ZAZZAFAR KAUNA 61-70

Start from the beginning
                                    

"Nidai iyakar gaskiya ta na fad'a ynzun dai sai monday ai zasuyi resume ko.?"

"Eh."

Yace a dakule dan har maganar ta fice mashi rai yaga Moha yana son ya nuna mashi bai san maiye so ba ko kuma yana son nuna mashi bai kishin matar shi?wani tsaki ya kuma ja yace ma Moha.

"Kowa ya ringa Kai matar shi idan sun je school sun hadu okay."daga kai Moha yayi yana cewa.."yanzun naji batu." Kashe wayar sukayi yana jan tsaki dan yaji haushin abunda Moha yayi mashi wani tsaki ya dauka yana tashi ya had'a wayoyinshi ya bar gidan.

Duk yinin yau bata fito waje ba tana cikin daki ta Kunshe kanta dan har yanzun boobs dinta basu bar yi mata zafi ba ,dan ba karamar matsa Najeeb yayi masu ba..tsaki tayi tana cewa.."Allah ya saka man nidai ba yafe ba." Agogo ta duba taga har karfe biyu na rana ya wuce,wanka ta Kara yi ta shirya cikin wasu riga da saket na atamfa ta gyara gashinta ta fito parlon

Kofar dakin shi ta wulla ma harara tana jan tsaki sannan ta wuce kitchen taliya ta girka jallof da ta zuba mata yan kan ku hanta sai tayi zobo mai yawan gaske ruwa ta dauka har create ukku ta Kai room dinta ta ajiye da su lemu sai zobo duk ta saka a freeze.

Zama tayi ta ci taliyar ta koshi ta bar plate din da tayi using da shi a parlo ko daukewa bata yi ba...ranta bata yi ba yanzun zai dawo ba dan haka ta zauna ta fara hadin donuts da cake sai cin-cin ,tana aikin tana duba lokaci dan bata bukatar ganin shi bata son ganin shi bata bukatar hakan.

Da ace akwai yanda zatayi da tayi ta bar ganin shi har abada,da akwai yanda zatayi da tayi ta raba wannan qaddarairen auren bata son auren bata son shi da ace Umma zata yi mata adalci da tayi mata magana tasa Najeeb ya tsinke igiyar wannan auren dan ita dai ba abun da auren nan zai tsinana masu daga ita har Najeeb ba.

Bata jin son shi ko kadan a zuciyarta bata jin komai a kan shi,sai ma tsantsar tsanar shi da take k'ara maimaye mata zuciya ba dare ba rana...takan rasa dalilin da yasa bata jin shi a zuciyarta tabbas tasan Najeeb mutune mai kyau ga kuma kudi ga kuma ilimin ga k'ira dan Najeeb ingarman namiji ne yana da tsawo da fadanden kirji ga kuma kwarjini da haiba.

Tsaki tayi tana cewa

"Matsalarka baka da kirki baka da tausayi kuma baka jin komai ka d'aga hannu ka bugi mace ,Kai hawayen mace basu karya maka zuciya sai ma Kara hawa da ita da suke."

Tsaki tayi tana mai cigaba da soya cin-cin din ta tace.."wanann halayen naka na rashin tausayi yasa naji bani sonka ban son ka kasance uban y'ay'ana,bamu dace da juna ba Najeeb bamu dace ba ko kadan,maiyasa idonka ya rufe baka hango rashin dacewar mu ba? maiyasa baka je ka nemo dai dai ka ba wanda ta dace kai,nima ka barni na auri dai dai ni wanda ya dace ni."

Haka ta kama masifa tana aikinta bata samu ta gama snacks din ba sai gab da mangariba,samun manyan bokitai tayi ta zuba donut din da cin cin har da cakes din ma da yake cupcakes ne tayi shiyasa.

Gyara kitchen din tayi tana fitowa da boket din ta kai daki tana kullewa tubewa tayi tana shigewa toilet ta tara ruwan zafi ta Kara gasa jikinta sannan ta fito tayi sallah zama tayi tana azkar har aka kira isha'i ta tashi tayi sallar sanann tashi ta nade sallayar sannan ta zauna saman stool ta shafe jikinta da creams masu kyau da kamshi wanda suke Kara ma jikinta kyau da glowing ,humra kawai ta murza tana hayewa saman gado ta dauko wayarta tana chating da Umma tana cin Donut din ta hankali kwance.

Bayan ya dawo daga wajen aiki ya shigo gida tsaye yayi yana kallon plate din da taci abinci ta bar shi yashe a parlo, tsaki yaja yana ida shigewa room dan ya kwaso gajiya sosai da sosai ga kuma wani Karin girma yau da ya shiga school din ya tadda anyi mashi dan dean of faculty aka bashi ba tare da yasan ma za'a bashi ba.

Da fari ya fara gardamar ansa amman ana ki bashi goyan baya dan duka staff din na faculty din kowa yana Na'am da bashi dean din dan ba ya iya ya ansa shiyasa bai dawo da wuri ba ga kuma ciwon kai...yana fitowa wanka ya fito ya dauke plate din ya maida kitchen yana daura indomie ya girka da kanshi har da markade Apple yayi Apple juice yasa wani freeze ya zuba wanda zai sha.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now