawo Yaya Bash wuya ya kalli Baba yana cewa.

"Bugun ya isa haka Baba,ka sani wannan abun da kake ba hanya ce ka dauko wanda zata bulle da Kai ba,gaya man dadin da kakeji kana dukan mahaifiyarmu a gaban idonmu a gaban bakuwar fuska.?"

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now