Chapter 19-20

20 1 0
                                    

*FALAK🍒*

Mom Islam

E.O.W

Page 19-20

Beauty ta kafa kai kenan wayar Arif ta fara ring, yai saurin d'agawa tare da cewa "my lovely dad am coming"
Taga ya fice da sauri.
Jikinta na karkarwa tabar d'akin har tana bigewa da bango, tana zuwa d'akinta ta fad'a gado tare da dafe k'irji ta fashe da matsanancin kuka mai tsuma zuciya, kuka takeyi sosai kamar wacce aka yiwa duka, a daren dai ko abinci bataci ba haka ta kwanta zuciyarta a cunkushe da tarin bak'inciki.
Maleek•
Cikin hanzari ya iso bedroom d'in Maleek, Arif yace "my dad gani"
Abin mamaki nace ashe yana nan yace kar tayi abinci dashi?.
Maleek yace "ya maganar kayannan suna shiga kuwa?"
Arif yace "eh dad ai kullum cinikinsu akeyi ina tunanin saima anyi sabon d'iba"
Maleek yayi murmishi kafin yace "ubangiji ya barni dakai my lovely son"
Arif yace "Amin ya rabbi"
Daga nan Arif ya fice,  a cikin daren ya wuce inda dad d'in yake siyarda cocaine (hodar ibilis) kasancewar babu nisa a tsakaninsu, yana gudun kar dad d'in yazo ya ritsashi bai gama lissafi ba, a tak'aice dai anan ya kwana.
Germany
Yau kwanan bak'insu Falak wato 6arayi kwanansu uku a cikin d'akin, amma suna nan jiya I yau, dan babu abinda ya sauya zani, kullum cikin duba Taswira suke had'e da bincike tare da wani boka da already dama anzo dashi.
Yau sun shiga k'ofa ta biyu, matsatsinta ya isu, basuda halin komawa baya, cikin tsananin tashin hankali da tsoro ga zafi da ko shan iska gurin bayayi, suka fara jimanta halin da zasu shiga sunzo da gorar ruwa harda kayan itatuwa duk sun taho dashi tun kafin akai sati sun cinye fin rabi, ruwa kuwa yakusa k'arewa, cikin nawuyacin hali Manaf yace "gaskiya bazan iya wannan aikin ba komawa zanyi har ga Allah akwai cutuwa a ciki, banga alamun zamuyi nasara ba"
Boka ya sheke da dariya kafin yace "ai a k'a idar wannan d'aki idan aka shigo dole sai an shiga ciki kafin a fito"
Manaf yace "munyi tafiya kamar wasu marasa galihu ko kwata bamuyi ba nidai na gaji"
Boka ya rungume Manaf dake wani irin tari, kafin yace "kayi hakuri inada yak'inin sai munje gurinnan nayi muku alk'awarin duk Wanda yaji jikinsa babu K'arfi yayimin magana zanyi masa magani"
Tashi d'aya Manaf yaji k'arfin jikinsa sukaci gaba da tafiya babu iyaka, anan k'ofa ta biyun da ko rabinta basuyi ba anan dare yayi musu, dole suka gwamutsu cikin matsatsi suka fara bacci, dan babu gurin kwanciya.
Falak•
Yauma kamar jiya sam bacci ya k'auracewa idonta ta kasa koda runtsawa, aikinsa takeyi ma bazai bari bacci yayi nasarar d'aukarta ba, a koda yaushe tana binciken inda zata k'arawa d'akin sirrin dad d'inta tsaro domin kareshi daga sharrin azzalumai, cikin hukuncin ubangiji take samun nasara da abubuwan da zasu dinga taimakarta.
Tunda suka dawo dad ya wuce part d'insa kasancewar yau ko gurinsa batazo ba, shiko har yayi bacci saboda rashin baccin da beyi ba jiya,
Iyakan Falak abin yaso ya zame mata jiki, saboda tana nunawa bacci halin ko ina kula, sai ta kusan raba dare a gaban system, a Nigeria nema take samu take hutawa, idan ta dawo gurin dad babu halin kwanciya bare hutu ko tayi charting da wani inba searching akan abubuwan da zai kawo musu ci gaba ba.
Cikin rashin tsammani tana shirin rufe system d'in taje ta kwanta taji kiran sallahr asbha, da sauri ta kalli agogo tana mamakin "oh kodayake ba'a mamaki da ikon Allah"
Taje tayo alwalah tayi nafila kafin ta kabbara sallah lokacin an shiga, tana idarwa ta d'auko alkur'ani mai girma kamar kullum da ta sabarwa kanta, bayan tayi karatun ta mayar dashi mazauninsa,
Ta koma gado tare da Jan blanket, hhh kunsan fa hausawa sunce ba'a cin bashin bacci, aikuwa yayi awon gaba da ita, har k'arfe 8:30 tayi ankawo mata breakfast sai akan dinning aka ajiye bata tashi ba, dad harya yi breakfast ya shirya ita yake jira, dan gudu gudu ya shirya sabda kartazo ta uzura masa, ya jita shiru har yanzu, kai tsaye ya taho part d'inta a hankali yake ambatar "my daughter" shiru bata amsa ba, ya taho a hankali ya murd'a handle d'in k'ofar, ya ganta ta rufa da bargo, ya janyo k'ofar a hankali ya dawo parlo, system d'inta daya gani jone a chaji ne yasashi cewa "k'ilama bata samu tayi bacci ba, Allah yayi miki albarka y'ata" a hankali yake maganar ya fice.
Parking space yaje, ya shiga mota aka wuce dashi gurin aiki,
Alhmdulilh yau kam beji fad'uwar gaba kamar koda yaushe da yake jiba idan yazo zai shiga company d'in, yayi aikinsa cikin yardar ubangiji sosai yayi komai cikin nutsuwa, har wasu kayayyakin da aka basa contract ya bayar an had'asu, yana zaune yana hutawa har k'arfe 1:pm na rana tayi, wata mota fara mai kyan gaske tayi parking, sai da akayi checking mutumin kafin ya shiga, bayan sun gaisa da dad yace ga list d'in kayan da yake so, k'ofofi ne na zinare sai table shima na zinare, mutumin Mai kirki ya ninkawa dad kud'i fiye da inda ya siya, tun daga lokacin sukayi musayar lambar waya, dad yayi masa godiya mutumin ya tafi, jikin dad na rawa ya rangad'o wa Falak Kira, yanzu ma ta fito daga wanka tana d'aure da towel, taje da sauri ta d'auki wayar tana murmishi, "Dad"
Ta fad'a a hankali, kafin ta amsa kiran, "auta yaufa akwai bidiri anyi ciniki fiye da kowacce rana"
