Ga kuma drive  da ta mai dashi dan wulakanci da rashin kunya daman yace ba zai ce ta dawo gaba ba,dan bata Kai wanann matsayin ba da zai tsaya yana gaya mata wai ta dawo gaba,kenan ya damu da ita kuma ya damu da mai dashi drive da tayi.

Yanzun gashi da kanta ta dawo gaba ba dan Allah ba,ganin yanda yake sharara gudu da ita ga wata daff da yazo yin overtaking zai wuce bata san lokacin da ta rushe da kuka ba tana cewa.

"Dan Allah kayi hakuri Sir,kar da ka kashe ni wallahi ban shirya mutuwa yanzun ba."

Cikin kuka tayi maganar a gigice tayi mashi maganar tana hade hannunta waje d'aya,shi dariya ma ta bashi sai dai bai yarda ko murmusawa yayi ba balle har yayi dariyar duk da ta bashi dariya to the extent,wai bata shirya mutuwa ba daman ita mutuwa sai an shirya mata take zuwa kenan?tabbas yarinyar nan ya k'ara yarda har yanzun da sauranta.

Yarinta da rashin hankali suna dawainiya da ita,daman matsalar auren yarinya kenan sai kayi hakuri ka Kai zuciya nisa dan ka dunga ganin shirme da hauka kenan iri iri.

Ko kallonta baiyi ba balle ya nuna yaji tana wani abu wai shi magana,kuma bai fasa kokarin ganin ya Kai inda yake son zuwa kafin 9am tayi dan komai ya faru ai itace sila itace ta b'ata masu lokaci bayan sai da yaje har bakin kofar room ya gaya mata ta shirya da wuri karda ta tab'a mashi lokaci amman duk a banza a wofi dan fadin baiyi amfani ba.

Tunda har fad'a mata tayi sauri ta shirya akan lokaci baiyi amfani ba ,ko kuma yace bata ji ba saboda kunnenta na k'ashi ne to shima ba zaiji magiyarta ba kuma bai saurareta ba Koda kuwa zatayi kukan jini bana hawaye ba.

Kuka take bill haki da gaskiya tana bashi hakuri iyakar kokarinta ,ganin bai da niyar rage gudun ta kalle shi tace..."Sir dan Allah ka saukeni anan zan samu taxi ta karasa dani." Yanda tayi mashi maganar ne a laddace da kwantar murya ya bashi mamaki.wato da yake taga mutuwa shiyasa take mashi biyaiya kamar ba itace bace take mashi duk rashin kunyar da ta gadama ba tsaki kawai yaja yana mamakin halin mata.

Su dai mata komai nasu daban yake ba komai suke dan Allah ba komai sai sunyi mashi riya da yaudara wai shi Zulaihat take ma magana cikin sanyi da natsuwa ta koma mashi Zulaihat din da ya sani a baya ba ta yanzun ba,ta koma wata so silent  har wani sinne kai take tana kukan da ta rabu da yin shi girgiza kai kawai yayi yana mai shan wata kwana tafiya kadan yayi ya iso bakin gate din school din.

Dai dai inda aka tana dar mashi dan ajiye motarshi yayi parking yana duba time,tara saura minti biyar yana da 10mn dan yana bad'a 5mn daman kafin ya shiga lecture venue daman shi haka yake ko kallonta bai yi ba ya had'a laptop din shi da wayoyinshi ya bude ya fito.

Ta godema Allah yafi sau ba adadi da taga sun iso lafiya zufa kam ta tasha ta har ta gode Allah ga ciwon kai da take ji sama sama,sauke ajiyar zuciya tayi tana goge fuskarta bag dinta ta dauka tana fitowa.

Had'a ido sukayi ta turo mashi baki tana magana k'asa k'asa ta kama gabanta tana Allah ya saka mata kusan kasheta da yayi daman can ba sonta yake ba shiyasa yaso ya kashe ta Allah yayi saving dinta.

Murmushi yayi yana bin ta da kallo komai nata burgeshi yake,wata sa'ar rashin kunyarta na bashi dariya kuma tana mata kyau, k'asa motsi yayi yana kallonta yana jin yanda sonta da kaunarta suke zagaye duka alhahirin jikinshi .

Tafiya take cikin natsuwa kamar ba ita bace ta murgada mashi baki ba,ganin lokaci na tafiya ya nufi office dan idan har ya biye ma zuciyarshi to zai iya kwana nan tsaye yana kallonta bai gaji ba.

Bayan ya shiga office wayoyinshi kawai ya ajiye yana dauko projected din a zaiyi using da ita a wajen lecture din ya dauko hanya...kamar yanda ya saba haka ya shigo fuskarnan tamau babu fara'a ko kadan a samanta.

Kallo d'aya zaka yi mashi kaji shaskarshi da tsoronshi ya shigeka dan wannan shine haduwarshi da ta farko dasu duba da shi sabon malamine a makarantar ,amman yanda ya shigo masu yasa kowa ya kama kanshi yasha jinin jikinshi.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)जहाँ कहानियाँ रहती हैं। अभी खोजें