kamar yanda yake a ɗabi'ar Rashid ya shafo sumar kansa a sanda suka hau babban titi, yay ƙasa da murya tukunna ya ce, “Daddy don Allah ka yi haƙuri “.

Daddy yay kamar bai ji shi ba, ya ƙara maimaitawa a karo na biyu nan ma Dady yay masa banza, sai can ne Suhail ya iya buɗe baki da ƙyar shi ma ya ce, “Daddy don Allah kar ka kaimu station kayi haƙuri, Daddy hakan kamar tona asirin gidan mu ne, Daddy kaima zaka iya sasanta lamarin amma idan muka je station sai ayi tunanin ko wani mummunan laifi muka aikata”.

“Amma ai ni kun iya tona min asiri a gaban ko waye kuma a duk lokacin da Ku ka ga dama, ƙarshe ma yau abin akan Uwata ya ƙare har ku iya karya min ƙafar ta...".

Rashid yay saurin cafewa da faɗin,"na rantse da Allah Daddy yarinyar nan ƙarya take yi lafiyar ƙafarta lau...".

Daddy ya katse shi, "Dilla can rufe min baki, gaba ɗaya kun zama sai kace dabbobi duduf duduf kullum kuna cikin Dambe kamar ƴaƴan madanbata. uwar ku na ganinku ba zata yi muku magana ba, kun girma baku san kun girma ba, kuna ta girma amma babu hankalin sai cin kashi kuke kullum, haka ku ka ga sauran ƴan'uwanku na yi...".

ai Daddy bai ida abinda zai ce ba bakin Suhail a gaba ya ce,"Daddy suma fa su nayi kawai don su ɗin sun fi mu yawa ne yasa ba'a ganin na su".

ya faɗa da tsananin jin haushi, don yana mugun kishi idan Daddy nayi musu faɗa ya dinƙa kwatantawa da step brothers na su, duk saboda hakan ne ma mafi aksari ba ya biyewa Rashid ɗin balle azo yi musu nasiha a dinƙa haka kuka ga sauran ƴan uwanku nayi ko kuma kuyi koyi da su.

Daddy ma ya katse shi da cewa, "idan sun yi ai ba irin naku na mahaukata suke yi ba shisa ba'a shaidawa, Amma yau zan yiwa tufkar hanci, duk zaku gane kuren ku ɗaya bayan ɗaya, ko wanne zai ji a jikin shi, yo wai ni...kai ubangiji ya shirya mana dai”.

Yama rasa abinda zai ce musu kawai sai ya riƙe haɓa yana cizar leɓen sa na ƙasa, da tunanin tasa yarintar, shi dai ya san bai yi ba ko kaɗan.

tausayin Daddy ya kama Suhail ganin yay tagumi, a hankali ya ce,"Daddy Wallahi yaron nan ne yake jan komai, sam bashi da kunya bai san gaba nake da shi ba, baya bani girma na, yafi tsoron su Yaya Babba, kuma na rantse da Allah Daddy in ace bana kai zuciyata nesa akan yaron nan da tuni na gama da rayuwarsa billahillazi kaji na yi maka wannan rantsuwar, wallahi da tuni sai dai uwar shi ta haifi wani”.

Caraf Rashid ya ce, “wallah ƙarya kake yi, kai ɗin banza kai ɗin wofi, ai wallah ka yi tsarara na tsaya ka dake ni har kana iƙirarin wai uwata ta haifi wani, ai ko a dukan da ka sha yau kasan wallah ƙarfi na da naka ba ɗaya ba wallahil azim, kuma ni baka kai in dinƙa baka girma ba kayi kaɗan, shekara nawa ka bani...hmm wai sai dai uwata ta haifi wani, ai ko sai dai in a haifi waninka wallah...”.

tayoyin motar suka bayar da sautin ƙuuu akan titi saboda wani mugun taka burki da Suhail yay, ya juyo ya kalli Rashid ya kuma kallonsa, ya jijjiga kai tare da yin ƙwafa me ƙarfin gaske yana hura hanci da sauke numfashi.

“marar kunyar banza da wofi kawai, kaci gaba da magana rabon in raunanaka ne yanzu...”.

bai gama rufe baki ba Daddy ya doka musu tsawa tare da faɗin, “Inna Lillah wa inna ilaihi rajiun!. Hasbunallah wa ni’imal wakil!!, ku rufe min baki, na faɗa muku ku rufe min baki, na fiku zafin kai fa ku kiyaye ni wallahi, ƴan banza kai”.

Jin haka duk suka yi shiru, sai hucin su da ke faman tashi a motar, kuma babu shiri Suhail ya ɗora driving ɗin da yake saboda mugun kallon da yaga Daddy na watsa masa.
motar tayi tsit tafiya kawai suke akan titi, Daddy na nunawa Suhail direction da hannu na inda za su je.

Ga mamakin su sai suka ga sam ba hanyar station suke bi ba balle suje station ɗin, ta cikin mirrow suka haɗa ido suka harari juna.
Suhail yay parking a daidai inda Daddy yay masa nuni, suka fito daga motar suna kallo Daddy yay gaba amma su sai sukai cirko cirko, da wata muguwar harara Daddy ya bisu ba tare da yace musu ƙala ba.

RAGAMAR DAMISAWhere stories live. Discover now