GIDAN SU SAUDAT.

Da kuka ta koma gidansu ,tana shiga ta faɗa jikin Ummanta tace "Umma nayi abun da zai dameni "Umman da taji abin da Saudat tayi ta dinga yi mata faɗa sosai kuma faɗan ya shigeta .

Kwana goma a tsakani wani ɗan yayar Umma yazo yana son Saudat , hamdala Umma tayi kasancewarsa mai kuɗi irin mijin da Saudat takeso ne ,kuma koda yazo gurin Saudat ɗin bata nuna bata sonsa ba ,kasancewar ta samu cikon burinta.

Koda kawo kuɗin sa aure tare da jin sa rana ba'asa da nisa ba , sati huɗu akasa.

Umma da baba sai murna suke zumunci zai ƙara ƙarfi.

              *******

Kwanci tashi babu wuya a gurin Allah ,yayinda kwanaki suka shuɗe satikai suka shuɗe ,Allah ya kawomu bikin Saudat , biki ne da akayishi na masu nera ,kasancewarsa ɗan Sunnah bai bari anyi wasu wasanni ba , amma anyi walima aka kaita gidanta dake taminos tsakaninsu da su Umma nera ɗari ,sai dai muyi mata fatan Allah ya bada zaman lafiya da kuma zuri'a ɗayyiba.

GIDAN ABDULL

Bayan Abdull ya gama cin abinci ya miƙe ya koma ɗakin Fatima tare da wucewa bedroom kai tsaye , yana shiga yaga big boy a tsaye zigidir aihuwar uwarsa ,ido biyu sukayi da Abdull -Abdull ya waro ido tare da cewa "ubanwa ya kawoka gidannan , jiki na rawa Big boy yace "Fatima ce ta gayyato...wani wawan mari Abdull ya bashi kana yace "bazanyi maka komai ba , sbda ba laifinka bane amma ka sani Allah ya isa tsakanina dakai ka ɗibi kayanka ka fice "jiki na kyarma Abdull ya ɗibi kayansa ya fara sawa ,Abdull ya wankesa da tagwayen maruka ,sbda yama rasa hukuncin da zaiyi masa .
Fatima da taje gurin mai gadi ta sanar masa koda Abdull yazo tambayarsa wani ya shigo yace baiga kowa ba , tana dawowa taji kuka big boy ta daskare a gurin tare da tsugunawa ,a zuciyarta tace "tawa ta ƙare "ta juya zata fice Abdull ya fincikota ya haɗa kanta dana big boy ya gwara kana yace "na sakeki saki uku dama laƙamin ke akayi ko da yake kece kika nacemin, ihu ta kurma tana tsalle tana yayi mata rai amma ina bakin alƙalami ya bushe ,tun farkon maganarsa   da big boy ya kunna recording ,sbda gudun musu koda buƙatan jin abinda ya faru ya taso , haka big boy yabar gidan Abdull na dukansa ya kasa taɓuka komai tunda yasan shine bashi da gaskiya.
Big boy na fita Abdull ya dawo kan Fatima yace "ki barmin gida kafin in illataki "ganin yana magana a hassale yasata ɗaukar mayafinta dake gefe ta fice da gudu , kai tsaye mashin tahau ,ana sauketa tace "bari ta shiga ta karɓo masa kuɗi ,jiranta ya tsaya yi ta yiwa mai gadi magana akan ya bita ya karɓo kuɗin ,Fatima na kuka ta faɗa palon su tana shiga ta iske Hajiya  rta a zaune tana gyara wasu tsadaddun mayafan data saro ,da gudu Fatima taje ta faɗa jikinta tare da cewa "Hajiya kiba mai gadi kuɗin mashi yana jira a waje "ɗari biyar ɗin dake kusa dashi ta miƙawa mai gadi ya fita , Hajiya tace "ya na ganki haka ?"Fatima tace "ya sakeni saki uku "a razane hajiya ta miƙe tare da dafe ƙirji tace "kice ya mayar da ke bazawara wlh yau za'ayi tashin hankali dan wlh bazata saɓu ba wai bindiga a ruwa"Hajiya ta miƙe tare da sanya hijab tayi gidansu Abdull,kasancewar ba nisa ,tana shiga taga Abdull ɗin tsaye shi da hajiyarsa da anty Ummi suna sauraron magana a waya , ji tayi ance wlhi Fatima ce ta gaiyyaceni "hajiyar Fatima ta yanke jiki ta faɗi , su Anty Ummi suka yayyafa mata ruwa ta taso ,tare da nisawa , daga nan tace "kuyi haƙuri da nazo da niyar yi muku masifa ne sai na tsinci abin da akayi ,dama ashe har yanzu Fatima na bata dena bin maza ba ?"hajiya tace "au kinma san tana bin maza kenan ?share hawaye hajiya tayi ta juya tare da cewa "Allah ya haɗa kowa da rabonsa na alkairi ,ta fice .

