5

16 5 4
                                    

*RAGAMAR DAMISA*
       '''FreeBook.'''

*©️Halimahz*

*SADAUKARWA GA:-*
Muhammad Kareem(MK)

_for your business advert DM 08145146915._

*(5)*

Duk sun shiga mota sun zauna a baya babu wanda ke da niyyar driving, Daddy da ke tsaye daga bakin motar bayan gama wayarsa ya bisu da kallo ɗaya bayan ɗaya, wani tsabagen takaici ne ya cika masa rai, cikin ƙufula da faɗa ya ce,"ashe rashin mutuncin har a kaina ma gwada shi za a yi".

Jin haka yasa Rasheed saurin kallon Suhail ya ce, “baka ji ba ne?”.

Kamar jira Suhail ɗin yake yi a fusace ya ce, “Wallah ban ƙi mu kuma dakuwa akan haka ba”.
“To a tunanin ka waye zai ji tsoro?, waye yake tsoron ta mutu ko ta yi rai”.

“Wanda ya ji a jikin shi”. Suhail ya faɗa a zafafe.
Rashid yace,"ka bar ganin ka bani shekara uku kayi tunanin zanke rangwanta maka, ni sam bana ɗaukarka a wanda ya girme ni".

Suhail ya taso sama yana faɗin,“na rantse da Allah idan ban daki bakin ka na ci ubanka a wurin nan ba ka canja min suna”.

Cikin zafin rai da huci irin na cikakkun masifaffu Suhail ya fara ƙoƙarin fitowa daga mota, Rashid ma yay ƙoƙarin fitowa dukan su kowa na ɗaga riga zai cire.

Rashid ya ce,"daga yau ba zaka ƙara sha'awar zagina ba".

Suhail ɗin ma ya ƙara cewa,"an zageka kayi duk abinda kake ganin zaka iya marar kunyar banza fitsararre, kuma wallah ban ga me hanani cin ubanka a wurin nan ba yau".

ganin haka ya sa Dady saurin tarar numfashin su da faɗin, “sai kuma cikin ikon ubangiji da nasara uban naku yana tsaye dai a gaban ku, yana jiran ku ci nashi uban shi ma daga nan ya ci naku uban”.

Sai a lokacin suka farga suka dawo hayyacin su, Suhail ne ya yi ƙwafa me ƙarfi ya nufi mazaunin driver zai zauna, har yanayi kamar zai bi ta kan Daddy ɗin, Matsawa Daddy ya yi cike da mamaki a fili ya furta, “ubangiji kai ka bani Su, kuma kai kaɗai zaka shirya min Su har ma ka daidaita zuƙatansu, duk ɓacin ran da kuke saka min ba zai taɓa sawa in yi muku baki ba sai dai adu'ar”.

Sannan ya shiga ya zauna a gaba Rasheed yana baya, bayan daidatuwar zaman Daddy ya ɗaga waya yay kira yana cewa,"Bilal je ɗakina ka ɗauko min ATM a jaka, standard charterd zaka ɗauko kayi da sauri".

in few minutes Bilal ya ƙaraso bakin motar, ya miƙawa Daddy ATM ɗin yana faɗin, "Daddy Hajiyarmu ta ce a taho wa da Hanifa Golden morn, sannan da sikari da lipton wanda ke da akwai ya ƙare".

Daddy yay guntun tsaki da faɗin, "wato sai da na ce a ɗauko ATM sannan aka san sun ƙare, da bana gidan me kuke ci?".

Bilal na sosa ƙeya da ɗan murmushi a fuskarsa ya ce,"ai yau ɗin ya ƙare ne".

"to ku dafa fara da mai kuci, ni ba kantin kayan shayi nayi ba".
Bilal ya waro ido waje yana cewa,"Dady shinkafa a breakfast? ita ɗin ma da mai da yaji". yay maganar da jinjina zancen.

Daddy yay masa wani kallo ya ce,"ita ɗin ba abinci ba ce?, ku kullum cikin a siyo a siyo". ya faɗa yana mayar da dubansa ga Suhail ya ce,"kai kuma muje".

Suhail ya kunna motar yana murza stearing, har suka fita daga gidan babu wanda ya ce ma kowa komi.

zuciyar kowa cike da saƙesaƙe, duk su biyun sun san ba haka tafiya tare da mahaifin su ke kasancewa ba, shi me yawan yin hira ne ga ƴaƴansa a duk sanda suke tare, musamman idan ta kasance fita ne suka yi to ya ta basu labarin yanda rayuwa take da kuma shawarwari iri iri, to amma yau ɗin sai ga saɓanin hakan, wanda sun san ba komai ba ne illa fushi da yake da su.

RAGAMAR DAMISAحيث تعيش القصص. اكتشف الآن