Jikin sa sai yayi sanyi ya sauke numfashi yace, "to in kun shirya zan saka a kai ku a mota sabida k'afar tata kafin kuje ku saka a gyara mata inda zata zauna, zan baku magungunan da zata dinga sha da abubuwan da ya kamata ta cigaba da ci in sun k'are a kuma siya. Kuyi hak'uri dan Allah na rasa yadda zanyi ne."
"Haba likita meye na bada hak'uri? Ai kayi k'ok'ari ko kaine ka buge ta ai sai haka."

Rauda ta tab'e baki tace, "Daman su y'ay'an masu kud'in nan babu abinda suka sani sai kansu, yanzu inda girmamawa ai yaci ace wani nasa yazo ya cigaba da d'aukar nauyi na tunda sune silar komai. Tunda bashi da lafiya an bar maganar daman ba gata ne dani ba sun yiwa banza. Allah wadaran wasu masu kud'in" Rauda ta fad'a a fusace.

Dr yace, "Wallahi Hydar bashi da wannan halin baki ga yadda ya tsaya akan ki ba rashin lafiya ce dashi in ta tashi sai ya kwashe sati uku a sume bai farfad'o ba, yanzu zancen da nake miki tun da yazo nan ciwon ya same sa bai tashi ba har yanzu."

Umma tace, "kai ka biye mata ai likita ai ko iya haka aka tsaya yayi k'ok'ari sosai, wanda in sun buge ka suke guduwa fa su kuma ace musu me?."
"Umma maganar da ta fad'a gaskiya ce ya kamata ace wani nasa ya tsaya, amma da zaku san waye shi ku kuma san abubuwan da suke faruwa da ku kan ku kun tausaya masa shida y'an uwan nasa."
"Allah ya kyauta" Umma ta fad'a.

A wannan lokacin aka had'a magungunan Rauda da komai nasu aka saka Rauda a ambulance Umma ma ta shiga aka wuce da ita gida. Kafin suje Inna ta gyara d'akin Umma an yiwa Rauda shinfid'a aka shigo da ita a akan gadon aka zaunar da ita aka basu maganin ta suka koma.

        Umma ta cire mayafi ta ajjiye  tace, "Daman na gaji da zaman asibitin nan, zaman asibiti sai dole." Rauda tayi shiru bata ce komai ba haka kawai take jin haushin wanda ya kad'e ta a ganin ta bai d'auki lafiyar ta da mahimmaci ba tunda ita talaka ce.
Ummulkhairi da Khalil sai dawowa sukayi suka ga su Umma a gida suka dinga murya Umma ta dawo.

      K'arfe biyu na rana Baba ya diro gidan ganin k'ofar Umma a bud'e ya saka shi ya lek'a ya gansu a zaune Rauda tace, "Baba sannu da dawowa." Kallon su yake da mamaki kafin yace, "Me kuma ya dawo daku?." Umma tace, "Kud'in wanda ya kad'e tane ya k'are a asibitin kuma bashi da lafiya shiyasa aka dawo damu gida." Baba yaja dogon tsaki yace, "Kai amma ban so hakan ta faru ba, yanzu shikenan bazan kuma ganin sa ya bani wani abun ba? Abin takaici wallahi."

      Rauda tabi mahaifin nata da kallo da mamaki kafin ta d'auke kanta Allah ya sani abinda yake yi yana bata takaici kawai dan babu yadda zatayi ne uba uba ne. Juyawa yayi ya fita yana fad'in, "To Rahma a fito." Ba musu Rahma ta fito da hijjabi ya nuna mata kular yace, "gashi nan na dubu uku ne ayi aje a dawo." Da to ta amsa ta d'auki kular ta fita ranta a b'ace.

Inna ta fito daga d'akin ta ta kalle shi tace, "Tsakani da Allah malam nima da nake goya maka baya na gaji da wannan tallan da kake d'orawa yaran nan, ka duba halin da Rauda take ciki ta dalilin talla ni na d'auka zaka saduda sabida hakan amma ko gezau bakai ba."

     Kama k'ugu yayi yace, "To uwata kama kunne na zakiyi ki fad'i maganar nafi fahimtar ki sosai." Inna ta d'auke kanta gefe yace, "in ban d'ora musu tallan ba a gida kike so su zauna naita kallon su su ba aure ba ba kuma samari ba?, meye amfanin su in basu yi tallan ba?."
"Abinda kake sakawa suna yi ba shine zai kawo musu miji ba, aure kuma ai lokaci ne in yazo kamar ba'a zauna ba."
"To bazan daina ba, tallah yanzu suka fara siyar da abinci ba ki d'auka yanzu aka fara wallahi sai sunyi. Inda Allah ya bani manyan y'ay'a maza ya za'ayi na saurare su?, haihuwar y'ay'a mata a farko ma ai asara ce."

Umma da take d'aki tace, "Haba malam, da kanka kake furta wannan maganar?, abinda Allah ya baka ne fa kake cewa asara?."
"Asara mana inda wad'anda na  aurar suke gidan mazajen su ne y'ay'ana maza da yanzu sune suke taimaka min ko d'awainiyar ku suka d'auke min ai na huta amma duka mata ne kuma suka auri talakawa ba uwar abinda nake mora, su kuma wannan da suke zaune ba miji sai na zuba musu idanu haka kawai ina ciyar dasu a banza bana k'aruwa?."

KWANTAN ƁAUNAOnde histórias criam vida. Descubra agora