Hajiya da anty Ummi sun shiga tashin hankali matuƙa ,sbda abin ya basu tsoro da mamaki ,amma hajiya tayi masa faɗan gaggawar sakin da yayi ,a faɗan da tayi masa mari ne kawai babu.
Haka Fatima ta koma abin tausayi ,tun a ranar tayi nadama.

GIDAN SU ZAIYYAN
fs
Bayan Zaiyyan ya gama shafa mai itama ya shafa mata ,mamaki yake duk bakin tsiwarta ya mutu tashi ɗaya ,har tsokanarta yayi amma taƙi kulashi.
Washe gari tea ya haɗa mata da asbha kafin ya masallaci ya bata tasha ya tafi ,wanka ta shiga tana fitowa tana kaya a gurguje gudun karya ƙara yi mata wayo irin na jiya , ta shafa mai da powder tayi sallah lokacin an shiga .

Zuwa ƙarfe shida da rabi Zaiyyan ya shigo ,Ramu ta gaishe sa ya amsa ,tare da janyota jikinsa , kasa ƙwacewa tayi ta ƙura masa ido batace komai ba , ɗauko flaks yayi ya haɗa nashi tea ɗi  yasha ,zuwa ƙarfe goma yai wanka ya tafi gidansu bayan yayi mata sallama , zaman kaɗaita daya ishi Ramu ta fito palo ta zauna tana kallon ko ina na gidan tace "aure akwai daɗi amma jiya na yabawa aya ,wlh nidai nace akwai wuya "ita kaɗai take maganarta taji sallamar Hajiya Nafisa da Lami wato mahaifiyarta , daka tsalle tayi ta rungume Lami tana cewa "yau tare zamu tafi "bayan sun shiga sun zauna ta gaushesu suka amsa ,Hajiya Nafisa tace "ya naga kin rame ?"Ramu tace "jiya ne likita ya cire min kaya...Hajiya Nafisa ta dakatar da ita tare da cewa "ba nace ki daina fallasa sirrinki ba ?ƙifƙif ta farayi da ido Lami tace "aikam gashi tana ci gaba dayi , faɗa sukayi mata akan haƙƙin mijinta da kuma biyayya da yawan shan kayan marmari ,ta miƙe taje kitchen tana shirin  ɗora girki Lami tace "yanzu zamu wuce "Hajiyan tace "ki kula da tsafta sbda itace gaba akan kowanne aiki "tom "Ramu tace sukayi mata sallama tace "a gaida baba da ƙannenta.

      BAYAN SHEKARA ƊAYA

Ramu na hango tana zaune a palo kan kafet ta baje ƙafafunta gefe mangwaro ne tana yankarsa da wuƙa , sallamar Zaiyyan ne ya sata yin ƙarfin halin miƙewa ta rungumesa tana cewa "sannu da dawowa gwarzon namiji "murmishi Zaiyyan yayi kana yace "maman ƴan uku sannunki da gida "tashi tayi ta kawo masa abincinsa da juice ɗi  data haɗa masa ,kasancewar ta iya hausar boko tana gani a littafai inda ake haɗa lemu kala-kala, tana zaune taji kamar ana mintsinninta ,cije baki tayi tare da sunkuyar da kai ƙasa , Zaiyyan ya lura da yanayinta tun jiya take naƙuda a tsaye ,ya kira number Hajiyarsa ,ba'a jima ba ta iso tace "ina tunanin aihuwace haɗo mana kayan baby mu tafi "Zaiyyan ya miƙe yaji Ramu ta rafka salati ,Hajiya tayi gurinta da gudu ,tace muje hospital "kafin Sudais ya ɗauko key kan ɗa ya fara fitowa , Hajiya ta fara adu'oi tana tofa mata ,cikin ikon Allah faya ta fashe jariri ya faɗo ,duk a gaban Zaiyyan akayi komai ,yana ganin namiji ta haifa ya hau murna tare da hamdala .
Ranar suna yaro yaci sunan babanta Bashir suna kiransa da dady ,rayuwar gidan nasu ta zamo abin sha'awa da koyi ga kowa .

TAMMAT BI HAMDULLAH

Anan zan dakata da wanan gajeren labarin ,
Ina roƙon duk wanda na ɓatawa rai yayi haƙuri ,ko aka sami wani kuskure a cikin labarin , masoyana ina godiya da bibiyar labarina da kukeyi wasu na sansu wasu ban sansu ba ,to nagode Allah yabar zumunci .

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Sep 04, 2023 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

NIDA YARINYA Where stories live. Discover now