Chapter 1-2

357 10 1
                                    

🤦‍🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️
*NIDA YARINYA*
🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂🪂

_Zainab Habib /Mom islam_

*Bismillahir rahmanir rahim*




1-2
yarinya ce ƴar kimanin shekaru goma sha huɗu na hango , zaune take a bakin ƙofar wata tsohuwa tana karkaɗa ƙafarta , tsohuwar dake zaune a cikin ɗaki tace "Ramu maza kije ki karɓo min fatari na idan Adamu ya ɗinke "cikin tsiwa Ramu tace "ka jiki dai ke baki da aiki sai aikan mutane ,ni yanzu ma zanyi kwaskwarima in fice "riƙe baki tsohuwa tayi kana tace "ke karki kawomin rashin arziƙi ,ubanki ma sai in aikeshi yaje balle ke "miƙewa Ramu tayi kana karkaɗe koɗaɗɗen zaninta tace "idan yazo kya aikeshi nikam dandali zani ".

Tsintsiyar dake bakin ƙofa ta wurgawa Ramu tana cewa "shegiya irin Dije irin tsiya ,baku san mutunci ba ,tsohuwa ta rariko Ramu da gudu taci karo da wani dutse tayi tuntuɓe ,Ramu dake tsaye tana jiran tsohuwa ta zo gurinta ganin ta faɗi yasa ta tu tsirewa da dariya tace "bani da alhakinki har da tafawa , a hankali tsohuwa ta rarrafa ta miƙe tana ɗingishi tace "shegiya irin tsiya kin yiwa Dije "oho dai kindai faɗi sai ki koma ɗaki "Ramu tace "tana tuntsirewa da dariya ta fice .

Tafiya taci gaba dayi tana yi tana ranguwaɗa harda yarfe hannaye taci karo da wani mai kwsar kwata , toshe hanci tayi taci ɗammara kana tace "jibeka zankaɗeɗe da kai amma ka ƙare a kwasar kwata ?" saurayin ne ya kalleta a kai kaice kana yace "ke dan uwarki ni kike gayawa haka ?"lura da tayi idanunsa sun juye alamar yana shaye shaye ya sanyata cewa "an faɗa mai shan giya kawai "ajiye baron dake gabansa yayi ya zubo da gudu , mai makon ta miƙe hanyar da take bi sai ta dawo hanyar gidan tsohuwa , da gudu ta shigo tana cewa "tsohuwa ki taimakeni zai kasheni "tsohuwa da ta gama kiɗimewa ta turo ƙofa da ƙarfi tana cewa "ya kasheki "dan Allah tsohuwa ki buɗe wlh ya biyoni "ya kasheki "tsohuwa ta faɗa tare da hayewa gadonta mai rumfa , fitsari Ramu ta saki a wando ƙafafuwanta har rawa suke tana ihu , wani wawan cafka yayi mata kana yace "ubanwa kike zagi ?"cikin suɓutar baki tace "badai ubana ba "buge mata baki yayi kana yace sai uban wa ? ya wanketa da mari ta riƙe gurin a hankali tace "Allah ya isa "waro ido yayi kana yace "waye wai ubanki ne ?"cikin tsiwa tace "kaje ka dubashi "tsohuwa dake ɗaki ta ɗaga murya tace "wlh kaci ubanta dama maganinta irinka mahaukaci "bugu ɗaya yayiwa ƙofar ta buɗe ya faɗa ɗakin da gudu yana cewa "ke gyatuma ki iya bakinki wlh zan mugun saɓa miki "nayi shiru "tsohuwa ta faɗa tare da toshe bakinta , mai kwasar bola yace "dena kallo na "cikin sauri ta sunkuyar da kai yace "tari naji kinyi sai na buge bakinki "Ramu dake bakin ƙofa tana jin diramar da sukeyi ta sanya dariya mai sauti tare da cewa "yau a dandali akwai labari mai daɗi ,ta fice da gudu .

Fitowa yayi ya tsaya a tsakar gida yace "wlh idan na kama jikarki sai nayi mata dukan tsuguna kaci doya "wlh kayi mata dukan sumewa ma "tsohuwa ta faɗa tana gwalo ido ,ficewa yayi cikin tafiyarsa irin ta ƴar shaye-shaye .

