ZAZZAFAR KAUNA 41-50

Start from the beginning
                                    

"Kadan ka gani wallahi nice maganinka."

Bin ta yayi da Ido kawai yana murmushi ya ma rasa ya zaiyi mai zai mata?yarinyar tasha da shi ta sammace shi taji sirrin da ke cikin zuciyarshi...dafa kanshi yayi jin ya dan fara yi mashi ciwo saboda kukan da sharbe kamar wani wawa,sai yanzun yake jin haushin kan shi Ina hankalinshi da tunanin shi ya tafi da bai gane da rainta ba?shafa gemunshi yayi yana Kara sakin murmushi again sai ya tashi dan shiga yayi wanka ya samu ya sha magani saboda ciwon da kanshi yake mashi.

*Jigawa-Dutse🥀*

fitowa tayi babban parlon gidan tana kare mashi kallo,har tsoro da mamakin haduwar gidan yake bata shin anya kuwa mutane sun san ciwon kashe kudi kuwa?tambayar da tayi ma kanta kenan tana mai k'arema manya manyan royals din da ke a mamake  parlon kallon komai na parlon da ruwan gold aka yi mashi ado.

wannan wata irin dukiya ce aka kashe ma gidan nan tana al'ajabin kyaun da gidansu na kano yayi mata ashe bata ga komai ba,Ashe kango ne akan wanann gidan na dutse hango tsaruwar gidan su na Ukraine tayi sai taga ko half din wannan bai Kai ba, gida ne idan ba gani kayi da idonka ba to ba zaka ce a nigeria yake ba.

furzar da iskan bakinta tayi tana samun waje ta zauna tana kallon wata Yar dattuwa da ta fito hannunta rike da jugs har biyu ga dukan alamu daga cikin kitchen ta fito zata je dinning.

Dan durkusawa tayi tana cewa.."barka da hutawa Hajia." d'aga Kai Beauter tayi tana cewa.."yauwa barka dai Ba'a fatan kina lafiya." murmushi tsohuwar tayi tana cewa ."Alhamdullahi." murmushi Beauter tayi tana cewa.."Hajiya fah.?" kitchen ta nuna mata tana cewa. "tana cikin kitchen."

Tashi tayi tana nufar kitchen din tsaye ta tadda Ammie tana Kara gyara kitchen din saboda basu dade da gama sauwa ba ,kuma bata son ta tafi ta bar Bab'a da aiki dan aikin zai yi mata yawa ga gyaran kitchen ga kuma wanke-wanke ai aikin yawa zai yi mata ga kuma jiki na tsufa.

Tana shiga ta anshi abun wanke wanken hannun Ammie tana cewa.."Sannu da aiki Ammie." murmushi Ammie tayi tana cewa.."Yauwa Daughter ya gajiyar tafiya.?" murmushi tayi tana mai cigaba da wanke wanken ta tace.."Gajiya tabi jiki Ammie ashe akwai nisa sosai tsakanin kano da jigawa.?"

"Eh da nisa sosai gaskiya amman wasu sun ce babu nisa wai."

Dariya tayi tana kama baki tace.."wai Allah Ammie, wallahi Ammie akwai nisa kamar nayi kuka fa haka na kama ji nidai naga nisan tafiyar."

"Ai daman haka zaki gani tun da baki tab'a bin hanyar ba dole tayi maki nisa gaskiya kam."

Cigaba da hirarsu sukayi har suka gama gyara ko Ina suka dawo parlo,tare suka jona kayan kamshi a babban parlon kamo hannunta Ammie tayi hawaye na zuba a fuskatarta tace.

"Allah yayi maki albarka Jiddah,ban tab'a kawo wa a raina nan kusa zan samu kawar da zata tayi ni gyaran parlon ba balle azo kitchen."

Dan shuru Ammie tayi sai kuma ta cigaba da cewa.

"Allah sarki!ya Allah ka jikan Hafsat."

d'agowa Beauter tayi tana goge ma Ammie hawayenta tana cewa.."Ammie wacece Hafsat kuma.?"

murmushi Ammie tayi tana cewa.."Hafsat kanwar Myson ce wanda akan ta ban sake haihuwa ba saboda cire man mahaifa da akayi,ta dalilin ciwon cancer da ya kama man mahaifa."

"Allah sarki,Allah ya jikanta da rahama,amman Ammie tana da shekara nawa ta bar duniya.?"

"shekara goma."

"Allah sarki Hafsat ,Allah ya jikanta Ammie."

"Amin Daughter shiga ciki kiyi wanka kafin a kira sallah karda mangariba tayi maki a bayi."

Tafiya tayi tayo wanka bata fito parlo ba sai da tayi har sallar isha'i sannan ta fito zama tayi suna ta labari da Ammie bai shigo gida ba sai wajen nine...yana shigowa ya zauna kasa yana daura kan shi a saman kafar Ammie ya furzar da iska yace.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now