Cikin farinciki Falat tace "Masha Allah Dad wlhi na makara"
Dad yace "ki shirya a hankali kinji Daughter"
Yana katse Kiran taje gaban dress mirror tashafa lotion d'inta masu k'amshi kafin ta shafa powder ta fesa turare kafin tazo gurin saka Kaya, yau kam shadda take burin sakawa, abinda mutanen garin yawancinsu basa sawa kenan, ta d'auko shadda mai ruwan toka ko ta ina ansa stone sai aiki da akayi a k'asan rigar da Kuma gaban rigar, tayi mata kyau sosai tayi d'aurin d'ankwalin Zahra buhari, kasancewar tazo da abin d'aurin d'ankwalin, wow Falak tayi kyau sosai, tasa plate shoe d'inta fari haka ma hand bag dinta fara, ta fito fuskarta wasai itama yau haka kawai ta tashi da tsananin farinciki wanda bazai misaltu ba.
Tana zuwa parking space, ta shiga mota driver ya kawota company.
Cikin fara'a take amsa gaisuwar mutanen gurin, tana isa office d'in Dad ta durk'usa ta gaishe shi, ya amsa tare da shafa kanta, kafin yace "ya gajiyar aiki"
"Alhmdulilh tace masa, ya nuna mata alert d'in kud'in tayi hamdala kafin tace "dad yanzu fa kasan dole a shiga d'akinnan a d'auko wasu?"
Dad yace "ta66 ai na mance to yanzu ya za'ayi tunda gashi mun sawa mutanen da suka shiga tarko"
Falak tace "ko zasu kai shekara suna tafiya dad ba hanyar da muke bi sukabi ba, zamu iya shiga ba tare da sun ganmu ba".
Dad yayi hamdala kafin yace "yau da wuri zamu koma gida".
Egypt
Cikin hukuncin ubangiji su Ummu suka lokacin anata kiraye-kirayen sallahr magariba, kai tsaye gidansu suka wuce.
Gidane na Family babban gida, gidan hawa biyu ne na gidan sama, mahaifiyarsu momy ne a can, k'asa Kuma kakarsu, wato mahaifiyar babansu,
Sai da suka fara shiga sashenta suka zauna, saboda gudun kamun baki, kafin suka yi sallah, bayan sun idar ta kawo musu abinci, basu wani ci mai yawa ba, kasancewar kunsan ba kowa bane in yayi tafiya yake iya cin abinci sosai, Ummu Shukura tace "Granny wlhi a k'oshe muke sai zuwa anjima"
Kasancewarta masifaffiyar mata tace "kwa iya da gulmarku banda gulma babu abinda kuka ajiye, kun wani rankayo biki, inace da kud'in kuka turo masa zaifi jin dad'i a maimakon zuwanku"
Momy ta ta6a Ummu Shukura a fakaice alamar su tashi, ashe idon granny yana kansu tace "daga fad'ar gaskiya sai guduwa to ku gudun mana"
Momy tace "haba Granny har yanzu baki sauya halinki na fad'a ba? sam wannan abinda kikeyi bai dace ba"
Momy ta bud'e jaka ta mik'a mata kud'in da a k'alla a kudinmu na Nigeria zai kai dubu goma Ummu Shukura ma ta ajiye mata, Granny ta zube a k'asa harda rage murya tana zumbud'a godiya, cikin tausasa kalami tace "kuyi a hankali da y'an biki, wani neman yaga ka ajiye yakeyi sai ya d'auka"
Ummu Shukura tace "hakane Granny"
Suka mik'e tana ce musu su gaida Umminsu.
A hanyar hawa steps, Ummu Shukura tace "meyasa Ummu Amal bata zoba?" Momy tace "ta kawomin uzurinta amma ta bada kud'i abawa Ummi"
Suka k'asa da zancen Granny mai hali baya fasawa,
Cikin farinciki suka shiga d'akin Ummi  itama ta tarbesu tana murnar ganinsu, aka fara gaiggaisawa Ummi tace "Ina Ummi Amal fa?"
Momy tace "dan Allah ayi mata uzuri wlhi tace "mijinta ne ya hana shiyasa batazo ba amna ga kudi ta bada nata gudunmawar"
Ummi tace "Allah yayi albarka"
Daganan aka fara hirar yaushe gamo, Ummi tace "ni naga banga Beauty bane?"
Momy tace "na barta a gida"
Ummu Shukura tace "nima dai da anyi shawara dani wlhi baza'abar Beauty a gida ba, wannan mugun uba nata bashi da hali ko kad'an"
Ummi tace "hmm Allah ya kyauta amma abin babu dad'i".
Kusan kwana sukayi suna hira cikin farinciki, washe gari da asbha suka dukufa aiki, yawancin mutane a daren suka zo kwana, sukayi aiyukansu da wuri, ba wata al'ada sukayi ba, duk da sai gobe d'aurin aure.
Abdul-Naseer ya shigo gidan yana k'walawa Ummi Kira, Momy da Ummu Shukura da sauran y'an uwa sunata tsokanarsa wai ango yasha k'amshi.
Shiko sai risinar da kansa yakeyi, inka ganshi kamarsu ta 6aci tsakaninsa da Momy, sunyi kama sosai, duk da  kamar da yayi na larabawa, momy kuma sak turawa.
Zuwa yamma su momy sunyi wanka, Abby ya shigo, sukaje har d'akinsa suka gaishe shi, yayi musu nasiha kafin yace musu "shima bai kwana a gida ba aiki ne ya rik'eshi.
Ya tambayi Ina beauty, Momy tace "ai tana gida, shima sai daya jinjina cewar da tayi tana gida yaji babu dad'i yasan waye Maleek".
Zuwa yamma suka kai kayan lefe gidan su budurwar da Abdul-Naseer yake nema, kar6a ta karamci da mutunci akayi musu, tare da Sha Tara na arzik'i anyi musu hidima sosai abin sai Wanda ya gani, suka dawo gida suna bada labari, dayake sun sanwa Granny kud'in da aka basu tadinga cewa matar Abdul-Naseer  ai y'ar albarka ce yayi sa'ar yin aure Allah ya bada zaman lafiya"
Zuwa dare aka dinga buga ganga a wani kyakkkyawan fili Mai d'auke da grass carpet yawancin abokan nasa suna ta rawa, harda wani bak'i a cikin su da alamu shid'in namu ne lolz wato( Nigeria)
Washe gari, da misalin k'arfe 11:20 aka daura auran Abdul-Naseer da Fadwa, d'aurin auren da ya samu halartar abokai ta 6angare uku tare da abokan arziki.
Switzerland
Arif bai samu ya cimma burinsa a wannan dare ba, amma yad'au alwashin safiya nayi da ita zeyi breakfast....

