ZAZZAFAR KAUNA 11_20

Comenzar desde el principio
                                    

Murmushi yayi yana kamo hannunta yayi kissing din hannun a hankali yana Kiran sunanta yace.."Jiddah." D'agowa tayi tana kallon shi tace."Na'am." Furzar da iskan bakinshi yayi yana cewa.."Tabbas inasonki kuma Ina kaunarki Jiddarh ki nike son ki zama abokiyar rayuwata har *DA'IMAN ABADAN*  kuma Ina murnar komawarki a wajen mahaifinki amman kuma ina jin tsoro a wani bangaren."

Dai dai bakin salon din da za'ayi mata gyaran gashi ta parka motarshi tana waigowa ta kalle shi tace.."tsoron mai kake ji.?" Langwabar da Kai yayi yana cewa.."Ina tsoron karda iyayenki su hanani ke Jiddah ko kuma karda ke kice ba zaki aureni ba cousin Broth dinki zaki aura." Dan shuru yayi sai kuma ya cigaba da cewa.."ni kuma Jiddarh zan iya mutuwa idan na rasaki, qaddarata shine sonki da Allah ya jarabeni da shi wallahi Jiddarh ban tab'a fadawa a tarkon son ko wace y'a mace a rayuwata sai a kanki and Jiddah wallahi ban san maiye so ba kuma ban san maiye zafin so ba sai a kanki Jiddah ki taimakeni karda ki gujeni ki so ni ki aureni ki rayu dani har *ABADAN*"

Shuru tayi tana kallonshi take idanuwanta suka sauya kala daga shinning din milk suka fara komawa ja,tabbas ya tuno mata da Yaya Auwal ya tuno mata da irin soyayyar da Yaya Auwal ya nuna mata kamar zaiyi hauka amman idonta ya kulle taki ta soshi duk da yanda kowa nata yaso ta soshi amman ita ta kasa, ta kama Kara da kiyashi daukar marar sani,bayan iyayenta to bata ga mai sonta kamar AK ba dan son da yake mata na gaskiya ne ba na karya ba ,ba kuma dan wani abu nata yake sonta ba,dan bata da abun da zai sota kyau ya fita haka kudi haka komai na rayuwa balle ma da ya ganta a gantale a titi amman ya ji ya gani ya dauka taya zata juya mashi baya kenan zata kasance butulu marar cika alkwari.

Furzar da iskan bakinta kawai tayi tana shafa gefen fuskarshi tace..."Beb zanfa dad'e zaka iya jira.?"D'aga mata kai yayi yana cewa.."zan iya jiranki partner Koda kuwa shekara zakiyi a ciki." Kumatunshi kawai taja tana bude marfin mota zata fita, dan rikota yayi yana bata ATM card din shi, kallonshi tayi tana cewa.."akwai kudi a hannuna kuma itama Ammie ta bani ATM  card dinta yana a cikin bag."

D'aga mata kai yayi yana cewa.."I know,nasan kina da kudi amman da nawa kudin nike bukata ayi using." Har ta bude baki zatayi magana ya daura hannunshi a saman bakinshi yana gaya mata pin din murmushi kawai tayi tana ficewa daga motar tana shiga ciki.

Tana shiga ta samu waje ta zauna gaisawa tayi da mutanen wajen da yake an saba da ita a wajen dan duk gyaran da ake yi ma gashin Beauter a wajen take yin shi ,bayan layi yazo kanta aka fara yi mata sosai aka wanke kan aka gyara aka yi ma gashin style mai kyau da daukar hankali bayan angama aka gyara mata farcenta sukayi gwanin birgewa da daukar hankali.

Yanda ta barshi a cikin mota haka ta tadda shi dan ya dan jingina kanshi a jikin kujara yana bin suratul lukuman baiji isowarta ba sai dai kamshinta da ya bugar mashi hanci,bude idon yayi a hankali yana saukewa a samanta ya sakar mata murmushi maida mashi da martani tayi tana shiga.

Key tayi ma motar suka dauki hanya sai ya dan kalleta yana cewa.."sannu Partner fatan ba'a gajiyar man dake ba sosai." Hurar da iskan bakinta tayi tana cewa.."Yauwa tam ba laifi Beb,amman yau na dan ji zafin gyaran gashi ba laifi."

"Ayya Partner sannu dan biya damu St mu dan huta ko.?" Kallonshi tayi sai kuma tace.."kace zaka tuno baya?wai mai ya kaika St-sophia's cathedral Beb.?" Murmushi yayi yana sosa gefen gemunshi sai kuma ya kalleta yace.."ke mai kika anso a cikin bakar leda a St-S.?" Furzar da iskan bakinta tayi tana cewa.."Oh God Beb,ya haka da yin tambaya bayan baka bani ansar tawa tambayar ba.?"

Ido d'aya ya kashe mata yana cewa.."Uhm!kuma ina jiran ansar ba." Dariya tayi tana Kara ba motar wuta ba inda tayi ma tsinke sai a St-sophia parka motar tayi tana kure babban wajen shakatawar da kallo abubuwa da suka faru da ita mai dadi a wajen yana dawowa mata a lokacin da take jin tafi kowa ba ta biyunta,idan ta shigo a St-S ko wace yar'iska maiji da kyaunta da gashinta da kuma karuwarcinta sai ta sara mata ta bar mata fili.

DA'IMAN ABADAN (ZAZZAFAR KAUNA)Donde viven las historias. Descúbrelo ahora