Tsohuwa najin ya fice ta nunfasa tare da yakice ɗan kwalin kanta tana fifita "wanan yarinya kwai masifa ,taje ta tsokano min tsuliyar dodo yanzu da naɗamin duka ai dana shiga uku ,tsohuwa ta faɗa tana share ragowar hawayen dake idonta.

Tunda Ramu ta fita take neman tsokana ,duk wanda tagani ko sa'an waye tsokanarsa take , wasu manyan sun bari a yarinta ke damunta wasu kuma basa ƙyaleta , cin karo tayi da wata budurwa tana waya a kusa da gidansu ,kasancewar gidan tsohuwa da nasu babu nisa , har zata wuce sai ta dawo da baya ta kalli budurwar ta tuntsire da dariya kana tace "jiran saurayinki kike ?budurwar dake yamutsa fuska tace "jiran ubanku nake "a'a'a ,Ramu tace "tana riƙe baki sai kuma tace "badai ubana ba sai dai naki "budurwar zata bita da gudu ta arce tare da yi mata gwalo ,cizon yatsa budurwar tayi cikin takaici tace "Allah yasa ma babyn nawa bai zo ba da wanan shegiyar yarinyar sai ta yarfani ,wata ƙila ma ta fallasani tace "aron kayan nayi, tana cikin magana wata mota Sharon fara mai gilashi tayi parking a kusa da ita , washe baki budurwar tayi kana tace "baby har ka iso ? leƙowa yayi yana yi mata murmishi yace "na ɗauka ma nayi miki laifi sbda ban fito da wuri ba ? "uhm ai baka laifi babyna ,budurwar ta faɗa tana kashe masa ido , buɗe murfin motar yayi tare da fitowa a hankali yace "dole in jinjina miki sarauniyar mata ,sunyi nisa a love Ramu ta taho a hankali da kifiyarta a hannu ta sace tayar motar tare da rugawa da gudu inda bazasu ganta ba .
Saurayin ne yace "Saudat ina sonki so mai tsanani bansan ko kema kina yimin irin son da nake yi miki ba?, lumshe ido budurwar da ya kira da saudat tayi kana tace "ai ni a tunani na Abdull soyayyar da nake yi maka tafi gaban kwatance, jin daɗin kalamanta ya sanyashi kamo hannunta ya buɗe murfin mota ta shiga shima ya shiga mazaunin driver ya tada mota , mamaki ne ya kamasa ya buɗe murfin motar ya fito tare da kallon tayar motar a fili yace "innalilahi wa'inna ilaihir raji'un , fitowa Saudat tayi ta kallesa tace "wai meke faruwa ne babyna?"tayar motar ce ta sace kumafa lafiya nazo da ita ai kin gani ma ko ?Abdull ya faɗa cikin ɓacin rai "to bari a kirawo masu gyara man ,Saudat ta faɗa tana shirin kama hanya ,Abdull da ransa ya gama ɓaci ya ɗauko wayarsa ya rufe motar da key yace "ki koma gida ni zan tari napep in hau ,ba haka taso ji ba daga gareshi sbda taso ya tafi da ita tunda duk zuwa yana yi mata kyauta mai tsoka gashi yau babu ko sisi kuma bashin kayan dake jikinta taci bata biya kuɗin ba , gani ranta a ɓace ya matso kusa da ita a hankali yace "Saudatu ki kwantar da hankalinki idan ganina ne da zarar munyi aure kin dinga ganina kenan ,murmishin yaƙe tayi lokacin daya fara tafiya a zuciyarta tace "ancema tunaninka nake ni tunani na daban ,ya zanyi in biya bashin da ake bina ?"ganin yayi nisa yasa ta yin gudu kaɗan-kaɗan har ta cim masa yana tare mai napep, baby yanzu tafiyar kenan ?Abdull dake shiga napep yace "insha Allah ba lallai gobe ma in dawo ba ,sbda zani Abuja wata ƙila nayi one week ma a can ,gabanta ne ya bada dumm a fili tace Bana ƙaunar muyi nesa da juna ji nake kamar in bika,murmishi Abdull yayi kana yace "ina dawowa sai maganar auranmu kisa ranki a inuwa.

NIDA YARINYA Where stories live. Discover now