page 8

379 16 4
                                    

*A DAREN AURENA*

            BY

MissDmk✍🏻

Page 8

Fa'iz?
Na yi magana ta leben baki,yadda ni kadai naji magana ta sai kuma shi dake kallo na, alama yayi min da ido da nayi shuru, durkusawa har kasa nayi na gaishe da Ummah kafin na gaida sauran...

Yazid yace Hafiza Ina kk samo wannan hadaddiyar, kyakkyawar yarinya?ni tunda kk fito nake kallonta...

A hassale Fa'iz yace ba ka da kunya koh?eh Yazid?

Hamma wasa na keyi kaima kasan wasa ne, don Allah kyakkyawa kiyi hakuri I'm jourvial shiyasa, murmushi nayi nace ba komai, ya wuce, Hafiza na tafi driver na jirana a waje... Sallama mu kayi kafin na wuce, ko minti biyu banyi da tafiya sai ga kiran sa,

Miye kk tsaya kina murmushi a gaban Yazid?

Shuru nayi ina awna maganar sa? Coz ban gane ba..

Can dai yace ba na ce ki dinga sa Hijab ba?

Ai Abaya na... Ban karasa ba ya katse ni da cewa kinja anata kalle min ke, why Faizah? miye sa ba zaki bi umarni na ba? Don Allah karki sake fitowa haka...

Nace OK,

Wai daman kinsa Hafiza?

Nace eh, ai itace K'awar da nake baka labarin ta..

Oh really? Please don't say anything to her, I wanto surprise them, ranan nasan za ta yi farinciki in ta samu labarin ke zan aura...

Shuru nayi ina tunanin what if shine muradin zuciyar Hafiza? Can nace ya kk da Hafiza coz na ga baku Kama,

Uhmm she's my cousin, yarinyar kanni Abba ne..

Ji nayi gabana ya fadi amma ina tsoron tambayasa how close they are? What if shine Hamman da take mutuwar so? Ganin nayi shuru yace please don't say anything to her Kinji, bye! Anjima zan zo gidan kit ya yanke...

Jikina ya mutu, tunanin Kala kala suka dinga zuwan min, gaskiya indai shine muradin ta, zan bar mata shi kawai dan ba zan so zuminci mu ya watse akan saurayi ba, Idi ka mayar dani gida kawai, amsawa yayi da toh, da sakesake cikin raina na isa gida, sam na kasa sukuni..

Bayan sallar magrib sai gashi ya zo, zubula hijab nayi har kasa naje na same shi, gaishe shi nayi kafin na zauna

Lafiya kk Roh? Ya nagan ki ba a yadda na saba ganin ki ba?

Uhmmm ina da tambaya amman please inaso ka gaya min gaskiya ban so ka boye min komai..

Amsawa yayi da toh gayamin Inajin Ki,

Ya kk da Hafiza?

Dariya yayi sosai kafin yace kishina kk yi?

Uhmmm if you see it that way, nide ka bani amsa ta,

Well she's my favorite cousin, ina jin hakan, na mike nace wai wait daman kaine favorite da take bani labarin ka?

Eh.amman mai take ce maki akaina?

Bakomai kawai ya kamata kuyi magana da ita I think she have something to tell you..

Nifa ba maganar Hafiza ya kawo ni nan ba, indai Hafiza ce ai kulum muna tare da ita, kuma na san za ta ji dadi duk ranan da tasan cewa ke zan aura, Faizah na kosa ranan ya zo, ranan zakin sa cewa ni mai sonki ne kuma mai kaunarki ne, A Daren Auren mu zan shayar dake madaran soyayya..

Don Allah ka daina fadin haka...

Tsoro kk ji wai? ke da ya kamata ki fara shiryama wannan daren, ranan da zamu zama daya nida ke?

A DAREN AURENA Where stories live. Discover now