Page5

170 14 0
                                    

🌹Namijin Bahaushiya🌹
      

By NucyAdam
 

Episode5
Bayan yasha ruwa ya mika mata kofin, bubbude hanci yafarayi irin maison ta tantance kanshi meye yakejini kallonta yayi my luv wani dan wari wari nakeji, Zaro ido zahra tayi wari kuma tafada itadai asanin ta babu abunda ke tashi a falon daga kanshin turaren wuta saikuma kanshi miyar kubewarta to ko kanshi miyarne yake masa wari tafada a ranta, ganin kamar maganar tasa bata mata dadi bane yasa ya kakalo murmushi sorry my luv inaga hancinane me kika dafa mana ne tace tuwo ne miyar kubewa  yace ok my luv ban cika son miyar kubewa ba amma dayake nakine nasan zaiyi dadi kwarai. Dadi tadanji sanann ta wuce takawo musu abinci bayan sun gama ci mukhtar yana zabga hamma my luv muje mu kwanta ko? Da mamaki zahra take kallonsa habeebi tun yanxu xamu kwanta karfe 9 murmushi yayi haba my luv nida nAke fita office da sassafe aikinga dole na kwanta bacci da wuri ko? Shagwaba tafara masa irinta yara tana bubbuga kafa nandai ya lallasheta sukaje su ka kwanta duk da xahra dai ba bacci takejiba ..
    Watanni sun tura da bukin zahra da mukhtar sosai zahra takejin rashin dadin wasu halayen mukhtar nafarko idan tayi kwalliya baya yabawa duk irin kyawun daxayi bataji yana kodata kamar yanda take gani a film dama littatafan novel. sannan hakama idan tayi girki shima baicewa yayi dadi saidai ya dibi girki ya yi mukus duk da yawan abincin da yakeci tasan idan abinci baimaka dadiba baxakaci da yawa haka ba amma sam baya yabawa.. saikuma yawan korafi da yake dashi ko yaya aka danyi abu ba daidaiba xaiyi magana amma fa idan anyi daidai baxaice angode Allah ya saka ba 😹. Yauma kamar kullum bayan ya dawo daga office xahra tayi kwalliya cikin riga da wandon ta jeans irin crazy dinann baayan yashigo takarbi kayan hannunsa tanata jira taji ya yabi swag din nata amma shuru tagaji tace habeebi bakace nayi kyauba kallonta yayi kinyi kyau mana my luv amma wannan wandon aiyayi miki kadan wannan saidai salma ( kanwarta) yafada batare da ya yi tunanin komaiba itakam jikinta ne yayi sanyi sosai daki ta koma tacire kayan tasaka bakar jallabiya bayan tafito takawo masa abinci baayan yagamaci kallonta yakeyi my luv yadai najiki shuru yau babu hira ne adan dakile tace bakomai yace kintabbatar tace eh ok to bara ni naje nakwanta idan kintashi saiki dan kulle gidan, kulle gida kuma? Aa gaskiya kaje kakulle ok yje ya kulle ya wuce y kwanta, zahra kam a zuciyarta sake sake kawai take dama mukhtar haka yake tayi tunanin soyayya zasu durza duba da yadda baiji dadin matarsa tafarko ba ashe shima da halinsa tafada a ranta to waya sanima ko itama da tanayi rashin yabawarsane yasaka ta watsar 🤔

      Tofa yaya abun yakene 😂 kubiyoni cikin littafin mijin bahaushiya danjin yadda xata kaya, gaskiya xan tsaya da typing sbd bakwa comments , kusani comments dinku suna karamun kwarin gwuiwa pls comment share and vote
   Taku NucyAdam 🥰

Namijin Bahaushiya Where stories live. Discover now