ZAZZAFAR KAUNA 61-70

ابدأ من البداية
                                    

Da yake daman Najeeb ba daga baya ba wajen iya girki duba da zaman da yayi kano da kuma zaman da yayi a London duk shi yake masu girki shi da Moha a haka har shima Moha din ya kowa..da fari Moha bai biye mashi dan zuwa yake eatry yana samo abunda zai ce shi kuma Najeeb yana da kankami ba ko Ina yake iya cin abinci ba duk kyaun eatry kuwa ya gwanmace ya girka da kanshi.

Bayan ya gama cika cikin shi ya kwashe kayan da yayi using dasu ya shigar da su kitchen ya wanke sannan ya fito ya kalli labari wajen karfe goma na dare ya kashe kallon ya shigewarshi room din shi ,ba bacci ya kwanta ba dan baya jin bacci dauko laptop din shi yayi ya fara research yana research yana shan lemu...Dan yanzun duk wani kunci da takaicin da Zulaihat ta kunsa mashi ya nemai shi ya rasa yanzun zuciyarshi sawai take babu dacin komai a cikinta.

★★

*JIGAWA 🥀*

Weaving din hannunta tayi a saman fuskarshi tana dan hura mashi iskan bakinta tace.."Hi Beb." Firgigi haka ya kalleta yana lumshe Ido,fuskarshi dauke da murmushi yana kama hannunta yana murzawa a hankali ya kuma lumshe idonshi bai ce mata komai ba.

Durkusawa tayi a kasa tana cewa a hankali.

"Beb."

Again dagowa yayi yana kallonta can kuma ya bude baki a hankali yace.

"Na'am Partner hope kin tashi lafiya.?"

Turo baki tayi tana cewa.

"Uhmm nidai Ina ta missing din ka duk fa jiya ban saka a iso ba sai da kazo man a dreams dina kuma ko."

Ta ida maganar tana turo baki a cikin shagwaba kama bakin yayin yana cewa.
"Partner kin san mai.?"
Girgiza kai tayi tana cewa..."A'a."  Murmushi yayi yana sakin bakin a hankali.."Ina tausayin randa bakin nan zai shigo hannuna dan sai na fanshe duk kwalelen da yake man." Sake turo bakin tayi tana cewa.."wayyo Allah Beb nidai gsky Beb a'a." Murmushi kawai yayi yana shafa gefen sajen shi can kuma ya ce.."Nima kina a raina Partner kin san yana yin aiki,abunka da tallaka ammam kina a raina kema kin sani lokacin da dawo har kin kwanta."

Jan hancin shi tayi tana cewa.."Amman aikin jiya yafi na kulle yawa ko.?" D'aga mata kai yayi yana cewa."kinsan Lagos naje motocina aka sauke a shekaran jiya sai costume suka zo su bani matsala haka kawai da mun fara maganar ta waya sai kawai naje na nuna masu takardu sannan suka sakar motocin kusan mota sama da 3k suka so su rike fa."

Zaro ido tayi tana cewa.

"Sama 3k." Murmushi yayi yana jan hancinta yace..."aikuwa duka kudina na kwashe nayi order din su kin san ai motoci nike saidawa."

"Hakane Allah ya Kara tsarewa Beb."

"Amin ya Allah."

Mika mashi wayarta tayi tana murmushi ansa yayi yana kallonta sai kuma yace.."Masha Allah Partner su waye wa'annan din." Ansar wayar tayi tana Kara kallon picture din tana cewa .

"My twins."

Kara anshe wayar yayi yana kare ma yaran kallon,yarane kyawkyawa Masha Allah farare tas kamar ba yan kasar nigeria ba ga gashi har saman baya, kallonta yayi yana kallon picture din sai kuma ya saki murmushi yana jin son yaran har cikin zuciyarshi da kuma tausayinsu da ya tuna waye ubansu kuma ba ta hanyar aure aka haife su ba ga dai kyau iya kyau amman basuyi dacen uba na gari ba.

"Partner Ina son su sosai,Allah yasa idan munje Gusau Mama ta bani su na dawo dasu Jigawa and Ina kika samu picture din su?ko daman can kina da su?kuma ai naga nan da girmamsu dan zasu Kai 7yrs kuma suna da 2yrs kika bar su."

Murmushi tayi tana cewa.."Nima yau na samu picture din ." "When?" yace mata, murmushi tayi tana cewa.."IG" kallon karin bayani yake mata cigaba da ce mashi tayi.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)حيث تعيش القصص. اكتشف الآن