ZAZZAFAR KAUNA 21-30

Start from the beginning
                                    

Tunda ta kwanta bata san inda take ba baccin gajiya kawai take dan bata san Ammie  ta shigo ba balle kuma yaji addu'ar da tayi mata da fitar ta,can wajen karfe ukkun dare yunwar cikinta ta tadata tashi tayi tana murza ido, dump lamp din gefen gadon ta kunne tana maida hular baccinta ta sauko saman gadon tana bissimllah,direct toilet ta shiga ta wanko fuskarta ta dauraye bakinta ta fito tana neman wayarta duba time tayi taga ukku har da rabi ,mamakin baccin da tayi take sai kuma ta kwabe baki tana nufar hanya dan sama ma cikinta abinci dan wata irin yunwa take addaba mata a ciki.

Koda ta fito direct dinning ta nufa tana bude warmers din da suke a dinning din, jallof cous-cous ne da yaji kayan lambu da kuma tsokar nama sai da miyaunta ya tsinke dan couscous din yayi mata kyau sosai,kuma baiyi sanyi ba da yake ba a karamar kula aka zuba couscous din ba , kula ce wanda zata kai duba dari biyar ko ma sama da haka.

Sosai ta zuba couscous din ta zauna taci ta koshi sai da taji har ba waje a cikinta sannan ta ture plate din tana tsiyaya ruwa a glass cup mai kyau da daukar ido ta sha sai kuma ta tsiyaya pineapple juice mai sanyi tasha tana lumshe ido,sai da ta sauke ajiyar zuciya tana jin wata natsuwa na saukar mata a ko wane lungu na jikinta.

Kwashe kayan tayi ta maidasu a kitchen sanann ta dauko bottle daya na ruwa ta nufi room dinta dashi dai dai zata shiga room dinta ta sauke idonta a kanshi, murmushi tayi tana weaving din shi shima weaving dinta yayi yana cewa.

"Hope kin tabbata kin koshi sosai.?" D'aga mashi kai tayi tana cewa.."Yeah." Huro mata kiss yayi yana bude kofar room dinshi ya shige lumshe ido kawai tayi itama tana ida shiga nata room din...Koda ta shiga ajiye ruwan tayi a saman lakar gado sanann ta shiga toilet tayi alwallah ta fara sallah,ganin har hudu da minti ashirin tayi asuba tana gabatowa..kuma yanzun har ta saba da yin sallar dare saboda tunda ta dawo da kwana a gidan su AK take tashi sallar dare saboda yan gidan sun saba da tashi har tashin ya zaman mashi jiki.

Bata koma bacci ba sai wajen karfe shidda na safe sai da ta gama har azkar sannan ta koma bacci ,ta dade bata tashi ba dan sai wajen 1 na rana ta tashi tana tashi wanka tayi da alwallah wata doguwar rigar ta atamfa ta saka ta daura hijab tayi sallar azahar...tana gama sallar ta zauna saman stool tayi shafa ta daura dan kwali sannan ta fashe turare ta fito,zaune ta tadda Ammie a babban parlon tana magana da wata mata Koda ta karaso a parlon zaunawa tayi kusa da Ammie tana daura kanta a saman kafadarta tace.

"Gud Afternoon Ammie."

Shafa kanta tayi tana cewa.."Afternoon Too Jiddah,fatan kina lafiya." D'aga mata kai kawai tana Kallon matar da ke gaidata tayi murmushi tace.."Ina wuni ya gida." K'asa matar tayi da kanta tana cewa.."lafiya lau Hajiya ya kuma gajiyar tafiya.?" Alhamdullahi tabi jiki." Cewar Beauter tana komawa dayan parlon ta kunna kallo ta basu waje su ida maganar su duk ta lura kamar matar gateman din gidan ne Ammie take magana da ita.

★★

*ABUJA🥀*

Kallon Zubaida tayi tana murmushi tace.."Sis maiye sirrin?Kinga yanda kika koma kuwa?daga yin aure ko sati biyu ba'ayi ba." Murmushi Zubaida tayi tana kama hannun Zulaihat suka shiga room dinta da ita sai da suka zauna ta kulle kofar room din ta kalli Zulaihat tace.

"Sis."

D'agowa Zulaihat tayi tana murmushi tace.."Na'am gaya man sirrin dan Allah wallahi baki ga yanda kika yi kyau ba kikayi fresh kin zama wata Hajiya."

Murmushi Zubaida tayi tana cewa.."kwanciyar hankali da kuma samun miji na gari ga soyyyar da yake nuna man ba dare ba rana." Dan shuru tayi tana kallon Zulaihat itama ta chanza ta Kara haske da kuma kyau sai daukar Ido take amman batayi wata kiba ba tana yanda take bata rame ba kuma batayi kiba ba,amman tayi haske sai glowing fuskarta take  dan tunda akayi aurensu basu hadu ba sai yau,yau din ma Zulaihat din ce tazo da kanta ita ba yanda batayi da Moha ba ya barta  taje sai yace a'a ta barshi karda taje ta takura masu suna cikin amarci,yanke shurun Zulaihat tayi tana cewa.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Where stories live. Discover now