Page3

267 6 0
                                    

🌹Namijin Bahaushiya 🌹
   
By NucyAdam
 

   Episode3
Karfe 7:30 shima mukhtar yafito sane cikin kayanshi naxuwa office  suite na company estilo yayi kyau abunshi kofar bedroom din safiyya ya kalla bayan ya fito ba motsinta alamar bata tashibama ballantana tayi tunanin zaitafi office har ya samu breakfast.
- [ ]      Karfe 2 daidai yatashi daga office schl din su zahra wuce dan sunyi waya akan zaizo bayan tagama lectures a haraban makarantan nasu yayi parking takaraso fuskarta dauke da kyakkyawan smile dinta shima gogan nata smile din yaketa antayo mata 🤪 bayan tashiga motar yaja suka tafi suna hirarsu ta masoya.. akofar gidansu yayi parking bayan sun kara taba hira na 10minutes anan ne yake fada mata cewa shifa yanaso yaturo ayi maganar aurensu cikin jin kunya taja gefen gyalenta ta rufe fuskanta, au kunyata ma kike ji yafada yana leko fuskan nata haka dai suka yi sallama bayan ta tabbatar masa zata fadawa mamanta itakuma saita fadawa babanta. Bayan mukhtar ya ajiye zahra gidan hajiyarsa ya nufa bayan sun gaisa yake fada mata xancen turawa gdn su zahrar nan tace yaje yasamu kawunsa yayan babansa saiya fada masa, dayake mahaifin mukhtar ya dade da rasuwa kuma shikadai ne iyayensa suka haifa. Bayan yayi sallama da hajia gidan yayan babanshi yawuce a anguwan kabala bayan yayi masa bayani  yace yana jira gidan su yarinyar su bashi rana sai aje a nemar masa aurenta yayan baban nashi yace masa ba damuwa duk ranar da suka bashi saiyazo yasanar masa insha Allah saisuje tare da abokinsa alhaji namadi. Daga nan gidansa yawuce as usual yauwa dayashigo safiyya tana toilet da alamu wankan dabatayi sai yamma shi takeyi baisamu mukarram a  falo ba kamar jiya xama yayi a daya daga cikin kujerun da suke falon da sauri ya tashi sbd jidayayi ya xauna akan wani abu kamar ruwa hannunsa ya shinshina nan yaji wani mugun zarni a fusace yanufi dakinta da nufin yi mata maganaa, kasa kasa yake ji kamar safiyya tana waya tsayawa yayi daga corridor din dakin ya kasa kunne muryar safiyya yaji tanacewa idan ma baici abincin ba xan saka mishi a ruwan shayi dan shan shayinnan na dare da ya xame masa kamar masifa kullum saiyayi yishi na tabbata tanan xaa samu nasara tunda malamin yace duk iskancinshi idan yaci ko yasha maganin nan sai yanda nayi dashi, sosai mukhtar yacika da mamakin abunda safiyya ke fada awaya muryarta ya kara ji tana fadin ai ita kanta munafukar uwar nan tasa sainasa anrufe mata baki dan itama tasamun ido, sosai bacin ran mukhtar yakaru labulen dakin yadaga yashiga yatsaya yana kallonta sosai gabanta yafadi tayi saurin jefar da wayar tana sosa bayan wuyanta abban mukarram yausha kashigo mugun kallo ya watsa mataa da ya tabbatar mata yaji abunda take fada, cikin kausashshiyar murya yace mahaifiyar tawa kike kira munafuka safiyya cikin in ina take kokarin kakalo abunda xata fada masa kamun tasamu damar cewa wani abu yace kije gidanku nasakeki saki biyu,, sosai  gabanta ya fadi tashiga bashi hakuri bai saurareta ba yashige dakinsa yasaka key don ma karta samu damar biyoshi....
09139097669

Namijin Bahaushiya Where stories live. Discover now