Idan baku manta ba, da nace muku gajeren labari ne, yanzu kam wasan ma ba'a fara ba, littafin FALAK iya kaiwa Book1,2,3,4 insha Allah, banyiwa kowa dole ba, nasan masoyan Falak zasu so jin labarin ba'ayi komai ba, dalilin da yasa nace muku labarin zeyi tsayi kenan, a page 30 zan tsaya Ina Mai baku hak'uri, bawai ina nufin wani abun bane,
normal group 300 posting d'aya a Rana ba kullum ba,
Zanyi Vip group 500 posting biyu   a rana.
Zanyi special wato manyan mata masu so ta private 1k posting sau uku zuwa hud'u Rana.
Ba lallai kullum y'an normal su samu ba, falyakun khairan... Kafad'i alkairi ko kayi shiru...

Dama gareku masu son adama dasu a doguwar tafiya mai d'auke da sabon salon cakwakiya zasu iya biyan kudinku tanan. 3175689751,Zainab Habib first bank.
Idan katin mtn ne zaku d'auki hoton katin ku turo ta wannan number 08141799224
Masu son shiga group d'ina suyimin magana WhatsApp only mata zalla 08141799224

Mom Islam

Masu son shiga group d'ina suyimin magana WhatsApp only mata zalla 08141799224

Mom Islam

FALAKWhere stories live. Discover now